RUƊIN ƘURUCIYA 29

Start from the beginning
                                    

"Nana wai shirin me kike yi ne haka?"

"Inna kin manta ne, babar 'yar ajinmu ce fa ta haihu yau suna, nace miki zamuje, bana tambayeki ba kika ce kin barni ba?"

Inna tace "ai na manta ne, kuma baki tunamin ba, se ganin ki nai kina shiri kawai dole in tambaya ai"

"Ai na gayamiki kin manta ne"

Inna tace "Allah ya taimaka"

Nana ta cigaba da shafe shafen hodarta tana shiryawa.

Inna na aiki a tsakar gida, sega ƙawayen Nana sunyi sallama.

Inna ta amsa musu tana ƙare musu kallo ɗaya bayan ɗaya. Daga bisani tai musu nuni da ɗakin da Nana take.

Kai tsaye suka nufi ɗakin suka shiga.

"Ahh su Nana 'yan mata irin wannan ado haka?"

Nana tai fari da ido tace "to a garin nan idan ban ado ba waze yi?"

"A'a ba wanda zeyi ta Jamilu ba da kanki a sare, ai idan muka wuce ta hanyar gidan me unguwa ya ganki seya rikirkice"

"Wallahi kuwa, dan mun haɗu ɗazu na kai niƙa yace min ina Nana? Nace masa kina gida amma da yamma ta layinsu zamu wuce zamu suna, ina ga ma yana nan a bakin layin yana jiran mu"

Nana tace "ke Hannatu, kama kanki, ni ba sa'ar wannan yaron bace"

Hannatu tace "ke! Jamilun ne yaro?"

"Eh mana ban da ya rainawa kansa hankali ni zece yana so?"

"Ke Nana shikenan kowa yana da saurayi amma banda ke?"

Nana tace "To Alawiyya meye dan bani da saurayi? Ke nifa wallahi ɗan Birni zan aura insha Allah, amma se nayi karatu me yawa, in auri saurayi ɗan gayu ɗan birni"

Hannatu tace "eh lallai kin ɗakko da zafi, ko da yake kuna da 'yan uwa a Birni ai"

Alawiyya tace "Amma ki tsaya ku gaisa da shi, kinga ba daɗi wulaƙanci"

Ɗan shiru Nana tai tana tunani, dan harga Allah ta na son taji ance ita ma ta na da suarayi, ta na son sanin me ake ji a soyayyar idan ana zance me ake cewa?"

Ba ta kuma cewa komai ba ta tashi, ta ƙarasa shirinta suka fito tsakar gida.

Nana tace "Inna zamu tafi?"

Inna ta kalleta tace "zaku tafi ina kenan?"

"Haba Inna, ɗazu fa nace miki ga inda zamu"

Inna ta ƙare musu kallo tace "ba inda zaki"

Saroro Nana tai tana kallon Inna, Cikin rawar murya Nana tace "Inna meyasa? Na tambayeki fa kince kin barni"

"Yanzu kuma nace ba zaki ba"

Ƙwalla ta taru a idon Nana tace "Inna meyasa ba zani ba?"

"Saboda na isa, kin wuce kin ban guri ko senai fatali da ke a gurin nan? Ku kuma maza ku kama hanya ku tafi"

Sumi sumi suka nufi hanyar fita daga gidan.

Nana kam da gudu ta bar tsakar gidan tana kuka, ta rasa wace irin rayuwar takura ce haka, wasu lokutan gani take kamar Inna ba ta ƙaunarta Saboda yadda take takuramata, da hanata sakewa.

Su Alawiyya na fita suka fara gulmar Inna.

"Taɓ Hannatu, dama haka kakar Nanan take, wannan mata anyi jarababbiya, ji yadda ta koremu"

"Hmm kedai bari, shiyasa Nanan ma gata nan jarababbiya, wallahi idan nice ba zan yadda da wannan abun ba, ai kakata ce ba uwata ba"

"Wallahi kuwa balle kuma ni"

RUƊIN ƘURUCIYAWhere stories live. Discover now