RUƊIN ƘURUCIYA 21_22

Start from the beginning
                                    

Inna ta jinjina kai tace "ba shakka, 'ya'yan turawa ko, shikenan Allah ya temaki turawa, Allah ya shirya"

Tana gama faɗin haka ta juya ta koma cikin gidan.

Shi kam Sadik kamar ya fashe, saboda yadda ya kumbura baki yana wani irin huci.

Mother tace "kaga abunda ka janyo min ko? Na gayamaka tunda Allah yasa tsohuwar nan ta tare a gidan nan kayi komai a hankali, in ba haka ba ido zata samana komai ta gani taita masifa"

Usman yace "Mother, dan Allah duk kuyi haƙuri dan Allah komai ya wuce, karki kuma yin wani lafin, kuma dan Allah idan ta ɗau zafi ki dena tanka mata, hakan yana tunzurata, Yanzu dai duk kuyi haƙuri"

Sadik bece komai ba ya wuce ɓangaren su, Khairat ma ta shiga cikin gidan tana sunkuyar da kai kamar munafuka.

Mother kuwa tana zuwa ɗakinta, cikin 'yan uwanta ta hau masifa tana mitar Wai Inna tana ja wa 'ya'yansu masifa tana musu baki, ita Alla alla takema ayi bikin nan tabar mata gida duk tabi ta isheta.

Suka haɗu suka dinga yi da Inna suna zagin ta.

Ita kam Inna tunda ta koma ɗakin da suke, tai shiru tana tunani al'amuran Sadik na bata tsoro da mamaki, tabbas idan aka cigaba da tafiya a haka da wannan sakacin ko sakarcin na uwarsa tabbas Yaron ze lalace.

Dan ta lura halayyar sa daban da ta sauran yayyen sa, tarbiyyar Sadik na buƙatar jajircewa da kuma sa ido, saboda kansa yana rawa fiye da shekarun sa.

Sadik kuwa gaba ɗaya ransa a ɓace yake, Alla Alla yake a gama bikin nan wannan tsohuwar ta bar musu gida, ya rasa me ya tare mata take masa wannan abubuwan, ba damar ya motsa se ta haushi da masifa.

Haka yana kumbure kumburen baki, yai wanka ya kwanta, amma bacci yaƙi zuwa.

Can kuma se partyn da su kai suka dinga dawowa kansa, take surorin 'yan matan nan suka dinga dawo masa kansa.

Ƙoƙarin banzatar da tunanin yayi, amma abu ya faskara, zuciyarsa ta dinga raya masa cigaba da kallon series film ɗin nan, amma wata zuciyar ta shiga gargaɗin sa.

Series ɗin yana ƙayatar da shi, amma kusan kaso arba'in na film ɗin yana bayyanar da very hot Romance ne tsakanin masoya.

Runtse idanunsa yai, amma se ya dinga Ganin Farhan a idonsa, da wannan kyakykyawan murmushin nata.

A hankali ya furta "Oh God"

Ya ɗakko wayarsa, ya dinga kallon lambar da ta kirashi da ita, se kuma ya kalli agogo yaga kusan sha ɗaya na dare, jiki a sanyaye ya ajiye wayar, ya nemi guri ya kwanta.

Da tunani barkatai cikin ransa da haka bacci yai awon gaba da shi.

Washegari Alhaji Abdullahi ya dawo daga tafiyar da yayi, wanda ya kasance ranar fara bikin ɗansa Usman.

Da yamma ya shiga gaida Inna, lokacin kusan duk jama'ar gidan sun yo ye sun tafi gurin biki.

Cike da girmamawa suke hira shi da Mahaifiyar sa.

Can Inna ta nisa ta kalli ɗan nata tace "Abdullahi!"

Wani banbarakwai yaji, dan Inna ba ta sba kiransa kai tsaye da sunan sa haka ba, se idan ta na da wata mahimmiyar magana.

Hakan yasa shi tattara nutsuwarsa da hankalinsa akan ta, yana sauraren me zata ce masa.

Cike da damuwa tace "Kamar yadda ka sani, ni mace ce me son haihuwa, Allah ya bani haihuwa, sedai duk sun koma, kaine ɗana na huɗu, bayanka na hayayyafa amma duk ba su rayu ba, ɗan uwanka Abubakar ya taso ina murna Allah ya barmin, se bayan yayi Aure ya haifi wannan Yarinyar ya karɓe shi ya karɓi mahaifiyarta"

RUƊIN ƘURUCIYAWhere stories live. Discover now