" Mashaaa Allah! Adda kinyi kyau"

Nayi murmushi Nima nace

" Nagode Anna"

Purse dinta ta janyo ta bani 500 na saka jakata ban manta Yi Mata godiya ba, ta bani tsaraba akan na Kai gidan su Zuhra Kuma kada nayi dare. Ban Jima ba na samu napep mukai ciniki ya kaini har kofar gidan, tunda muka Shiga unguwar nasan na masu dashi ne, gidaje kankararru ga Kuma shiru baka m ganin wulgawar mutane, na sauka na sallame shi sannan na Isa gate din nayi knocking a hankali, security ya bude yana kallona kasa da sama yace

" Gurin wa Kika zo?"

Na gaishe shi sannan na fada Masa, se ya Kara tambaya ta ko Zuhra tasan da zuwana na girgiza masa Kai alamara a'a, se yace to na kirata, ni Kuma bana son hakan so nake kawai ta ganni, Amma se na Ciro wayata da niyyar kiranta, se naji honk a bayana, da sauri na matsa, Yaya Man ne shi da wani me yanayi da Saif sede daga gani ya girmi hatta Yaya Man din. Aka bude musu gate ya danna Kan motar ciki, me gadi ya mayar ya kulle, se Kuma ya buden yace

" Ki shigo inji oga Man"

Na saki ajiyar zuciya na shiga na samu Yana fada musu

" Akan wannan da kuke gani zaku iya fara takun saka da Zuhra, ku ganeta saboda next time"

Se Kuma Suka fara bani hakuru Wai Basu gane ni ba, to da sun sanni ne? Na ayyana a raina, karasawa nayi na gaida Yaya Man da Kuma na gefen shi, Yana murmushi yace

" Yau gidannan Babu Zama finally Unaisa tazo"

Wanda ke gefen busy with his phone yayi saurin dauke Kan shi daga wayar  yace

" She's Unaisa?"

Ya fada yana kallona from head to toe, na tsani irin wannan kallon Amma a ganina ai duk waccan Yar hau din ce ta jamin, idan kana zuzuta Abu da zancen shi kowa zai so yaga abun. Tare muka Shiga har parlon da ya gaji da haduwa, Ina tsaye ya kwadawa wata Kira daga ganin yadda tazo kasan me aiki ce ya Bata umarnin ta raka ni wajen Zuhra. Na bi bayanta muka haura stairs nanma parlon Dana samu se da yayi putting na kasan to shame. Daki dake gefe ta kwankwasa sannan ta tura tace min ki shiga kilan Bata tashi ba ma. Na Mata godiya na wuce ciki, komai na dakin peach ne, it looks lovely, dakin yayi duhu saboda ko Ina a kulle yake se AC dake aiki Babu kakkautawa, na karasa gaban gadon inda ta kudundune na yaye tare da bubbuga gefen gadon, ta bude idonta se Kuma ta rufe, se ta Kara budewa kafin ya Mike a sukwane, ta rungume ni, se ta sake ni ta shige toilet. Nayi dariya na kunna Kwan dakin na ninke Mata duvet din na gyara gadon na zauna Ina fadawa Anna na samu gidan, ta bani sallahun na gaishe su na Kuma dawo da wuri.  Bata Jima ba ta fito sanye da bath robe ta zauna gaban dressing mirror tana fadin

" Unaisa naji dadin zuwan ki, Wai Dan kwatancen da na Miki har kin gane kenan?"

Na Harare ta ta Gama shiryawa sannan ta ja hannuna muka fita,tana ta mini Hira tun Ina murmushi har na saki jiki mukai ta Hira,dakin Dada mukaje, kana kallon matar kasan bafullatana ce, kusan tsayin su daya da Anna, for some unknown reason se nake ganin kamar Anna, bawai Kama suke ba Amma kawai se nake ganin yanyain Anna a tare da ita. Tunda na shigo ta kafe idanun ta cikin nawa, har na tsugunna har kasa na gaishe ta, tana ta kallona Wanda yasa naji I'm uncomfortable itama ta amsa tana nuna min gefenta na zauna, tace

" Ina Maman ki? Yau dai Unaisa tazo mun huta da mita"

Nayi murmushi nace

" Tace a  gaishe ku"

Ta danyi murmushi amma se Naga yanayin ta kamar tana cikin damuwa, ta dubi Zuhra tace muje mu gaida Abba. Muka Mike shi har yafi Dada Wasa da barkwanci, ya dinga min tambayoyi Ina amsawa sannan muka koma dakin Zuhra, ta kunna Mana kallo wani film da ban ma gane a wacce kasa bace, they're more of Chinese. Se tace min ai Koreans ne and I began to think yadda ake take gane su Bayan kusan duk Kamar su daya. Wasa Wasa kafin mu tashi a kallon Nima na fara gane su.

A parlon Dada muka je cin abinci, tana zaune tayi shiru da abinci a gabanta, se Yaya Man da wannan Dana gani. Muka zauna shi din yace ma Zuhra

" Finally yau munga Unaisa"

Nayi murmushi, ita Kuma tace

" Yaya Muhammad ka ganta kyakyawa ko? Wallahi tafi Ya bilkisu kyau"

Na zungure ta ta kalleni na Harare ta, shi Kuma se dariya yake, Bayan mun Gama lunch din Dada tace min

" Unaisa ku Yan wanne gari ne?"

Nace

" Masaya, Anna tace a Birnin kudu yake"

Dada ta gyara zamanta tace

" Baku taba zuwa ba"

Na danyi shiru Ina son tuna last da muka je, se na tuna time din da aka cewa Anna mu ba Yayan Baba bane,idanuna suka ciko da kwalla na danyi kasa da kaina nace

" An dade, bazan ma iya tunawa ba"

Se ta gyada kanta I was hoping kada ta Kara min wata tambayar Kuma, Amma se tace

" Dangin Maman ki fa?"

Na danyi shiru nace

" Anna Bata San iyayen ta ba, kawai dai akwai yayarta Inna Zulai a gurin ta tashi, se tace Wai kamar sunada wata yaya Kuma, I'm not sure yadda abin yake"

Ban taba maganar da wani ba Amma bansan me yasa nayi maganar da Dada ba, kawai naji ya kamata na Bata amsa, Bata Kara zancen ba Amma she looks disturbed, tace naje wajen Zuhra Dan daga ni se ita mukai maganar, na koma bayan laasar na koma na Mata sallama se tace min

" Inna Zulai din tana nan?"

Se na girgiza Kai nace

" Ta Jima da rasuwa"

Daga Haka ta bani Kaya sosae, Abba ya bada kudi a bani na dinga godiya se gida.

Dadas' POV

Bayan fitar Unaisa da tafiyar ta, Dada ta mike zuwa window Wanda yake katoto Yana Kuma baka damar hangar duk wani Abu Dake faruwa a parking space din gidan, a hankali Unaisa ke takawa, kana kallon ta kasan ta Kai shekarun Yan matanci, a hankali take tafiya me cikeda karsashi kuma, bayanta Zuhra Dake dariyar da Bata San me suke fada ba, jiyowar Unaisa da sakin murmushin ta yasa Dada matsanancoyar faduwar gaba, hakan ba zai taba yiwuwa ya Zama coincidence ba, Dole duk inda Unaisa ta fito ta hada iri da tsatson Inna, a hankali Unaisa ta shiga waving hannunta ma Zuhra se taga tamkar ranar da Inna ta juya tana daga Mata hannu bayan an kaita dakin ta, wannan tafiyar ita ce ta karshe daga ranar Babu labari Babu Kuma dawowar su, daki ta koma ta bude safe dinta Bayan ta Danna passcode ta Ciro wani karamin hoto Wanda ba se an fada maka ba dadewar tashi ta Isa, hoton ya kunshi Fulani guda biyu, wadda macen tamkar Unaisa ce a tsaye sede kasancewar ta hoton Fara ce yayinda Unaisa take baka, Haka Kuma se Dada da Abba cikin shiga ta alfarma, se wani a tsaye Wanda mahaifin Dada ne, da Kuma karamar yarinyar shekara takwas zuwa Tara. Ta jujjuya hoton ta cigaba da shafa fuskokin dake hoton musamman fuskar photocopy din Unaisa!

Unaisa is not free! Pay N300 to 3091721807 Aisha kwalam Hassan first Bank of Nigeria and send evidence of payment to 09063467258

UNAISAWhere stories live. Discover now