Cikin sauri wani Security ya fidda five hundred ya bashi ya amsa ya juya.

Kana ta dan kalli wajen da Security din yake tace;"Thank you"

Bata tsaya jiran mizai ce ba tayi gaba cikin sauri ta shiga gidan.

A farfajiyar gidan ta tsaya tana kara kallon kayattacen gidan su da kullun kamar sabo haka yake saboda yawan gyaran shi.

A hankali take takawa har ta isa part din da tasan Kanwar Maman ta na zama Nadiya tana kiran ta M2

Tana zuwa ta iske kofar a bude saurin shiga tayi cikin dakin.

"M2 na! M2 nah!"

Take fada da duka muryar ta cikin doki tare da murmushi.

Wata matashiyar budurwa ce ta fito daga Bedroom din dake cikin palorn shekarun ta zasu kai talatin da biyar baka iya gane kyaun ta kai tsaye saboda da ka ganka kasan Boko da wayewa da hutu sun zauna a jikin ta, Doguwa ce Mai dan jiki amman ba sosai ba babu kallabi a kanta hakan yasa gashin ta ya bayyana wanda iyakar shi tsakiyar kanta amman fa yasha gyara, Sanye take da Suits riga da wando pink color sun kamata dai-dai jikin ta inda Hanaah ke tsaye ta nufo hadda gudun ta tana zuwa ta dauke Hanah kamar karamar yarinya kana tace;"My Princess ina kika shiga ne tun da safe na shigo garin morning flight nabiyo saboda ke amman ina isowa Aunty tace man Wai baki gidan kwana biyu zonan naji waya taba man Princess dina"

Turo baki Hanah tayi kana tace;"Nide Mom yana ganki da kayan aiki bade yau zaki koma ba ko?"

Ta ida maganar tamkar zatayi kuka.

"Ohhh Princess taya zaki ce haka one week zanyi nama fada wajen aiki saboda ke din kin san ke tadaban ce zo muje bedroom maganar bata tsaye bace"

"Ke Maimuna Idan kin gama gyaran palorn ki hada ma bako na abin motsa baki"

"To"

Har sun juya sun tafi sai kuma Nadiya ta juyo ta kalli Nanny dake goge-goge.

"Maimuna badake nike magana ba"

"Nace to"

Nanny tace batare daya kalle mu ba ta cigaba da abinda take.

Nadiya tayi Ashariya kana tace;"Dan iskan ci ke kin raina kowa a gidan nan idan aka maki magana a gadaran ce kike amsawa to su Aunty sukaji zasu iya amman banda ni, Nayi maki magana zaki wani ce TO yadda kika san ke wata tsiya ce haka kikeyi a gidan nan to bari kiji keda sauran yan aiki baku da babanci dadewar a gidan nan bashi zaisa ki dauka kema kin zama yar gida ba"

"M2 Nide kyale ta muje kinga har ranki ya baci bani son kuma ranki na baci muje nide"

Nayi maganar ina jan hannun Auntie Nadiya da sai Masifa take.
Sai a lokacin Nanny ta dago muka hada ido ras! Naji gabana ya fadi idanun ta sunyi Jajawur kamar wadda ta dade tana kuka.

Ta gama goge-gogen tazo ta gifta ta gaban mu ta wuce.

Naja M2 mukayi bedroom muna zuwa ta zaunar da ita bisa gado kana na dauko ruwa na zuba mata na mika mata nace;"Sha 2nd Mum"

Amsa tayi tace;"Wallahi Hanah bana son matar chan ko kadan saboda yar rainin hankali ce kina gani fa yanzu ina masifa amman bata ce komi ba tazo ta gifta ta gaban mu ta wuce kuma idan nayi ma Aunty magana haka zata ce nayi hakuri yadda kika san ta shanye su Aunty haka suke tsoron ta"

"Hmmm kede M2 mubar maganar amman ba'a cewa komi ni idan ana maganar tama raina baci yake sosai dan haka mubar ta yanzu de gani nazo"

"Yawwa akan kayan da zaki saka ne gobe"

Laptop din ta ta jawo ta bude mata pictures din dogayen riguna tace ta zaba.

"Wayyo Allah Aunty na kasa zaba su duka sunyi kyau tayani zaba"

ZAFI BIYU Where stories live. Discover now