"Kai Haba Mummy kai Naji dadi sosai da sosai Daman na dade ban gan shi ba"

"To yanzu de kin huce zaki dawo gida ranar Birthday din ki ko kin san nayi shirin komi please Hanah ki dawo mana"

"Gaskiya Mummy ni bazan koma ba nafi jin dadin zaman nan saboda nan babu mai mani munafunci"

"Kira man Annie muyi bankwana"

Tashi tayi taje ta kira Annie suka dawo tare.

"Annie zamu wuce amman ina neman alfarma wajen ki kice ma diyarki ranar Monday tazo gida mun shirya mata wani abu ne please Annie"

"Haba Maman Hanah kada kice haka mana Hanah zata zo insha Allah"

"A'a Annie bazan koma gidan nan fa gaskiya dan Allah abarni anan idan naje nasan Dad bazai barni na dawo ba"

Annie ta kama hannun kana tace;"Kada ki damu zai barki ki dawo kinji"

"A'a Annie nifa saide idan dake zanje kuma mu dawo tare"

"To shikenan Allah ya kaimu"

Girgiza kai Mummy din ta tayi tace;"Banda abun Hanah akwai mai gudun gidan su yanzu Kinga kin azama Annie dawainiya ko"

"Haba nan gidan ai gidan kowa ne kuma kin sani dan haka ba dawainiya Hanah kwana biyun da tayi sabon da mukayi da ita ai kamar mun shekara dan haka bakomi munajin dadin zaman ta sosai da sosai dan banko son naji tace zata tafi"

"Bade abinda zance Annie saide muce mungode Allah yabar muzunci"

"To Ameen mungode da ziyara insha Allah zan kawo maki Hanah da kaina"

"To Annie nagode sosai da sosai"

Nan Annie taba ta turarrukan wuta masu Kamshi kana sukayi bankwana Annie tace;"Hanah raka Mummy din ki mana"

Langwabe kai tayi dai-dai lokacin da su Imran suka shigo sun taso daga masallaci nan suka gaisa da Mummy din Hanah duk ba susan ita bace.

"A'a Annie kyale ta munyi bankwana ai nide a kyaleni ban son fita ne"

Murmushi Mummy din tayi tace;"Annie kyale ta yanzu nasan bazata fita waje ba mungode sosai sai munyi waya"

"A'a Munmy din Hanah ce kai munajin labarin ki motsi kadan Mummy Mummy"

Murmushi jin dadi tayi kana tace;"Kai nima ai inajin Labarin ku Uncle Imran da Malam Hakeem na fadi dai-dai ko"

"Eh hakane mune"

Nan suka kara gaisawa kana tayi bankwana suka tafi Hanah na jikin Annie.

"Hanah miya  bazaki raka Maman ki ba? kin san akwai sirri tsakanin Uwa da diya sannan zataji dadin haka"

"Annie ba yin kaina bane kawai idan naga koda fuskar Nanny ne raina b'aci yake sosai da sosai shiyasa naki raka ta"

"To Shikenan tashi kije Laure takai maku abinci dakin ku"

"Annie yau ba'a tare zamuci ba?"

"A'a zamuci anjima"

Sai yanzu ta tuna da abinda ya faru kallon fuskokin su Imran tayi taga yadda suke cikin damuwa kallon Hakeem tayi taga fuskar shi na kasa baka ganin ta Dan murmushin jin kunya tayi kana tace"To shikenan Annie sai anjima"

Kaiwa da kawowa Hajiya Babba take a makaken Parlon ta.
Kamal da Gimbiya Rukayyah suna zaune suna jiran mizata fada.

"Gaskiya Hajiya rashin son da mutanan nan keman yayi yawa na rasa mi nakeyi na tsone masu ido"

"Kada ka damu dami sukeyi dauki waya kira mani Uncle din ka"

"Hajiya tun dazun tun kamin mu shiga Masallaci nake kiran number bata shiga ban san ma yanzu a wace k'asa yake ba"

"Kira shi ta WhatsApp "

"Kiran shi yayi kana ya mika mata wayar yace;"Gashi tana ringing"

Amsa tayi tare da saka Speaker an dade ba'a dauka ba saida ta kusa katsewa kana aka dauka.

"Hello Kamal ka kira zuwa anjima"

Bai bari akayi maganar ba ya kashe wayar .

Wani dogon tsoki Hajiya Babba taja kana tace;"Matsalar ka kenan Yasaarrr kullun kai ba'a samun ka kullun shi cikin aiki yake mtsww"

"Kada ki damu Hajiya zanyi mashi Message idan ya duba yaga mike faruwa da kanshi zai kira kin sande yadda ya tsani Hakeem saboda Hakeem yabar zuwa gidan nan dan haka kibar shi zai kira ki ko tsakar dare yaga Message dina saiya kira ki"

Gimbiya Rukayyah dake zaune tace;"Zauna ki huta Hajiya maganar Kamal gaskiya ne"

Rahama ce ta shigo Parlon tace;"Mikuke tattaunawa ne?"

"Bai shafe kiba wannan daga ina kike da ranar nan?"

"Ya shafeni nasan akan maganar kujerar Uncle Kamal kuke magana Hmmm naje part din su Zarah na fito kenan naga wata mota kofar part din gidan Annie wannan motar inada tabbacin Matar Governor kade zata iya hawan ta Kinga kenan Annie ta riga ku kai Case din wajen Governor shine nazo na fada maku dan inaga tana mu'amallah da ita"

Hajiya Babba tace;"Tofa yaushe matar nan ta fara mu'amalla da matan Manya a iya sani na kullun matan Almajiran gidan nan ne ke cika mata gida kenan yanzu dani take gasa?"

Kamal yayi saurin cewa;"Hakane Hajiya dan taga kina mu'amallah da manyan ne shine itama ta fara"

Gimbiya Rukayyah ta mike tace;
"Matar Governor ai abokiyar Hafsat ce muyi ma Hafsa magana mana muji"

"Bana son Hafsat taji komi game da wannan saboda naga goyan bayan su take"

"Hakane kuma Hajiya"

"Yanzu minene abinyi?

"Mu jira Yasarrr shine zai kawo karshen komi cikin sauki"

Wani murmushin k'eta ko mugunta zata zamu kira shi Kamal yayi kana yace;"Harna fara tausaya maka Hakeem"

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Hanne ce tayi mana girki saida yamma na fito nan naga matan gidan sun fito ko wace kofar dakin ta wasu zaune bisa kujera wasu kuma bisa farin bokiti ina fitowa suka bini da kallo nan na nufi toilet ina zuwa na iske wai Layi akeyi nima tsayawa nayi ina jira.

Na dan dade nan kana na samu na shiga toilet din wanka nayi na fito daure da zane sannan sanye da Hijab da namiji na fara cin karo da wani Katon Namiji yayi tsaye ya rike wando yana jira ne nide rabawa nayi gefe na wuce nan na k'ara wuce matan gidan tsakar gida yanzu ma sai suka bini da kallo har na shiga daki.

Yau bacci nake son yi da wuri hakan yasani shirin bacci da wuri nazo zan kwanta naji dakin kusa damu sun kunna kidi chan kuma naji surutu tsakar gida nayi tunanin ko fada akeyi na tashi na leka naga Mata da Maza ne zaune suke bisa tabarma ana cha-cha sai shewa suke.

Zama nayi bakin Katifa na dafe kai nace;"Shikenan rayuwata a Nigeria daga Bara sai kuma zama irin wannan gidan shin gidan su waye nan ko gidanKaruwai ne? Daga zaman Bara sai zama cikin Karuwai??"

Dafe kai nayi ina girgizawa ganin yadda rayuwata ke tafiya bana son nayi irin wannan rayuwar.

Jin ihun yayi yawa yasa na tashi na leka cikin sauri dan naga mike faruwa.
Dafe bakina nayi ganin Hanne cikin su suna magana suna dariya a fili na furta;"Wayyo Allah na kenan Hausawa ne??"

MARYAM ANKUDIE {Qurrah}

ZAFI BIYU Opowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz