Yana zuwa babu wani daukar Uzuri ya zauna bisa kujerar da Magajin gidan ke zama.

Yau babu wanda yayi mashi magana zama yayi yana kallon kowa d'age a kullun takamar shi itace shi Jinin sarauta ne.

Aka faragabatar da addu'a kamar kullun kana Abba Muktar yace;"Kamar yadda aka sani zamu nada sabon Magajin gidan nan saboda kula da sauran Makaratun dake a karkashin gidan nan sannan da harkokin Zakka da kuma sauran hakkokin dake akan duk wani magajin gidan nan dan haka zamu nad'a Abdulhakeem a matsayin........"

"What! Kasan mi kake fada kowa yasan wannan matsayin Kamal nan sannan tun kafuwar gidan nan d'an mace bai taba rike shi saboda baida gado akan kujerar dan haka kowa yasan Hakeem d'an Maryam ne sannan kowa yasan Uban shi Almajirin gidan nan ne har Uban shi ya mutu sharar Masallacin gidan nan shine aikin shi dan haka Hakeem baida gadon gidan nan ya koma Kauyen Baban su ya gaji Maluntar su ta tara Almajirai kofar gida da hura wutar Kara ya dauki Alqalami da Allo da bakar tauwada inaga shizai fi dan kowa gadon gidan su yake Gada"

"Sai Yau na tabbatar dake da Yaron naki Jahilci ke damun ku"

"Kada kaman ta koni wacece kada ka manta daga wane gida na fito sannan kada ka manta inada karfin da zan saka na amshi Mulki naba Kamal sannan Daga yau Governor din dake kan kujera shi zai dinga nad'a Magajin gidan nan dan haka Kamal tashi muje kasa Uncle din ka ya kira man Governor zan nuna maka banbancin d'an Mai sharar masallaci da jinin Sarauta "

Daga haka taja hannun Kamal suka fita sannan sauran Yaran ta suka bi bayan ta.

"Innalilahi Malam Mukhtar miyasa zakayi haka Hakeem baida damar amsar wannan Mulkin sannan nima bana son wani Nawa yayi sannan bana son Family din nan ya samu matsala saboda ni ko Ahalina dan Allah kasa a tsaida Hajiya Zubaida ko kayi man izini naje na tsaida ta"

Annie ta mike tana maganar hankalin ta tashe dan har jikin ta kyarma yake.

"Ki kyaleta tayi duk abinda zatayi ba Hakeem zan ba kujerar Kamal ba amman yanzu shi zan ba saboda bata bari na ida bayani naba zan nada Hakeem mai kula da Nafsir ne sannan shizai bada karatu a Masallaci,  ba ina nufin zan nad'a Hakeem inda take tunani ba, tana tunanin zan bashi kujera ne dan haka taron yau ya kare Hakeem ka sameni a masabkin baki"

Tunda aka fara maganar nan kan Hakeem na k'asa sai yanzu ya dago kai ya kalli Abba Mukhtar kana yace;"To"

Nan aka fara fita daga parlon kowa da abinda yake cewa nan fa kowa ya samu sana'a a Family din dan duk inda ka kalla gungun mutane ne kowa da abinda yake cewa.

Iman ce ta shiga dakin su ta iske Hanah na Bacci zama tayi tare da dafe kai.

Hanah dataji motsi nayi mika ta tashi taga yadda Iman tayi tagumi janye hannun ta tayi daga tagumin tace;"Malama lafiya de har antashi meeting din?"

"Hmmm meeting bai yuyuba ai"

"Saboda mi"

Nan Iman ta bata labarin fadan da akayi kana tace;"Wallahi bana son kan Family din nan ya rabu saboda wannan"

Dariya Hanah tayi tace;"Ikon Allah yanzu shima Maluntar har gadon ta ake? To a tunanina malunta ai  ba kudi ake samu ba saide lada "

"Yanzu kudi ake samu Hanah shine dalilin da yasa Hajiya Babba ta dage idan kika duba yanzu Malam mu duk sun shiga siyasa hakan ya ba masu Mulki damar yin yadda suke so saboda Malam da zasu fito su fadi gaskiya sun koma a karkashin su maganar gaskiya Uncle Kamal bai dace da wannan kujerar ba saboda ana son Malamin Ilimi ya kasan ce Maikamewa da kuma..."

"Ya isa haka Iman sai yanzu na fara fahimtar inda kika dosa lallai kam to Allah ya kyauta"

"Ameen Hanah. Tashi ki shirya yau Jummu'a"

"Tab ni rabon da inyi wata kwalliyar Jummu'a ai tun ina yarinya"

"Hmm to yau saikinyi ta"

Tashi tayi ta dan guntun tsoki ta shiga toilet daga cikin bathroom din ta fara kwala ma Iman kira.
Cikin sauri Iman taje bakin bathroom din ta tsaya tace;"Minene mike faruwa?"

"Towa zai hadaman ruwan wankan ne?"

"Ke Malama nifa ba Nanny din ki bace ace kullun saina hada maki ruwan wanka sannan na fidda maki kayan da zaki saka sannan hatta man da zaki shafa saina buda maki nagaji wallahi"

Hanah ta fito daure da towel tana Bata fuska ta zauna gefen gado tace;"Aiko saide naki wanka dan ban iya hada ruwan wankan daman ban gaji da bacci ba bari na koma"

Ganin zata kwanta gashi Shabiyu na rana ya kusa yasa Iman tace;"Zan hada maki amman anjima ki hada da kanki"

Dan Dariya Hanah tayi tana kallon yadda Iman ke magana kana tace;"Anjima ke zaki hada su"

"Haba yarinya zande kira Nanny ta dawo nan saita dinga maki bauta amman ba Iman ba"

Jin sunan data ambata yasa Hanah yin Shiru tare da Shan toka.
Jin tayi Shiru yasa Iman juyowa ganin yadda tayi da fuska yasa ta tuna ta ambaci sunan Nanny girgiza kai tayi kana ta shiga bathroom din ta hada mata ruwa ta fito ta iske zaune yadda tabar tayi tagumi sannan tayi zurfi cikin tunani.
Ta dan dade tsaye tana kallon ta kana tazo kusa da ita ta dan tabata firgigi tayi ta tashi kana ta sabke ajiyar zuciya.

"Tashi kiyi wanka"

"To"
Hanah tace ta mike ta shiga bathroom din Iman ta fita mata kayan da zata saka tana nan zaune ta fito ta zauna Iman tace;"Sarkin yan Makeup kwana biyu bakiyi ba amman yau nasan saikinyi tunda naga kin zauna haka"

"Wallahi nayi missing din Makeup kin san yadda nake son ta"

Hanah ta fada tare da fara Makeup ta dade tana makeup saida ta gama ta dauki kayan da Iman ta fidda mata doguwar riga ce ta atamfa dauka tayi ta saka a daurin kallabin ma ta dade kana tana saka agogo a hannun ta Laure ce ta shigo tace;"Hhh Uwar dakina wannan kwalliya haka kyau ace surukina zai gani"

"Kai Baba Laure nide mubar wannan maganar kin saka naji kunya"

"Gaskiya na fada Uwar dakina Allah ya kaimu lokaci de"

"Ameen Innata"

"Yanzu de muje Mummy din ki tazo"

"Da gaske kike kai Inna Laure naji dadin labarin nan"

Rungume Inna Laure tayi tana murna kana ta sake ta ta ruga a guje.

Koda ta fito Parlon lokacin Annie itama ta fito daga dakin Hanah tace;

"Mummy!"

Ta fada tare da yin tsalle ta ruga zata rungume ta.

Duk halin da Annie take ciki saida tayi murmushi.

Hanah na isowa wajen Mummy din ta tayi turus ta tsaya tare da komawa baya tana kallon Mummy din ta tare da nuna wadda ke bayan Mummy din ta da hannu, hannun har kyarma yake tace;

"Ke......!"


MARYMA ANKUDIE {Qurrah}

ZAFI BIYU Where stories live. Discover now