Kallon katangar nayi naga zan iya tsallake ta aje masu butar su nayi na tsallake katangar gidan.

Ban ko waiga ba har saida naga na fara barin Zango kana na tsaya na zauna ina maida numfashi tare da jan dogon tsoki nace;"Wai ita matar nan ko ina ruwan ta dani ko zakuna ke cikin Nigeria saina shigeta saide idan naje su hadeni"

Ina nan zaune bakin hanya saiga wata mota.

"BADAGIRI... BADAGIRI"

Mikewa nayi duk nasan banda ko sisi na shiga motar, Batare da tunanin maizai faruba.

Tafiya kadan sai mun hadu da Police sai sun leko suna kallon mu naji dadin kayan nan dan su suka taimake ni da ka ganni zakayi tunanin ni cikakkakiyar ba Hausa ce.

Kallon matar dake kusa dani nayi wadda ke tare da Mijin ta na gaidata da French naji ta amsa tambayar ta nayi ina ne zamu?

Cikin mamaki tace;"Ke ina zaki?"

"Nigeria"

Na bata amsa kai tsaye ina jiran amsa.

"To ai yanzu gamu nan a Badagiri LG din Legos ce"

Zaro ido nayi cikin farin ciki nace;"Kenan ina Nigeria"

Tace man;"Eh"

Ihu nayi saboda dadi nike a karshe kusa da Window hakan yasa na zura kaina a Window ina shakar iskan Nigeria ina murmushin da na dade banyi irin shiba.

"Nasan zan samu kyakyawar tarba ga mutanan kasar saboda kasar masoyina ce"

Muna isowa wani katon mutum shine driver din ya fito ya rike wata mata banjin yaren da suke magana saboda da turanci suke magana amman na fahimci saboda kudi suke fada wani mutum dake kusa dani shima sai fada yake inajin abinda yake cewa saboda da French yake maganar saboda motar a kulle take gashi muke baya kallon matar shi yayi yace;"Wai Kinga driver din nan yaki bude mana saboda Naira Hamsin din da matar chan bata cika mashi ba ta gaba gaski...."

Ai kamin ya ida mukaga driver ya chakumi matar nan zaro ido nayi na shiga ukku shikenan na mutu kawai nasan ni idan yasan banda kudi killani zaiyi kawai.

Da kyat aka raba su kana yazo ya bude mana nice ta karshe mutanan suka gama fita suna bashi kudin mota nima na yunkura da kyat na fito ina zare ido.

Hannu ya miko man ranshi a bace yana huci babu alamun imani a tare da shi.

Aza hannu kawai nayi a kai yanzu da abinda zan fara cin karo kenan a Nigeria???

⭐️⭐️⭐️⭐️⭐️⭐️⭐️⭐️⭐️⭐️⭐️⭐️⭐️⭐️⭐️⭐️

Lallai Ilimi haske ne kuma ilimi garkuwa ne sannan baiwa ne ilima yasa Hakeem ya banbanta da sauran samarin dake zaune a wajen hasken ilimi ya haska kashi ya fita daban a cikin su komi nashi a natse yake yin shi fuskar shi dauke da annuri ya fara gabatar da addu'a a cikin harshen Larabci.

Addu'a aka shafa kana suka fara gabatar da Meeting duk akan maganar hadin kai da zaman lafiya a Family din ne suka tattauna.

Tunda aka fara Hajiya Babba bata kara magana ba haka yaran ta harmade Kamal dayake kallon an tozartaci gaban kowa saida aka ambaci sunan shi yayi addu'a kana wani daga baya yazo ba'ayi mashi fadan makarar da yayi ba aka maida addu'a akan shi.

Ana gamawa kowa yayi haramar fita saboda zuwa masallaci wasu suka tsaya gaisawa da yawa sun gaisa da Hakeem tare da taya shi murna akan nasarar daya samu.

Tare da Imran suka nufi masallacin Jummu'a.

Bayan Jummu'a gidan cike da yan uwa da abokon arziki anata sada zumunci.

ZAFI BIYU Where stories live. Discover now