Da Hausa tayi maganar na maida mata amsa akan ban fahimce taba.

"A'a dana ganki sai naga kina man kama da Hausa Fulani nayi tunanin ko ba Hausa ce ke Bara ta kawo ki nan"

Cikin mamaki nace;"Hausa???"

Wannan shine yaren masoyi na ai dan naji yana waya dashi nace mashi wane yare ne wannan yace Hausa ne, maganar ce ta maidoni daga duniyar tunanin dana fada.

Tace;"A Nigeria mana keba yar Nigeria bace?"

Ban san lokacin dana damki hannun ta ina murna murnar ma tasa na kasa fadar abinda ke bakina hadda hawayen dadi nayi saboda ina kallon wahala ta yanke.

Cikin yaren French nace;"Daga Nigeria kike??"

"Eh ni yar Nigeria ce"

Rungume ta nayi ina murna hawayen dadi na kara zubowa daga idanuna koba komi na hadu da yar kasar masoyi na.

Rabani tayi daga jikin ta saboda tsamin da jikina yake yi.

Cikin mamaki take kallo na tace;"Daga ina kike ne?"

"Daga Benin  nake zanje Nigeria ne neman saurayi na Baban Baby na"

Nayi maganar cikin jin dadi da murna ina nuna mata cikina.

"Saurayi kuma?"

"Eh! Eh"

Nayi maganar cikin tsantsan farin ciki gaskiya na dade ban samu farin ciki ba kamar yau.

"Nasha wahala sosai da sosai kamin na samu na tsalla ke border na iso nan, Ban taba zuwa Nigeria ba naji dadi sosai dana ganki"

Ganin tanaman wani kallo yasa na dan tsagaita daga maganar.

"Kunyi aure ne?"

"A'a"

Nayi saurin girgiza kai ina kallon ta ganin tanaman wani kallo.

"Ina iyayen ki?"

Shiru nayi bance komi ba sai sanda kaina da nayi kasa ina kara kallon kifin dake gaban ta.
"Ke Musulma ce?"

Eh"

"Ya sunan ki?

"Beedah"

Daga haka bata ce komi ba ta dauki kifin guda daya taban .

Cikin sauri nayi karab na amsa na fara ci cikin lokacin kalilan na cinye shi.

Mikewa tayi zata tafi na kama hannun ta nace;"Ke kade kikejin yarena dan Allah Ki taimaka ki kaini Nigeria"

Murmushi tayi kana tace;"Ni kinganni nan daga nan idan na samu na shiga Cotonou na kwana biyu zan wuce Togo daga nan zan wuce Ghana ba Nigeria zanje ba dan daga chan na fito Kinga babu yadda za'ayi na koma baya, Amman kema zan baki shawara kada kije Nigeria ki koma gida gaban iyayen ki kiyi rainon cikin ki, Hmmm mutanen Nigeria suna da banbanci al'ada dana kasar ku wanda yayi maki cikin nan bazai bari ki ganshi ba koda kin ganshi zaice bashi bane saboda bada aure kukayi cikin ba dan haka kizo mu tsallaka border dake zaifi..."

Bata ida fadin abinda zata fada ba na sake ta daga rikon da nayi mata idanuna cike da kwallan bakin ciki inajin inama ban hadu da itaba, Da tasan wahalan dana sha a baya da bata fadi haka duk wanda zaice kada na shiga Nigeria to gudun shi nake, Naguji iyayena saboda sunce kada naje Nigeria to babu wanda bazan gujemawa ba.

Ban kara kallon taba nabar wajen a guje ko waigota banyi ba dan ban san ganin ta bare muryar ta duk wanda zai hanani shiga Nigeria to maki yi nane babu ruwa na da halayyan yan kasar.

A bakin wani ruwa dake gudana naje na zauna ina shakar kamshin kasar hakan yaman dadi sosai, Shafa ciki na nayi ina murmushi ji nake kamar na haihu a yau ina son cikin nan da abinda ke ciki, Wani tunani nayi sai kuma nace ban son haihuwa anan ban ida shiga kasar Baban kaba.
Dan guntun tsoki nayi dana tuna da matar nan wai hadda tambayar munyi aure to minene nata da aure ko babu inde mutum yasan wannan dan shine ai duk daya ne wani dogon tsoki naja tare da saka kafafu na cikin ruwan inajin sanyin ruwan na shiga ta saboda ranar da ake.

ZAFI BIYU Where stories live. Discover now