Chapter 2

207 20 0
                                    

*The newest!*
*ABDUL-KHAFID*

*—•«Start on:..... »•—*

*_BEE SMART✍🏻_*

*WATTPAD: @Smart_Feenert*
_Joining My Wattpad Link:👇🏻_
https://my.w.tt/qyn8iY2cHcb

*_{🌳EMAIL- smartfeenert@yahoo.com🌳}_*

*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*_🌴BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM🌴_*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*CHAPTER: 2*

Tunawa ta yi da awakin da take kiwo a gida, murmushin k'arfin hali ta yi, a hankali ta tashi ta goya jinjirin a banta ta fita daga cikin asibitin.

Sai da ta yi tafiyar kusan awa2 kafin ta kai ga isa gidanta, sai dai tana shiga gidan ta tarar da babu awakan babu samatarsu, tunani ta tsaya yi yanda awakin suka kunce kansu har suka fita a gidan domin ita dai a iya saninta a d'aure ta barsu, fita ta yi waje bakin k'ofar gidan nata ta samu Samarin da ke zama nan kusa da gidan dik safiya har dare, ba aikin fari ba na bak'i sai dai tsabar munafurcin tsiya da yanzu mata suka bar ma Maza, sallama ta yi masu kamar ba zasu amsata ba.

A raunane ta ce da su "Dan Allah Iro ko kaga inda awakina suka je.!" dariya wanda ta kira sunanshi da Iro ya fashe da ita kafin ya ce da ita "Yo kin bani ajiyarsu ne da zaki zo kina tambayata su?.!" D'ai daga cikinsu ne wanda ke zaune gefe yana shan Sigari ya ce

"Kai baabaa dik fa yanda tsoho ya lalace indai ya haifeka to ka bashi girmanshi ko da shi ba abin girmamawa ba ne, illa dai ka yi iya taka-tsantsan da shi dan kar ya je ya jawo maka jagwal nan gaba, domin mutanen yanzu abin tsoro ne, kana zaune kawai sai dai ka ji an jangwab'o maka E-ya-ne, ko ba haka ba ne gayu?." dukansu amsawa suka yi da "Maganarka babu gyara ko kad'an Baabaa!"

Ya k'ara da ce wa "To kun gani.!" a sannan ya juyo hankalinshi ta wajen Inna dake tsaye tana saurarensu, ya ce "Eh to kamar d'azu munga wannan d'an Jakin naki Auwalu da d'an akuyan nan naki Faisal, sun fito da E-ya-ne rigija-rigija sun bi hanyar kasuwa street to saidawa! Eh ko ba haka turancin ya ke ba Iro?.!"

Kai tsaye Iro ya ce "fad'i kanka sake Abokina, indai zagi ne mutum bai ma fara shanshi ba tukunna dan wannan ma bugun number ne.!" dukansu dariya suka fashe da ita inda ita Inna tun lokacin da ta gama jin yanda abin ya ke ta bar wajen zuciyarta sai k'una take mata, hawaye ne ta ji sun fara zubo mata, wanda da suna karewa da a wannan ranar sun dad'e da k'arewa, fitowa ta yi waje ko kofar gidan ba ta tsaya kullewa ba, ta shiga neman rance gida-gida, inda dik inda ta je ba wasu kalamai masu dad'i da take tararwa, ta rasa inda zata saka ranta tun 9:00am take tsaye har wajen 5:00pm bata zauna ba dan shi kam abinci ba a ma batunshi domin ita har ta manta da wani abu wai shi abinci, Yaron kuwa sai kuka yake da ya motsa sai ya koka, ba zaiyi shiru ba har sai lokacin da wani baccin ya sake d'aukarshi.

Gidan wata Dillaliya ta tuna da shi da ke cikin layin unguwarsu, kai tsaye ta wuce can d'in, anan ne Allah ya k'addara zata samu inda kafin a bata kud'in sai da aka goranta mata duk da wannan shi ne karon farko da ta je neman rance a wajenta, dubu ashirin ta samu a wajenta da sunan bayan sati biyu zata maido mata da abinta sannan zata ninka kud'in gida biyu kafin ta kawo mata, ma'ana dai kud'i da ruwa, haka Inna ta amince sabida girman buk'atar da take cikinta, k'asa ta taka zuwa wata babbar super market ta saya ma jinjirin Madara ta 3000 sannan ta dawo gida ta had'a masu abincin da zata tafi da shi asibiti, ana kiraye-kirayen sallar magrib ta gama komai ta yi alwala ta yi sallah tana gamawa Jinjirin ya farka ya fara kuka, a gaggauce ta had'a mashi Madarar ta bashi ya sha

Ganin yanda yake shan madarar ne ya sakata zubda hawaye domin ita kanta ta san wannan jarabta ce daga ubangiji, domin shi kad'ai ya isa ya jarabeka ta ko wacce irin siga domin ya jarraba girman imaninka, "Alhmdu lillah" ta ce a dai-dai lokacin da ta ji yaron ya saki cokali har ya runtse idanuwanshi, wanda cike da hamdala take kallon yaron tana jinjina irin girmanshi, domin sam-sam baiyi kama da yaron da aka haifa jiya ba, gashi fari dan lukuti da shi ga kuma tsayi kamar ba jinjiri ba, d'an k'aramin bakinshi ta saka d'an yatsanta ta tab'a wanda hakan ya sakashi motsa bakin sai da dimples d'inshi suka bayyana ta ko wanne gefe, ga gashin kanshi da ke kwance lumi-lumi sai girarshi da ke bid'ar ta had'e da d'ayar dik da ta jarirai ce amma hakan bai hana bayyanarta ba, sai idanuwanshi da suke masu d'an girma wanda idan ya d'an d'aga girarshi za kaga sun d'an shige ciki abin gwanin ban sha'awa, murmushi ta yi ta ce

"Allah ya albarka ce rayuwarka, ya kareka da ga tsangwama ta mutane wad'an da ba su san kaddara ba.!" Mik'ewa ta yi tsaye ta sab'ashi a bai, ta d'auki mayafinta da abincin ta yi gaba, tana fitowa waje ta shiga kulle k'ofarta wanda tun daga nesa ta ga an danno mata fitila irin mai mugun tsinin nan irin ta b'arayin kaji, kasancewar ba hutar nepa a unguwar, murmushi kawai ta yi ta ida rufe k'ofar ta ta domin ta san wannan ba aikin kowa ba ne sai na su Iro, wajensu ta zo ta rab'a zata wuce ta ji Iro na cewa

"Ai ka ga irinta nan, wannan shi ne aikin kullum, sai an kyakyace idanuwan mutane basa nan, sai a sulalale abar unguwar gaba d'ai, ba za'a dawo ba kuma, sai tsakar dare! Hmm! Allah dai ya shirya su O'o, ace mutum tsofai-tsofai da shi baya ma tunanin kwanakin da suka rage mashi a duniya amma sai d'an banzan yawon dadiro?"

Wani daga cikinsu ne ya ce "To ni ma dai tayani gani Iro.!"

Iro ya ce "Aiko ba zamu tab'a barin irin hakan na ci gaba da faruwa a unguwarmu ba Sule! Ace a unguwarmu kuma mahaifarmu ana samun irin wad'an nan Karuwa da Kawalai kuma mu zuba ido muna kallon abinda suke muna a unguwa?! Me kuke tunanin akan abinda zai iya haifarwa nan gaba idan har muka k'yalesu.......?."

Cike da damuwa Inna ke tafiya har bata ma ganin hanyar da take bi, domin dik irin mugayen kalaman da su Iro ke yi akanta dik tana jinsu kiri-kiri, akan hanya ta samu Napep ta tara ta shiga, da k'yar dai ta samu ta isa cikin asibitin, cikin ikon Allah ko da ta je ta samu Zubaidah har ta tashi zaune ta d'an gincira kanta a bango d'akin, gefen da gadonta yake, tana kallon sillin..........

The newest ABDUL-KHAFIDWhere stories live. Discover now