Paapa yana dariya yace "Sadiq is here to stay in our lives Baby.. he is practically my son tunda mahaifinshi was my very good friend.. Maganar biyan shi kudin shi kuwa bai taso ba don kamar yadda na fadi miki ya ba kamfanin kudin kyauta ne kuma banda abinki, ina na ga kudin da zan biya shi??? do you know the huge amount of money that he invested in the comapny?? not to mention debts din da yayi settling... Please Baby ki qyale shi ya huta haka nan"

turo baki tayi tace "toh shikenan Paapa.."

Paapa dai murmushi yayi yana mamakin Hanifa.. he never thought cewar zata tsani Sadiq har haka.. shi kam da farko yayi tunanin they will get along especially ganin yanayin rayuwar Sadiq very simple..

"Yauwa lest I forget Paapa, anjima zan fita.. zan je shopping"

"hmmmm, Baby kullum shopping ba kya gajiya.."

Dariya tayi tare da fadin "Paapa bazaka gane bane"

"Ni kuwa na gane tunda you can't save a single dime in your bank account" ya fada yana hararar ta.

Tana murmushi tace "zan fara saving kwanan nan"

☆☆☆☆☆☆☆☆☆

Wuraren qarfe biyar na yamma Paapa da Hafeez suna zaune a babban falon gidan suna kallon news suna hira.

Mamy ce ta shigo riqe da tray mai dauke da bowls na fruit salad.

Hafeez ya miqe da sauri ya nufi wurinta ya karba yayinda Paapa yace "ke kam Mamy ba kya gajiya.. instead of ki ba maids su kawo, I see that you will never change" ya qarasa maganar yana murmushi.

Mamy wadda ta sakar ma Hafeez tray din ce tace "Paapa yana da kyau in dinga motsa jiki besides you know that I prefer doing these things by myself"

Hafeez ya ajiye tray din a kan side stool wanda yake kusa da Paapa yayinda ya dauki daya daga cikin qananan bowls din zai fara zuba mishi...

Wayar Paapa ce tayi ringing na ga ya duba.. sunan Hanifa ya gani.

Ji nayi yace "Baby hooo, I wonder what the complain will be yanzu"

aikuwa yana answering call din tun kafin yayi magana na ga ya zaro idanuwa yayinda ya miqe da sauri dafe da qirjin shi... hankali a matuqar tashe yace "what??? where is she???..."

Mamy da Hafeez suka mayar da hankulan su kan shi yayinda suka zuba mishi idanuwa babu ko qyaftawa..

Gani suka yi ya saki wayar ta fadi qasa yayinda ya fara fadin "Inna lillahi wa'inna ilaihir raji'un.."

Mamy ce ta riqe shi tace "Paapa me ya faru??" Yayinda Hafeez yayi saurin daukar wayar ya sa a kunne yana sauraron mai magana on the other side of the call.

Mamy wadda take riqe da Paapa dai ji tayi yace "Hanifa..." daga nan kuma sai ya zame ya fadi akan kujera sumamme.

Aikuwa nan da nan ta fara salati tana kuka yayinda Hafeez ya jefar da wayar hannun shi a rude ya dawo kan Paapa...

toh fa.. me ya faru kuma??

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

BRISTOL PALACE HOTEL
NASSARAWA-GRA

Kwance yake a kan three-seater kujera na lounge din deluxe suite dinshi. Mai karatu da ganin yanayin Suite din zaka amince ya ci kudin shi don kuwa babu wani abin more rayuwar dan Adam da babu a cikin shi... it's more like a home!!

Ko ina na Suite din looking spotlessly clean kamar ba mutum bane yake zaune a ciki.. Wani lafiyayyen qamshi yake tashi wanda ya hadu da sanyin AC ya bayar da wani yanayi mai dadin gaske.

RAWANIN TSIYA | ✔Where stories live. Discover now