Part title

13 1 0
                                    



*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga  shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*RASHIN ADALCI 2021*

             *NA*

*HUSSY SANIEY*

Page 1

Wata matashiyar budurwace kwance saman gado, ta fitar da ɗaya hannunta  daga cikin bargon da take lullube, ta ɗauke wayarta  da  ke ajiye gefen filon da ta dora kanta a kai.

Tana ɗaukar wayar ta mayar da hannunta  cikin bargon ta kara lullubewa har saman kanta, ta kunna datar wayar  babu ɓata lokaci messages(sak'onni)su kai ta shigowa tsayawa ta yi har suka gama shigowa wani group da tafi so a dukkannin groups din dake wayarta ta shiga,sallama ta yi cikin group din wani friend(abokinta)dake kusa ya amsa mata sallamar.
Gyara kwanciyarta ta yi domin taji dad'in yin chat ɗin, "Abdul ina sauran mutanen group ɗjn suka shigane su fito muyi fira mana?".

Dariya Abdul ya yi kafin ya ce; "kinsan mutanen gidan tsoron sanyi suke suna chan kwance har yanzu basu tashi ba".

Murmushi Husna ta yi tace; "ai na yadda matsoratane sai sun zo kaji yadda zasu cika mana gida da surutu".

Dariya Abdul ya yi nan suka cigaba da firarsu, sun kai wajen minti talatin kafin wani ya shigo.

"Kai waye ya faɗa maku sanyine ya boyemu?" Inji wani Mubarak da shigowarshi kenan ya samu suna maganar ya shiga shima,(shima Mubarak yana cikin members ɗin group din).

"Husna kin ga ɗaya nan ya fara leƙowa har ya fara cika mana baki koh?"  Cewar Abdul

Husna ta ce;  kyaleshi Abdul borin kunya ne tun yaushe muke nan muna fira ba wanda ya tashi sai yanzu"

Mubarak ya ce; "Injiwa yace yanzu nazo? tun ɗazun Ina kwance Ina kallonku".

Husna ta turo irin sticker ɗiin nan wadda ake amfani da ita gurin nuna alamun anyi murguɗin baki.

"Ke waki ke murguɗa ma baki? Inji Mubarak.

Husna ta sake turo wata sticker ɗin irin ta gwalo kafin daga bisani tace; "da kai nake".

"Ke yarinyar nan kin raina mutane sai na kamaki za kiyi bayani ni dai kike murguɗa ma baki koh?"

Murmushi Husna ta sa ke yi kafin tace;  "naga zaka zo mana da wata bidi'a ne bayan kaje ka kwashi baccinka amma zaka fara cika mana baki yanzu".

"Husna ke kike tsayawa ma bashi amsa Mubarak ɗinne zai iya jurewa ana magana ya yi shiru?" cewar Abdul

"To nagane kai ke sanyata yi man rashin kunya kenan zanyi maganinku gaba daya kuwa"

Dariya Abdul ya yi sannan ya ce: "gaskiya ai ta faɗa borin kunya ne kake mana bayan yanzu kazo".

Dariya Husna ta rinƙa yi ma Mubarak tana faɗin "Malam kayi ladab saboda nan dai mun ganoka"

Mubarak ya ce; "Hmmm yarinya za kiyi bayani dalla-dalla dani kike zancen".

Abdul ma ya rinƙa dariya ya na fadin "daɗina  da kai abokina saurin shiga yanzu har ka sakarmata ta fa yi galaba akan ka kenan"

Husna cikin sauri ta turo sticker mai ɗauke da alamun zaro ido tace; "haka ka koma Abdul?"

Dariya Abdul ya turo da ita bai ce komai ba.

Mubarak ya ce; "ƙyaleni da ita aboki zan rama dani take zancen ai".

Husna tace; "Ni zaku nunawa  ban-bancin jinsi bari kakata tazo nasan zata shigar man"

"Dalla matsa gefe ai wannan kakar taki ita ma zata taddamu dama ita ke sawa kina mana rashin ji cikin group ɗin nan" inji Mubarak.

Husna turo wata sticker ɗin tayi mai alamun mutum zai kai bugu tace; "Eh Ina ruwanka kakar kace ko tawa,kuma babu wanda ya isa ya takura mana gidan nan ni da ita eheeey".

"Haba yarinya jikinki zai gayamaki mu dai kike ma haka koh?" Inji Abdul.

Husna tace, "Eh da ku nake ni bari ma nayi tafiyata tunda kakata bata fito ba sai anjimanku".

"Yauwa gara ma kiyi tafiyar taki ko mun huta da yen yen yen ɗinki", Inji Mubarak.

"Ƙara gayamata abokina wannan yarinyar duk ta ishi mutanen gidan nan", Inji Abdul.

Dariya Husna tayi tace; "wallahi kun dai faɗa ne kawai amma ai basu iya rayuwa idan babu ni cikin group ɗin nan ni ce fa farin cikin gidan"

"Ke koma gefe kada na dake ki wacece farin cikin ko dai ciwon kanmu ba" cewar Isa da zuwanshi kenan cikin group din ya datsi maganar.

"Ƙara gayamata dai Isa wannan yarinyar sai munyi maganinta cikin gidan nan" nji Abdul.

"Ha ha ha naku wasane maganina ai sai Allah ba dai ku ba, bayan ma idan babu ni kun rinƙa kiran wai ina Husna baku da natsuwa har sai na hau",  ta fad'a tana dariya saboda tasan ta jawosu kenan.

"Je kiyi ta istigifari yarinya dan wannan saɓone ki kayi waye yake ta ke" Inji Isa.

"Ban da lokacinka Malam ni dai na faɗa kuma kun sani nice farin cikin gidan nan dan haka na mayi tafiyata"  Husna na faɗar haka ta rufe datar wayarta tana dariya saboda ta san ta tsokano su.

"Yarinya dole ki ruga tunda kinsan mataki zamu ɗauka amma zaki dawo ai" cewar Mubarak.

*Hussy Saniey *🥰

RASHIN ADALCINơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ