2

1.5K 148 8
                                    

*KUNDIN HASKE*
          
        Al’kaluman marubata

   KUNGIYAR:-
HASKE WRITERS ASSOCIATION
(home of expert and perfect writers)

*TARE DA AL KALAMIN*

*ZEE YABOUR*

*BABI NA GOMA SHA BAKWAI*

_..... Mabud'in wahala_

*02*

    K'arar wayarta Nokia mai torchlight, Ya tashe ta, Ta jawo wayar hankad'an pillow, Ganin mai kiran ta saki murmushi, Ta danna receive, "Assalamu Alaikum", " Wa alaikissalam Habibty", "Ya Nurah ina wuni?", " Lafiya lau, bacci kike?", "Eh", "Toh ki tashi lokacin sallah yayi, nima na fito zani masallaci", " Allah ya tsare ya kai ka lafiya", "Amin, Ya jarabawar?", " Alhamdulillah, gobe zamu gama", "Allah ya bada Nasara", " Amin", "Sai na kira ki anjima, ki kular mun da kanki", Ta amsa da " In Shaa Allah"

    Mik'ewa tayi ta fita waje, ta d'auki buta tayi alwala, Ta gabatar da sallar la'asar, Ta fito ta d'aura sanwar tuwo, Umma ta d'auro miya,

    Tana jiyo Rahma daga sashen su Gwaggo na fama da ita ta tashi ta d'aura tuwo, tana fad'in kanta ke ciwo tayi jarabawa ta gaji, "Toh koma ki kwanta, bari na d'aura", Tana mamaki hali na Gwaggo yadda ta sagarta yaranta.

    Lukman ya kira Rahma, ya bayyana mata yana sonta kuma aure yake so suyi, babu jan aji ta amince, Shima yayi mamakin amincewar ta da sauri, but ya lura Yarinyar akwai rawar kai, Shi dai muradinsa ya auri kyakkyawa, mai diri, ba kidahuma ba, Ya samu hakan a tare da ita, Ranar raba dare sukayi suna waya, batayi karatun komai na jarabawa ba.

     Sameerah basu dad'e suna waya da Ya Nura, Yace tayi karatu, Sukayi sai da safe.

  Kusan minti 20 da gama shirinta, but Rahma bata fito ba, Ta duba agogon wayarta k'arfe 9:20, kuma k'arfe goma zasu shiga, " Umma bara naje na dubu Rahma kada mu makara", "Toh daga can ku wuce", " Allah ya bada sa'a da nasara", Ta amsa da "Amin"

    A bakin k'ofar d'aki ta tarar da Gwaggo, Ta duk'a ta gaisheta, Ta amsa da k'yar tana yatsina fuska, Rahma na gaban madubi tana kwalliya, ta d'auko janbaki tana shafawa,

     "Haba Sister kinsan fah 10:00 zamh shiga exams, amma kin tsaya kwalliya", " Yau ce ranar k'arshe haka kike so naje da fuska na maik'o", "Ni dai ki bar kwalliyar nan mu tafi",

    Daga waje ta jiyo muryar Gwaggo " Ba zata bari ba, idan ke haka zaki da fuskar kamar ba mace ba, ita sai ta kimtsa, ke Rahma kwantar da hankalinki ki matso kyau", Sameerah tayi shiru ranta ba dad'i.

    Turare ta d'aura ta fesa, Ta sab'i k'aramar jaka, Tace "Mu tafi", Sameerah tayi gaba, Tazo fita Gwaggo ta bita da harara, " Yarinya mai k'ashin arzik'i Allah ya nuna mana aurenki ya kai ki babban gida", "Amin Gwaggo na",

   Sameerah ta girgiza kai, instead ta mata addu'ar miji nagari amma ta babban gida take, Allah ya shirya.

     A napep take bata labarin saurayin jiya sonta yake kuma auren ta zai yi, Ta amince.

   " Daga ganin sarkin fawa sai miya tayi zak'i", Rahma ta harare ta tace "Ban gane ba" , "Daga had'uwar ku, baki san halayyar sa ba, ai ya kamata ki fara karantar halinsa kafin ki amince", " Wane halinsa zan karanta, ga kyau, kud'i da gayu daga Allah ya kashe ya bani", "Ba sune rayuwar aure ba", " Kinga dakata idan akwai kud'i to akwai komai, sune rayuwa, idan kinga miji da mata na yawan samun sab'ani babu ke kawo haka, kud'i sune ginshik'in zaman lafiya da farin ciki a gidan aure", "Kina kuskure Sister, Miji nagari da mace tagari ke gina gida nagari, da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali mai d'aurewa"

    "Wai ko bak'in ciki kike mun dan na samu mai kud'i", " Haba Sister, ni shawara ce nake baki", "Toh bana so, kiji da Nuran ki, ki barni da Lukman d'ina", Sameerah taja bakinta tayi shiru,

    Ko da suka isa, an fara shiga, Cikin hanzari suka bi layin shiga.

    Jarabawar tayi ma Sameerah sauk'i bata dad'e ba ta fito, Rahma sai faman cizon biro take, tana raba ido ko zata samu satar amsa, Ganin yadda take waige waige, Invigilator ya karb'e yace ta fita, Rai a b'ace ta fito

    " Can maka, an fad'a maka na damu da Waec d'in, da na auri mai kud'i shikenan, ba ruwana da wahalar neman kud'i, sai dai a bani naci nasha, na kwanta", Taja tsaki,

   Sameerah ta kalleta ta girgiza kai, ba abun ta mata magana ba, ta chab'a mata bak'a.

   Sameerah taso su wuce gida, Rahma tace su tsaya suyi hotona da classmates d'insu, Ta shige cikin maza ana ta hoto, Sameerah na gefe, idan aka mata magana tazo ayi, tace kanta ke ciwo, Ta dai karb'i numbobin wasu matan ajin.

     Cike da farin yau ta kammala sakandire ta dawo gida, Umma ta shiga yi mata addu'ar samun nasara, dafatan zaman lafiya da kwanciyar hankali a gidan mijinta idan Allah yayi aurensu da Nura, Duka yaran gidan suna gama sakandire ake musu aure, Tun tana Ss1 aka yi baikon su da Nura.

    Iyayen Nura ba masu kud'i bane, Mahaifinsa kayan miya da man gyad'a yake siyarwa, Mahaifiyarsa na sana'ar cikin gida na siyar da k'uli, yaji, kuka, daddawa da sauran su, Da haka suke rufewa juna asiri, Nura shine babban d'an su yaro mai hazak'a da son neman na kansa, Gyaran wayoyi yake, ta haka yayi karatun sakandire, Yaje poly yayi diploma, Yana ta neman aiki ya gagara, k'annen sa biyu mata Aisha da Fatima, Aisha tayi aure tana gama sakandire, Fatima na Ss2 a wata makarantar gwamnati nan unguwar su.

    Nura nada tsananin ibada da halayyar nagari, sau da yawa shi ke jan sallah a masallacin unguwar su, Sun had'u da Sameerah ne ta sanadin gyaran waya da ta kai masa, Ya yaba da hankali da natsuwarta, Ya nuna mata soyayyarsa, Ya d'an sha wahala kafin ta amince dashi, Halayyar sa ta yaba da ita, kuma yana da kyawun sa.

    Gidansu ba irin tsegumin da ba'ayi ba, Ta jajubo talaka ta toshe kunnenta, Rahma kallo Nura bai isheta, ta raina ajin sa.

    Kayan baiko da aka kawo kwali d'aya sai goro da kud'i dubu biyar, Haka Rahma da sauran yaran gida suka tasa ta gaba, suna mata dariya, wai a zamanin da ake kawo kaya kamar za'a bud'e shago ita kwali d'aya ko arzik'in biscuit babu, Tayi kunnen uwar shegu dasu, Umma ta k'ara gargad'inta kar ta sake ta d'auki zugar su, Kud'i ba sune aure ba, Halayya nagari.

     Yan d'akinsu kad'ai ke ganin girman Ya Nura, but sauran basa ganin shi a bakin komai, saboda bashi da arzik'i.

    Tana tub'e uniform, wayarta ta d'auki rurin, Ta d'auka ta kanga a kunne, Yayi sallama, ta amsa masa,

    "Ina taya Masoyiyata murnar kammala makaranta, Allah yayi ma karatu albarka, yasa aga sakamako mai kyau", " Amin Nagode", Ya Nura yace "Babu godiya tsakanin mu gimbiyata", Tayi murmushi tamkar yana gabanta, " Anjima zanzo", "Allah ya kaimu", " Amin", Ta kashe wayar cike da zumud'in ganinsa kwana biyu basu had'u ba.

    Rahma ta cire uniform, ko kaya bata saka ba, da d'aurin gaba ta jawo wayarta k'irar tecno android, Da masifa ta had'a kud'i, Gwaggo ma ta bata ta had'a ta siya, Number Lukman tayi dialing, Bugu d'aya ya d'auka,

     "My baby", Ya fad'a, " Nayi fushi baka kira kaji ya jarabawa ba", "Am sorry wani aiki ya tareni", " Toh naji", "Ina busy yanzu, anjima zanzo", " Sai kazo", Ta fad'a tana kashe wayar, "Shi kullum busy, ba kamar Nuran Sameerah a rana sai ya kirata sau biyar"

    " Ke dallah wannan mai zaman kashe wando, dan ban raba sana'ar sa da haka ba, ina zaki had'a shi da mai kud'i, su da abubuwa ke ma yawa, k'ila ma kirgar kud'i yake", Gwaggo ta fad'a, Tana jin haka ta saki murmushi har hak'oran ta na fitowa, Tace "Hakane anjima ma nasan yazo zai bani yan canji", Gwaggo tace " Dole ma",

*ZEELISH*

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now