Babi na takwas_Hafsat Rano

2.6K 187 4
                                    

*KUNDIN HASKE*

*AL-K'ALUMAN MARUBUTA...*

✍🏻

*_NA KUNGIYAR:-_*
     _HASKE WRITERS ASSO...._💡

*TAREDA AL-K'ALAMIN...*
       *_Hafsat Rano_*

*_WAYAR MIJI😭_*

*BABI NA TAKWAS.*

     *SHAFI NA DAYA...*


*GIDAN IDRIS*

Da sand'a ta nufi  wajen da ya ajiye wayar tana murmushi,
"Yau zan ga me kake aikatawa, yadda kake kaffa-kaffa da wayar nan."
Da azama ta d'au wayar, cikin sa'a kuwa ta samu wayar a bud'e ba wani samaki, ba bata lokaci ta danna kan shud'in application me nuni da Facebook.
Gaban ta ne ya fad'i ganin sunan Linda da koren rubutu a saman ak'watin sirri, hannu na rawa ta danna ta shiga kan sunan, ta fara yin sama tana son kamo farkon hirar...

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un." Shine abinda Ta furta tana k'ok'arin gasgata abinda idon ta yake gane mata, runtse idon tayi da sauri ta bud'e tana son tabbatar da abunda take gani k'wance akan screen d'in wayar Idris. Wani irin jiri ne ya d'ebe ta a take ta zube a wajen, cikin muryar kuka ta shiga furta wa kamar wata tababbiya,

"Haba Idris! haba Idris!! kar kayi mun haka mana, wayyo Allah nah, na shiga uku." Bubbuga kanta ta farayi a jikin kujera tana kiran  sunan Allah, tana furta kalmar
"Why! Why!! (Mesa! Mesa!!)

☆☆
"Swthrt! Swthrt!!" Ya bud'e murya lokacin da ya fito daka band'aki be tarar da ita a d'akin ba.

Jin motsin bud'e kofa yasa ta saurin ajiye wayar ta share hawayen fuskarta da sauri da tafin hannun ta.

Turus yayi ganin ta a zaune a kasa hannun ta rike da kanta tana jujjuya shi kamar wadda ake shirin zare mata rai..
Dam!!! K'irjinsa ya buga yayi maza ya kalli in da wayar sa take, sauke ajiyar zuciya yayi, yayi saurin karasa wa gareta.

"Me ya faru rabin raina?" Ya furta cikin kulawa yana kok'arin d'agota.

Wani abu kamar guduma ya daki k'irjin ta, zuciyar ta ta turnik'e ganin yadda ya wani langa'be kai,

"Munafiki." Ta furta a ranta, sannan ta daure ta kak'alo murmushin da be kai zuci ba;

"Kaina ne naji ya sara mun sosae, kasan yadda migrane (Ciwon kan bari d'aya) d'in nan yake damuna.
"Ayya sannu kinji Bbynah, tashi maza ki d'auko hijabin ki muje asibiti."

Sai data fara karanto masa Allah ya isa kafin ta daure ta k'ara k'ak'alo murmushi bayan ta janye jikinta daga gareshi tace;

"A'ah ba sai munje asibiti ba ma, ina barci shikenan."
"Kina ganin zai daina in kinyi barcin?" Ya k'ara furtawa cikin kulawa yana kok'arin rik'e mata hannaye. A wayance ta kauce ta nufi hanyar bedroom(Dakin k'wana) tana matsar k'wallar data silalo da fito. Bin bayanta yayi da kallo har ta shiga had'e da rufo kofa.

Wayar sa ya jawo, yana addu'ar Allah yasa Linda bata gaji da jiranshi ba ta sauka.

"My Swttest bby." Ya rubuta mata yana gyara k'wanciyar sa akan doguwar kujera. Wani d'an dodo me alamar bacin rai ta saka, hak'uri ya shiga bata  har sai da ya samu ta sauko, nan suka cigaba da maganganun da suke marasa kyau.
   Cikin dare barci ya kaura cewa idon Na'ima. Duk sanda ta runtse ido babu abinda take gani sai chat d'in Idris da Linda. Ba karamin mamaki take ba,sam bata taba kawowa Idris zai mata irin wannan cin amanar ba, ace yama rasa da wadda zai yi mu'amala irin wannan sai arniya wadda bata san me addini yake ciki ba. Tabbas hausawa sunyi gaskiya da sukace; "Mutum mugun icce.

Sake gyara k'wanciyarta tayi had'e da sauke numfashi. Farkon had'uwar su da Idris ta shiga tunowa da irin kaunar da ya nuna mata.

   Yammaci ne me cike da ni'ima, sanye take da kayan islamiya shud'i da farin hijabi, hannunta rataye da jakar Al'kur-anin ta.
Karar horn taji a bayanta, wanda sam bata da alaka da wajen da mota zata wuce, hakan yasa tayi biris ta cigaba da tafiyarta. Jin k'arar na kuma matsowa inda take yasa ta dakata wa gami da juyowa.
Zaune yake cikin motarsa k'irar Honda Civic ruwan makuba. Ganin ta tsaya yasa matashin saurayin wanda ak'alla zaiyi irin shekara talatin d'in nan balle murfin motar ya fito.
"Assalamu alaikum Malama me d'unbin ilimi."
"Wa alaikasalam." Ta amsa kai tsaye tana k'ok'arin cigaba da tafiya. Da azama yayi saurin tsaida ta, ta hanyar bin bayanta. K'in kulashi tayi ganin ta zo gida, da sauri ta karasa shigewa zauren gidan ba tare da ta amsa kiran ta ya biyota yana yi ba. Murmushi yayi ya shafa sajen fuskar sa.
"Babu komai tunda naga gidan ai." Yana shirin juyawa sai ga karamin kaninta Habibu ya fito rik'e da naira hamsin yana lank'wasa ta.
"Abokina." Idris ya furta yana sakin murmushi,
Kallon rashin sani Habibu yabi shi dashi kafin daga bisani yace;
"Ni ba ruwa na dakai, Mama ta hana mu magana da wanda bamu sani ba." Murmushi yayi kafin yace;
"Banda ni Mama ai tace karka kula, nifa abokin Antin kace da ta shiga yanzu gida." Kallon sa Habibu yayi kafin ya amsa masa;
"Mu bamu da Anti sai Yaya Na'ima kawai."
"Eh.. Eh.. Ai dama Yaya Na'iman nake nufi." Da haka ya samu yayi wa Habibu wayo har ya aike shi ya kira masa ita. Fafur taki fitowa bayan ta jawa Habibu kunne akan karya dameta. Ba yadda ya iya haka ya tafi da niyyar sake dawowa a karo na biyu.
  Sosai Idris yasha wuya kafin Na'ima ta amince masa, soyayya me kyau da tsafta sukeyi wa junansu, babu wata alamar yaudara ko maganar banza da Idris ya taba yi mata a iya lokacin da suka d'auka yana zuwa wajenta.
  Sake juyawa tayi kad'an har ta d'an gogi kafar Idris wanda yake ta barcin sa harda minshari.
  Lokacin aurensu ta tuno da irin yadda Idris ya dage akan babu wata bidi'a da zasuyi. Haka akayi auren cikin jindadi da farin ciki.
Tana gama tunanin ne taji kuka ya taso mata, tayi saurin sa hannayenta duk biyun ta toshe bakin gudun kar Idris yaji. Sai datayi me isarta sannan ta share hawayenta gami da rok'on Allah ya yaye mata damuwarta. Ba ita ta samu ta runtsa ba sai gabanin asubah.
   Zaune yake wajen karfe goma da rabi na safe, wayarsa ce a hannun sa suna gaisawa da mutuniyar tasa Linda, maganganun banza da suka saba yiwa juna yau d'in ma suke.
  Da sauri ya kalli kofa, Na'ima ce ta fito cikin sanyin jiki ta k'araso cikin falon, gefen k'afarsa ta samu ta zauna tana kokarin kauda kanta gudun had'a ido dashi. Ganin haka yasa Idris yasha jinin jikinsa, yasan tabbas akwai abunda yake damun Na'imar sa.
"Ina k'wana?" Ta katse mishi tunanin da ya tafi. Zamowa yayi daga kujerar ya zauna kusa da ita, yana son saka k'wayar idonsa cikin tata, kauda kanta tayi tana jin kamar zuciyarta zata faso.
"Kalle ni Wife(Matata)." Sake d'auke kanta tayi tak'i kallon sa don tasan tabbas in har ta yadda suka had'a ido ba abinda zai hana hawayen da take boyewa su sakko. Hannu yasa ya tallafo fuskarta gami da juyowa da ita tana fuskantar shi;
"Subhanallah..! Me zan gani Wife(Matata) kuka? Kuka kikeyi? Mene ne? Don Allah fad'amun. Nine ko? Me nayi?" Duk a jere ya jefo mata wad'an nan tambayoyin. Wannan kulawar tasa ita take k'ara sawa taji gaba d'aya ta tsani kanta, kowa yanzu a matsayin mayaudari dake kallonsa.

"Swttest Bby, i swear to Almighty God am single, Am not married. Believe me.(Na rantse miki da Allah bani da aure, ki yarda dani)." Wannan ne d'aya daka cikin abinda yafi d'aga mata hankali a cikin chat d'insu da Linda. Kuka ne ya kwace mata had'e da wata irin tsanar sa, da karfi ta k'wace daga rik'on da yayi mata ta ruga da gudu ta shige d'aki.

Kan gado ta fad'a ta saki kuka me karfi, cikin wani yanayi numfashinta ke kaiwa da komawa, ji take kamar an d'au gungumemen dutse an d'ora mata akan k'irjinta .
"Don Allah Wife(Matata) ki taimaka ki sanar dani abinda yake faruwa. Gaba d'aya kin saka ni a tunani wallahi." Ya fad'a yana tsaye a kanta. Banza tayi kamar bada ita yake ba, sai ma k'ara sautin kukanta da tayi.
"Ya Allah..! Wai menene don Allah?" Ya sake tambaya yana kok'arin zama kusa da ita.
"Baka san Allah ba wallahi, har kake kokarin had'ani dashi." Ta amsa mishi da sauri tana masa wani irin kallo.
  Cikin sanyin jiki Idris yake dubanta, anya kuwa wannan Na'imar sa ce, me sonshi da kaunarshi, ko dai aljanu sun taba masa ita ne.
  Dakewa yayi ya kai hannunsa gareta cikin sigar lallashi yace;
"Koma menene don Allah kiyi hakuri ki bar kukan nan haka, kar kije ki jawo wa kanki wata cutar don Allah."
"Ka daina had'ani da Allah Idris, don wallahi baka san shi ba, da ka sanshi wallahi da baka aikata abinda ya hanaka ba. Kayi gaggawar neman gafararsa." Kuka ne yaci karfinta, da sauri ta mike tayi hanyar toilet(Band'aki). Kasa binta yayi sai ma tsayawa da yayi yana al'ajabin maganganunta. Wani irin tsoro da fargaba ne suka shige shi a lokaci d'aya, tunowa da yayi da abinda yake aikatawa da Wayar shi.

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un." Ya furta da sauri.

"Kardai ace Na'ima taga hirar mu da Linda. Wayyo Allah in kuwa haka ne da wanda idon zan kalle ta?"

Kamar wani zararre yake sunbatu shi kad'ai, fita yayi daka d'akin da sauri ya nufi in da ya ajiyar wayar, kan chat d'insu da Linda ya shiga, gani yayi har ta turo masa wasu hotuna masu bayyana wasu bangarori na jikinta. Wa'iyazubillah. Da azama ya shiga goge wa yana fad'in "Astagfirullah! astagfirullah!" da karfi. Sai da ya tabbatar ya goge chat d'in duka,sannan ya danna mata block a take.
A suk'wane ya juya d'akin jin kakarin amai, Nai'ima ce tsaye cikin toilet(band'aki)a galabaice tana maida numfashi.
"Sannu."ya fad'a a d'an tsorace. Bata tanka ba sai ma rab'awa da tayi da gefensa ta fice daka d'akin. Bin bayanta yayi ya tsaya daka d'an nesa da ita yanason mata magana ya kasa. Sai data tabbatar ta samu nutsuwa sannan ta mik'e ta nufi kitchen (d'akin girki). Simple breakfast(Abinci me sauki) ta shirya masa kamar kullum ta jera masa anan tsakiyar falon, shiga tayi ta had'a masa ruwan wanka, ta fito masa da kayan sawar sa kamar yadda ta saba. Tana gama wa ta shige d'aki gami da rufo k'ofa.

☆☆
*GIDAN  JABIR*

Karfe 5:30 daidai agogon d'akin yayi kara, mikewa Jabir yayi ya shiga toilet(band'aki) ya d'auro alwala ya wuce zuwa masallaci.
  Khairat na ganin haka tayi saurin yin sallama. A gurguje bako addu'a ta nufi inda wayar Jabir ke chargi, ya manta garin sauri bai tafi da ita masallaci ba.
"Alhamdulillah.Dama ranar da nake ta jira kenan." Ta furta a hankali. Cikin azama ta shiga Whatsapp ta fara dube dube.
"Bilkisu!" Ta furta cikin mamaki,
Shiga kan chat d'in tayi, ta fara karantawa.
Baki sororo take bin chat d'in mamaki k'wance a fuskarta.
"Bilkisu!" Ta ka'ra nanatawa. Bilkisu aminiyarta ita ke hira da mijinta haka, kasa ta k'ara tana son gasgata abinda take tunani,
gani tayi Jabir yace:

"Ina nan ina jiranki idan kin gama school zan aureki."
"Kutm... ta lailayo ashar, cigaba da dubawa tayi tana sake zunduma ashar.
  Jabir ne ya shigo, ganin wayarsa a hannun Khairat, gaba daya sai hankalinsa ya tashi inda ya fara zagaye daga d'aki zuwa falo ya kasa magana. Chan yayi karfin hali yazo ya fuzge wayar.
"Jeki dauko mun ruwa zan sha." Ya bata umarni yana muzurai. Bud'ar bakin khairat sai cewa tayi;
"Bazan je ba."
"Meyasa?" 
"Oho!"
nan Jabir ya fara fad'a yana muzurai,
"Mesa zaki daukar mun waya?" Banza tayi tana wani rik'e k'ugu, k'ara maimaita yayi a k'aro na biyu. Cikin zafin kishi Khairat tace;
"Aikin banza kawai,wa zaka zarewa ido,shiyasa kullum in ka dawo gida baka da aiki sai danna waya. Ashe yanmata kake yiwa sakonnin soyayya, wanda ni matar ka ban isa ka fad'an su ba."
"Ni kike gayawa haka?"
"An fad'a maka, kayi abinda zakayi." Daga hannu yayi zai kai mata mari, kome ya tuno sai ya fasa, ya juya da sauri ya bar d'akin..

Rano💕

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now