13

1.1K 120 31
                                    

*KUNDIN HASKE*

    *Al-K'aluman* *Marubuta*

     KUNGIYAR:-

*HASKE WRITER'S* *ASSOCIATION* ( _Home of expert and_ _perfect writer's_ )

     *BABI NA GOMA* *SHA BIYAR*

     *KWAD'AYIN WASU* *IYAYEN.......*

  _Tareda Alk'alamin_

*Ayshat D'ansabo lemu* 🖊

               1⃣3⃣

"Lfy miye hakan kuma ? Daga zuwa zaki rungumeni kisaki kuka Ruk'ayyatu "

Ummah tayi mgn tana rabata da jikinta tareda k'arewa Ruky kallo ,tana mamakin yadda tasake lalacewa tarame sai fatan jikinta kawai daya nuna alamun hutu yai fresh......

"Maraba da Auta duk kewan umman ce yahanaki ganin kowa anshigo anata kukan shagwab'a "

Babah Hajjo tayi mgn tana ma Ruk'ayya kallon kurillah ,sai alokacin Ruky takula da babah Hajjo ta wadata fuskanta da murmushi tana fad'in

"Wayyo babah Hajjo yi hakury ina yini "

Ruky tagaidata tana míkewa ta nufi bedroom d'in umman yayinda babah Hajjo ke fad'in

"Lfy lau auta ya Amarci dafatan komi lfy naga duk kin sake zubewa ne, aita hakury zaman aure sai da hakury kidaina saka damuwa aranki komi ahankali ake sabo dashi "

Daga can bedroom d'in da Ruky ke jiyo mgn babah ta amsa mata da "Toh babah insha Allah ngd "

Bata wani jimaba tayi sallama da ummah da Ruky ta tafi, sai dai zuciyanta tab yake da mamakin yadda taga Ruky tayi tsammanin yadda suka kaita gdn hutu ganin farko dazata mata taganta shar tayi kiba , sai gashi kallo d'aya zaka ma Ruky kasan da mgn ko irin cikan d'aki da amare keyi bataga wannan ba

Ummah ce ta sanya kai cikin bedroom d'in nata , Ruk'ayya tayi d'ai-d'ai akwance tana danna wayanta , chart take da Zee tana sanar mata tafiyan da zasuyi da Kamal d'in

"Keh! Tashi maza kizauna muyi mgn wannan raman na lfy ne ? Meke damunki ? Kada kicemin haryanzu baki fitar da Ahmad aranki kin rungumi mijinki ba "

Ummah tayi mgn tana zama abakin bed d'in , yayin da Ruky ta tashi tazauna tana aje wayan hannunta , duban ummah tayi tana kokaryn fara share hawayen dasuka fara wanke mata fuska umman ce tasake mgn akaro na biyu tana fad'in

"Ina jinki wannan raman namiye ne keko irin cikar d'akin nan bakiyiba yadda Nadeeya tayi shar abn sha'awa da ita amma ke dubeki yadda kika sake lalacewa kaman ba gdn girma aka kaikiba , sbd kinsama zuciyanki bak'in hali ko "

Takare mgn cikeda takaici tamkar takai hannu ta make Ruk'ayya haka takeyi , wannan ma ai abn kunya ne aga Ruky haka yadda take alfahary takaita gdn girma da wadata

"Ummah bakisan irin zaman danake da Kamal bane , ummah nasha gaya muku wlh Kamal bai dace dani ba , Kamal bani yakeso ba ummah jikina kawai yakeso wlh umm........ "

Tsawan da ummah tadaka matane yahanata karisa abnd take niyyan karisawa, umman na fad'in

"Yimin shiru shegiyan yarinya me shegen taurin kan tsiya , arziki kullum yana binki kina kauda kai , bayasonki zai aureki ne ? Kawai kin d'auki karan tsana kinsa masa to bari kiji garama ki kwantar da hankalinki kici daulan dake gabanki Ahmad dake kulafuci akansa yai miki nisa , satin daya wuce akayi bikinsa da yarinyar yayan me waina uwarsa , don haka bansan jin kowani korafi akan Kamal , ki kwantar da hankali kiyi biyayya kowa namun murna kinsamu shiga cikin arziki wanda sai mace me sa'a kesamun auren yaran attajirai irinsu kamal , amma ke kinsamesa kullum cikin kushesa kike kina fad'in bakuda ce ba "

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now