page 05

1.3K 86 0
                                    

   Haki take tana faman sauke ajiyar zuciya sabida yadda zuciyarta tayi mata wani nauyi Launin idanuwanta yakoma jaa,Hawayene kawai ke ambaliya a idanuwanta wanda ta gaza tsaidasu domin barinsu tayi su zuba son ransu ko  hakan ka iya sa taji saukin radadin da zuciyarta ke mata,tana cikin wannan yanayin Elmoudan yafito daga dakinsu "Inteeesaar..."bai karasa maganar ba yakariso wurin da gudu yana me fatan Allah yasa lafiya,hannunsa yakai jikinta ze dago ta tayi saurin damke hannayenshi cikeda tsananin karfin dabatasan tana dashi ba,kara damke hannun take wanda Elmoudan ya gaza kwacewa banda kallon mamaki ba abinda yake binta dashi,seda tayi kimanin mintuna biyar ahaka sannan ta sa dukkan Karfin da Allah yabata ta hankadeshi yyi baya,ikon Allah ne yasa kansa be garu da console ba,mikewa tayi da sauri zata bar wajen yyi kokarin fincikota ta fado jikinshi,gabadaya ajiyar zuciya suke saukewa,da sauri tayi kokarin mikewa amma takasa dubaga irin rik'on daya mata bana wasa bane,murya asarke kuma adakushe tacr"sakeni.."...shiru yamata banda kallonta dayakeyi,"sakeni nace kafin naci mutuncinka".murmushin dayafi kuka ciwo yyi sannan yace"go ahead,kici mutuncin nawa,zanfison ki gaggauta cimin mutunci inteesaar,na tabbatar cikin mugayen maganganun dazaki fadamin zanji dalilin wannan rashin da'ar dakikemin. "Bakaramin tunzura tayi da maganganun Elmoudan gareta ba,yunkurin mikewa tasakeyi shikuma awannan lokacin beyi kokarin hanata ba,Tabbas Elmoudan yagama da rayuwarta ta yadda dukkan mai hankali baya zato,wato duk maganganun dayake fada mata karya yake?miye yake nema agurin YA MACE wanda batadashi?meyake so atattare da YA MACE wanda ta gaza bashi?meyasa yake cin amanarta?meyasa yake cin amanar auransu?meyasa yake nuna he's innocent while he's arrogant?meta rageshi dashi?har ta juya zata bar wajen wata zuciyar ta tunzuro ta juyo tareda kankance idanuwa,da hannu take dubanshi irin duban wulakanci kafin tace"tabbas men are irresistible and unreliable ,ba se na fada maka cewa kaji kunyah ba sbd kafini sanin hakan?meyasa zaka zauna kana tsaramin zancen banza zancen iska saboda ka kare bukatarka ta munafunci?meyasa bazaka fito fili is shaidamun cewar kai dan akuyah bane mai bibiyar yan mata,Wallahil azim Elmoudan sede kazaba koni ko Raliya,aikin banza kawai..."tana kaiwa nan tashige dakin ta tareda kulle kofar tana tunanin mafita,Tabbas sekin tashi tsaye zuciyarta ke shawartarta,wayarta ta daga takira Ziyada dake dinner tana kallo,ganin kiran Inteesaar yasa ta tuna da ita domin tun rannan dasukayi waya ta mata da lamarin aminiyar tata,"hello my one and only inteesaar"..."Ziyada ba wannnan ba ina cikin tashin hankali,ina cikin bala'i da masifa,Elmoudan na kokarin cire min zani akasuwa"..numfashi Ziyada taja sannan tace "meya kuma aikata maki?".."Ziyada chatt dinshi nagani dawata local prostitute,Ziyada Elmoudan na kokarin kasheni slowly,kinsan sarai shine rayuwata kuma yake aikatamin hakan "..."lamarinki is complicated Inteesaar."..."Ziyada find me a solution ba ki tsaya kina commenting situation dina ba"..."a tunanina it's high time mu fara neman sa'a wurin bokaye da malaman tsibbu,amma kuma wani hanzari ba gudu ba bana tunanin dakuwarki ta kawo nan,dabarunmu na mata ma sun isheki ki shawo kanshi karfa ki manta Elmoudan na mutuwar sanki shiyasa ma yake zaune dake da wannan dan iskan halin naki. ""Haka ne Ziyada amma me kike tunanin zanyi hankalinshi ya dawo gareni?Ziyada inason ya zamto ni kadai ce macen da Elmoudan ze iya sauraro,Ziyada kinsan am I insane when it comes to Elmoudan,kinsan what I am capable of doing akan Elmoudan,dan haka dan kutumar ubanki kizo gidana gobe dan musan yadda zamu ma tufkar hanci"..."Allah ya kaimu,amma it's high time dayakamata kirinqa sanin irin maganganun dazasu rinqa fitowa daga bakinki akan wani elmoudan ""Elmoudan yawuce ki kirasa dawani ,Yar iska kawai ke ina naki kamar Elmoudan din?na tabbatar baza ki taba samun me kyau da kudi kamar mijina ba don haka kada ki kuma zaginsa ko cin zarafinsa inba sokike muyi kaca kaca ba".."idan awurinki yakai haka ni awurina be kai haka ba,Allah ya huci zuciyarki sannan bawa baya cire rai da buri,kamar yadda baki taba tunanin zaki auri first class guy kamar Ahmed ba haka nima Allah ze kawomin Mr right dina soon"..."look at you dakinsan Allah ne keda ikon sawa da hanawa dabakiyi zancen neman sa'a wurin bokaye ba,anyways goodnight"ba ta jira cewar Ziyada ba takashe wayarta,jin Inteesaar ta kashe kiran yasa Ziyada jujjuya wayar tana tunanin irin halayyar aminiyartata.Tabangaren Elmoudan kuwa tsantsar mamakine yacikasa,taya idanuwanta zasu rufe haka?meyasa idan tana cikin giyar kishi take aikata komai agareshi?shin hankalinta daukewa yakeyi?ko kuma tanada mutanen boye ne be saniba ba?or is she psychologically unstable?shide yakasa gane kan wannan alamari
Amma duk da haka yaci alwashin seya rama zagin datamasa na dan akuyah tahanyar da bata taba tsammaniba,seya koya mata darasi zazzafa cikin rayuwar aurensu,kasa daukar wayar yyi sbd tsabar bakin ciki.Jidderh ce ke kwance akan italian bed dinsu fuskarta nakallon ceiling,hawaye ne ke zarya suna bin kuncinta ahankali wanda tarasa dalilin zubarsu,ayanzu de batasan ainahin damuwarta ba,batasan meke sata zubar hawayen ba,wannan wani irin lamari ne?yaushe zuciyarta zata samu Hutu?yaushe zatayi goodbye da bakinciki?numfashi taja kana tarufe idanuwanta,saurin budesu tayi sabida Elmoudan data gani,kara rufe idanuwanta tayi ahankali anan ma sake ganinshi tayi,shin meke shirin faruwa da ita ne?kode tasoma zarewa ne?duk cikin ranta take wa'ennan tunanin daga bisani ta bar idanuwan nata abude tana tsananin mamaki wannan alamari.Ahaka bacci ya sureta tareda mafarkan Elmoudan barkatai data rinqayi.Dakinshi ya nufa gwiwa asace domin shima ya dauki fushin da ita,ya dade yana tunani kafin daga bisani ya kwantar,Befi awa 2 ba yafarka yana goge idanuwanshi hankali tashe,ajiyar zuciya ya sauke ganin ashe mafarki ne,ya dade yana tunanin meyasa yarinyar ke zuwan masa amafarki kafin daga bisani ya share thoughts din daga ranshi.Washegari,7:25 Elmoudan yagama shiryawa cikin dakakkiyar shaddarshi Milk in color wacce tasha aiki me kyau,brown din hula.da takalmi ya saka wanda sukayi matukar amsarshi,be bi takanta ba yawuce office abinshi,Tayi matukar mamakin rashin zuwa bata haqurin dabe yiba,girgiza kai tayi ahankali sannan tayi dialling numbern mahaifiyarta domin shaida mata dukkanin abubuwan dasuke faruwa.
**************************
Elmoudan nafita daga gida yaga su Jasmine atsaye cirko cirko suna neman abin hawa,hakan yyi matukar bashi mamaki dubaga kudin mahaifinsu amma amotar haya suke zuwa school harda yar secondary school for crying out loud,garama Su Jasmine dake university sunada isashhsen hankalin dazasu kula da kansu,sauke glass yyi suka gaisa sama sama saboda basa son abinda ze shiga tsakaninshi dasu wanda yagane hakan tun ba yau ba shiyasa shima kamewa daga yimusu magana. "Jidderh shigo mutafi tunda kusan hanyar mu daya dake"daram taji gabanta ya fadi,seda suka mata kallon alamar tashiga sannan tashiga bayan motar tana dar dar,baice mata komai ba ganin she isn't comfortable,tun da tashiga motar ta sunkuyar da kanta,dagowar dazatayi tagansu a gate din makarantarsu me suna Crescent international school,jiki babu kwari tafito daga motar sannan tace masa"thank you "bata tsaya jiran amsarshi ba tashige school,da kallo yabita batareda yace komai ba ya juya yawuce office dinsu.

LABARIN JIDDERH Where stories live. Discover now