page 26

850 47 0
                                    

.. "Is he insane? Bashida hankali nr zeyi rejecting dinki as his first cousin wacce kuka taso tare? Bashida hankali ne ze watsa ma hajiya kasa a idanu? Lallai  Idan yaya elmoudan ya aikata hakan agareki babu ni babu shi, domin alqawari bece haka ba".. "Baby kenan, banida bakin godiya agareki sede fatan dacewa duniya da lahira, Allah yabarki da Muhd dinki yasa gidanshi wurin zaman kine, yanzu nasamu wani courage na musamman domin aduk sanda zamuyi magana sekin kawo any positive way out, Ashnoor bansan yadda zan shaida miki irin yadda ruhina ke shiga cikin tsananin farinciki ba aduk sanda kika karfafa min gwiwa nacewar yaya miji ne agareni duk da Zuciyata na musanta hakan"... Se anan Ashnoor tayi Murmushi tace"kada kidamu baby, you're more like a sister to me, inasonki fiyeda yadda nakeson kaina, kuma ba komai ya jawo hakan ba se shakuwa da tarbiyyar uwar kwarai wato hajiya, Allah ya tabbatar da Alheri cikin Rayuwar mu baki daya ".Karfe uku da minti ashirin Jidderh tashiga gida a matukar gajiye, afalo tayada zango domin ko ba'a fada mata ba tasan Mami ta tafi shop dinta sannan su jasmine na school, zare safar kafarta tayi sannan tacire dan karamin hijab dinta kafin daga bisani ta dauki ruwan sanyi tasoma korawa sabida yadda zuciyarta da ranta kema ta zafi
Ahankali ta lumshe idanu bayan tasha ruwan, sanyin ruwan Ya ratsa zuciyarta, ruhinta yayi sanyi sannan tanemi zafin da zuciyarta ke mata ta rasa, mikewa tayi jiki amace tayi wanka sannan tashirya cikin wata doguwar riga ta lace pink and ash, ash din hijabi tasaka sannan tawuce zuwa gidan su Ameerah, afalo ta tarar da mamansu Ameerahn, bayan sun gaisane ta shaidamata cewar yanxu Ameerah tafita amma ba jimawa zatayi ba, jin hakan yasa ta zauna suka chigaba da hira da maman Ameeran kafin ta dawo. Karfe biyar da arba'in dede Ameerah tafito raka Jidderh gida, ahanya ma hira suka tsaya yi yayinda Ameerah tace "ke namanta in fada miki kinyi new catch".. Waro ido Jidderh tai sannan tace"chab! Waye shi? ".. "Friend din yaya ne? ".. "Ayyerh sede ni karatu zanyi".. "Dalla can ai shima ba karatun ze hanaki ba, kuna soyayyarku kina karatunki".. "No bazan iya hada gudu da susar duwaiwai ba, kibashi haquri kawai "jin jidderh is sounding more serious yasa Ameerah cewa"toh shikenan, zan shaida masa inshaallah "... Horn sukaji ana musu shiyasa sukayi saurin juyawa domin duba me yi, ganin Mercedes Benz din Elmoudan yasa jidderh matsawa tareda sauke kai kasa domin yadda tunanin abinda yamata dazu Ya dawo mata, wani irin haushinshi takeji kamar ta rufeshi da duka, be tsaya bi takanta ba Ya wuce su abinshi, Ameerah ce takalli Jidderh da da yanayinta Ya canza tace "Jidderh is there something wrong? ".. "Absolutely no, mekika gani? ".. "Gani nayi kin canza farat daya".. "Kai Ameerah fadi gaskiya de bawani canzawa danayi".. "Wllhi jikina yabani Akwai wani abu tsakaninki da mutumin nan domin wani kallo danaga yamiki sannan kema alokaci guda kika fita hayyacinki.,, ".. "Miye haka Ameerah? Gaskiya banaso ✋, kada in karajin kinyi wani zance makamancin hakan domin hasashenki ba gaskiya bane"... "Allah Ya huci zuciyarki idan ranki Ya baci".. "Bazancen haka bane Ameerah, kawai de kin bata min rai ne".. "Yi haquri"tace
Sannan suka chigaba da tafiya har Jidderh ta karasa gida, Elmoudan kuwa yana shiga gida Ya tarar da inteesar na waya da Haj halima, kallonta kawai yyi domin yadda yaga taba wayar muhimmanci despite shigowarshi cikin gidan, bedroom yafada yay freshening up, sannan yashirya cikin wata brown din jallabiya, zama yyi tareda kawar da duk wani tunani daga cikin ranshi domin yyi alqawarin rage Kulawarsa da tausayinsa ga Jidderh ko hakan ka iya sa tadena zaton sonta yakeyi kwata kwata, mikewa yayi ya isa falon inteesar yazauna akujerar datake kallon ta inteesar yace"sannu da aiki inteesar "yyi mocking dinta, "yawwa my forever ya office?. "Fine"kawai yace mata sannan yasoma fadin "inteesar gaskiya banason friendship dinku da Ziyada domin bata kwanta min ba dubaga yadda behaviors dinta suke. ". Sauke kafafuwanta tai daga kan kujerar tareda tsura masa idanu sannan tace"ban ganeba Elmoudan, kasan me kake fada kuwa? Kasan wacece Ziyada awurina kuwa? Pls stop this joking ".. "Kallonta kawai ya tsaya yi cikeda mamaki sannan yace"ehh  ba se na maimaita miki ba, Banason alaqar ku da Ziyada and that is my final decision "... "You've no right dazaka hanani friendship to whoever I wished to'".. " ni ne kuwa keda right din hanaki duk abinda nai niyya matukar be saba ma shari'a ba, amma friendship dinki da Ziyada ki daukeshi as matacce".. "Elmoudan kasan kuwa me kake fada? Banajin kana cikin hayyacinka, oya stand up muje kaci abinci Naga alamar da yunwa kadawo shiyasa kake min wannan maganar ".. Irin kallon dayake mata ne shiyasa tasha jinin jikinta
Takasa karasawa inda yake zaune, "yanzu kina son nuna min ban isa dake ba kenan ko? ".. "A'a niba haka nake nufi ba, kawai de kazo da zance me tsauri ne'". "Inteesar bafa neman shawararki nakeyiba umarni nake baki? ".. "Ohhh my God! Wai me Ziyada tamaka ne? Meyasa kake kokarin rabani da aminiyata ta jini? ".. "Sabida kawancenki da ita be kamata sannan ni I am  not in support ".. "Elmoudan pls mubar zancen nan".. "Inteesar as you can see I am so serious about this, kidena saka wasa acikin maganar nan".. Kallonshi tayi akaro na uku sannan tace"wai ni mekakeso dani ne a rayuwar nan? "Tana maganar ne hawaye nafitowa daga idanuwanta, "bazaki gane ba inteesar, it's for our own good, I promise zan fada miki komai but not now". Kallonshi tai adage sannan tace"okay shikenan"maganar data yi bata kai zuci ba domin ko Elmoudan ya fahimci hakan daga yadda tai maganar, shiru kawai yayi mata badon ya haqura ba  domin yyi alqawarin raba ta da Ziyada, da wannan tunanin ya kwanta.

LABARIN JIDDERH Where stories live. Discover now