Part title

746 13 0
                                    

🌹Namijin Bahaushiya🌹

                       
  By NucyAdam
 

Wannan littafi mai suna namijin bahaushiya kagaggen labarine wanda ya tabo matsalolin dasuke faruwa damu hausawa Both mata da maza. Inafatan xaku ilimantu kuma kunishadantu



Episode 1....
   
Hajiya ni inaganin kawai zan sallami yarinyar nan ne tatafi gidansu, nagaji da matsalolin ta hajiya nabata lokaci koxata gyarama shuru, ga rashin iya girki ga son jiki sannan gakuma uwa uba kaxanta walh hajia abinci ko zallar namane idan safiyya ce zata dafa to baxaka iyaciba.  ga dan banxan kishin tsiya jiya haka ta daukemun wayata ta boye daga tafiya masallaci sallar asbah naxo nayi nayi da ita tafitomun da wayata ta ki wai ita bata ganta ba can you image hajia waxai dauki waya daga ni sai ita a daki. Juyin duniya taki fito da wayar nan haka nahakura nafita naje nayi welcome back na layina nasaka a wata wayar saida nadawo gida da daddare take mikomun wayar wai nayi hakuri itace ta dauka..  hajiya datayi zugudum tana sauraron bayanin da dan nata yake korowa gameda matarsa ta aure tanisa tace gaskiya safiyya tabata wayonta meye amfanin kazanta arayuwar dan adam fisabillillahi toni ina ganin kawai ita waccan din dakace kun fahimci juna mai zai hana atura gidansu ayi magana idan yaso sai asaka auren kurkusa duk shakiyancinta idan taga anyi mata kishiya ai xata gyara. Mukhtar yace hajia aini baxan iya da mata biyu ba yanda safiyya take da rigimar nan ai gara na sallameta kawai hajia beside ma ni gaskiya tagama ficemun akai walh. Hajiya tace to shikenan Allah ya zaba abunda yafi zama alkairi, amma dai kabi komai a hankali dan Allah. Yace to shknn hajiya insha Allah.. ni bara na  wuce .sukayi sallama da hajiyansa yafito. Wata mota naga yanufa wadda ke pake a kofar gidan nasu kirar Toyota 4runner 2WD yashiga ya bata wuta ya cillata kan titi .............
    
                       .......................

  Mukhtar muhammad bawa, kyakkyawan matashine dan kimanin shekaru talatin da biyar (35) babban maaikacin gwamnatine yana da rufin asiri sosai da sosai Dan baya cikin jerin talakawa haka zalika baya Cikin jerin masu kudi nacan sama sosai amma kwarai yanada abun hannunshi daidai gwargwado, safiyya matarshi ce dasukayi aure shekaru hudu da suka wuce asali bashi yaga safiyya yace yanasoba abokinsane yayan safiyyar shine kuma ya hadasu harsukayi aure sunada yaro daya mukarram. Kamar yanda mukhtar yafadama hajiyarsa kwarai safiyya tanada matsalar rashin tsafta dakuma rashin iya girki ga dan banxan kishi dayake damunta haka xalika tsaftar jikintama sam bata damu da itaba ballantana tayaron su mukarram wannan abu yana matukar cima mukhatr tuwo a kwarya, dan shi namijine mai son cin dadi komai yakawo gida safiyya batasan yanda xata sarrafashi yayi dadiba, irin matann nan ne da basu iya abu ba kuma baxasu yadda basu iya dinba.. wata uku kenan dasuka wuce mukhtar ya hadu da zahra, zahra kyakkyawar budurwace wankan tarwada sosai mukhtar yafada kaunarta haka itama tana kaunarshi sun hadune a hanyarta ta xuwa makaranta inda take karatun diploma a kadpoly bangaren Business administration... wanna kenan.....
       
       Kamar yanda nafada miki zainab yanada mata da kuma da guda daya but abunda nafahimta a yan watanninan damukayi dashi kamar baya jin dadin zama da matar tashi dan gaskiya alamu sun nunamun haka, duk da bai fito kai tsaye ya fadamun ba amma nafahimci wasu daga cikin maganganun sa dayake fada suna da alaka da hakan.. zainab tace to gaskiya nidai shawarar daxan baki zahra karki bashi kofar daxai dunga kawo miki maganar matarshi dan mazan dasuke debo xan tukan matansu nagida suna fadawa nawaje gaskiya ba abun saurara bane dan kema idan kinshiga ciki wata rana haka zaiyi miki. Zahra tace hakane ammafa bai taba fitowa gaskiya yayimun maganarta kiri kiri ba kawaii dai nice nake hasashen haka duba da waSu daga cikin kaalamansa. Hakadai kwayen biyu suka cigaba da tattaunawa kafun daga bisani kuma su tashi su shiga class dan suna da lecture 4 to 6 wanda kuma itace lecture dinsu ta karshe a ranar....
  
    To readers yaya kukaji salon labarin nawa ? Kudai kuci gaba da bibiyata dan jin yadda xata kaya acikin labarin nawa mai dauke da darussa kala kala. Taku a kullum NucyAdam
        Love u all 🥰
Chat me 09139097669

Namijin Bahaushiya Where stories live. Discover now