YASMEEN.

JannatMN tarafından

1.2K 63 13

Labari ne da ya k'unshi abubuwan ban mamaki kama daga kan:-Hak'uri, juriyar, tausayi, soyayya, yaudara, cin... Daha Fazla

Page 1 ✍🏻
Page 2✍️
Page 3✍️
Page 4&5✍🏻
Page 8&9✍🏻
Page 10&11✍🏻
Page 12&13✍🏻
Page 14&15✍🏻
Page 16&17✍🏻
Page 18&19✍🏻
Page 20&21✍🏻
Page 22&23✍🏻
Page 24&25✍🏻
Page 26&27✍🏻
Page 27&28✍🏻
Page 29-30✍🏼
Page 31-32✍🏼

Page 6&7✍🏻

77 3 1
JannatMN tarafından

YASMEEN.



*_Story & writing_*
*_by_*
*_Jannat mn(Real takowah)_*

*Wattpad_@Realtakowa*

*_Dedicated to my sister_*

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

_*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM*_

_*14 January, 2020😍*_

_*Hudubar farko a duniya*_

_Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam yace a hudubar sa ta farko a birnin Madina; *"Ku yada sallama a tsakanin ku, Ku ciyar da abinci, Kuyi zumunci sannan Ku tashi cikin dare kuyi sallah lokacin mutane suna bacci. Idan kukayi haka hak'ik'a zaku shiga Aljannah."* Ya Allah ka bamu ikon aikata wad'annan ibadun amin. Ya ku 'yan uwa ku tuna cewa duniya nan ba itace asalin mazauninmu ba. Asalin mazauninmu itace aljanna inda babanmu Annabi Adam ya fara zama. Saidai mun sauko duniya ne na d'an wani gajeren lokaci. Saboda muyi wata yar jarabawa kafin mu koma. Dan haka kayi k'ok'ari iya yinka dan ka shiga ayarin salihan bayi, Wacce zata koma ainihin matsuguninmu maikyau yalwatacce. Kada ka b'ata lokacinka a wannan k'untatacciyar duniya. Mu dai ba zamu iya canja abinda ya faru ba. Haka zalika ba zamu iya tsara abinda zai faru ba. Toh..! don me zamu sawa kanmu damuwar abinda ba zamu iya canja shi ba?_
_*DAN HAKA KAYI RAYUWARKA CIKIN BAUTAR ALLAH SAI KA ZAMA MAFI FARIN CIKIN BAYINSA. ALLAH YASA MU DACE. AMEEN YA ALLAH👏*_

_*Page 6&7✍*_

________Tashi sukayi ta kama musu hannu suka tafi d'akinsu, cire musu kaya tayi ta canza musu wasu ta rakasu toilet sukayi alwala itama tayi suka fito, Ayman ya tafi masallaci....suma suka gabatar da tasu sallar.

Da sallamarsu suka shigo cikin falon Ayman na sab'e a saman kafad'ar Abdallah, fuskarsu d'auke da fara'a daka gansu kasan suna cikin farin cikin. Da gudunta nufesu tana fad'in,

"Oyoyo Abba sannu da dawowa"

K'ara yallwata fara'asa yayi d'aukarta yayi ya cillata sama ya cab'e shima yana fad'in,

"Yauwa Aymanata"

K'arasawa sukayi cikin falon cikin farin ciki da annashuwa, zama yayi a d'aya daga cikin kurerin falon tashi tayi zata bar falon,

"Sannun da zuwa Alhaji an dawo lafiya"

"Yauwa, lafiya qlau salma"

Lemon mai sanyi ta shiga zubawa a cikin kasaitaccen Cup mai d'auke da launika biyu fari da ja. Fuskarta d'auke da murmushi ta mika masa Cup d'in tana fad'in,

"Sannu da zuwa Alhaji an dawo lafiya ya hanya"

Karb'a yayi ya k'ara yalwata fara'arsa, wanda ta fito da tsantsar kamar da suke da Abdallah da Ayman, yana mai jindadin abinda tayi mass.

"Yauwa Hajiya, hanya saidai muce Alhamdulillah lafiya qlau Hajiya"

K'asaitaccen murmushi Abdallah yayi dan yana matuk'ar son yaga Abbana da Ummansa suna irin wannan barkwancin yace mata

"Hajiya"

ita kuma tace masa

"Alhaji."

A duk lokacin da suke irin wannan wasan indan ya kalli abbansa sai ya ringa jin dadi, domin bai tab'a ganinshi cikin farin ciki ba tun bayar mutuwar Amensa sai zuwan Ummansa cikin rayuwar su.

Gaskiya Ummansa fitilace agaresu da zuwanta ta haskaka musu rayuwarsu yanzu, gashi kawata² Abbansa ya daina shiga damuwa da rashin wata walwala.

Yanzu gaba d'aya ya manta da rayuwar baya ya tunkari ta gabana,

"Alhamdulillah"

ya fad'a cikin jindadi yace zuciyata tare da jero musu addu'o'i na kariya dadai sauransu cikin jindadi yace

"Abba fatan an samu nasara akan abinda aka tafi nema"

"Eh..! Abdallah mun samu nasara, amma fa munsha wuya wajen gane gidan mutumin nan, da kyar muma samo gidan nasa..."

Nan ya kwashe labarin duk aubuwan da suka faru ya sanar dasu.

"Gaskiya Abba kunsha wahala sannun ku, Allah yasa andace"

"Ameen" suka had'a baki gabaki d'aya suka fad'a a tare murmushi sukayi, tashi yayi yace

"Bari naje na rage gajiya kafin lokacin sallar isha yayi"

"Toh..! Abba a fito lafiya"

"Ameen" ya Abdallah

Barin wajen yayi nufi d'aki, tashi tayi ta mara masa baya, su kuma suka ci gaba da hirarsu.

"Yaya yaushe zaka kaimu gidan Hajiya ne"

"Sai weekend insha Allah zan kaiku Aymana"

"Allah ya kaimu Yaya"

Hirarsu suka cigaba dayi har lokacin sallar isha yayi, tashi sukayi sukaje suka gabatar da sallar suka dawo.

Kowa ya hallara a saman dining table, abincin su suke ci cikin farin ciki da kwanciyar hankali twice ne suka fara gama su kace sun koshi,

"Toh..! Maza aje ayi brush akwanta gobe da School"

"Toh..! Yaya"

"Sai da safe Umma, Abba, Yaya"

"Toh..! Allah ya tashemu lafiya"

"Ameen"

suka amsa suka bar wajen, basu jima da tafiya ba shima ya tashi yace ya koshi sallah yayi da iyayen nasa sannan shima ya bar wake, Guri ya rage sai su,

"Agaskiya dole na k'ara godewa Allah da ya k'ara bani mata ta gari a karo na biyu, gaskiya Khadija in zamo tamkar fitila a cikin rayuwata da ta d'ana, zuwanki garemu ya kore mama duk wani bak'in ciki da k'uncin rabuta da matata Amina, shi kuma ya manta da maraicin mahaifiyarsa dole mu godewa Allah. Alhamdulillah Allah mun gode maka Allah ya biyaki da jannatul firdausi, ya Allah ya raya mana zuri'armu ya kuma shiryar mana dasu, dama dukkan al'umar musulmai baki d'aga akan ta farki na gaskiya, Ameen ya Allah👏🏻"

"Hmm" wani irin k'asaitaccen murmushi tayi sannan tace

"Alhaji nice da godiya ba ku ba komai zan muku kaida d'anka bazan tab'a biyaku halarcin da kukayi min ba, domin kun karb'eni hannun bibiyu a lokacin da na rasa kowa nawa ni kaina bansan koni wacece ba, amma kuka karb'eni kuka mutuntani ka aureni ba tare da kasan koni wacece ba kuma daga ina na fito....."

Kukane yaci k'arfinta tayi shiru badan taso ba, jawota jikinsa yayi ya fara lallashita da bata baki,

"Kiyi hakuri ki daina kuka inji matata, gani kukanki koh jinsa ba k'aramin tashin hankali nake shiga ba, duk na bi an rasa kwanciyar hankali da nutuwata, sai naji kamar ana tab'amin takobi a cikin zuciyata, ya ke matata ina mai rok'onki kiyi hak'uri kiyi shiru inba so kike nayi kuka ba nima...."

"Hmm! Nayi shiru kada kayi kuka kaji Alhajina"

"Hhh! Kinga yace kikayi kyau da kika daina kukan nan kuwa Hajiyata, gaskiya indai kukan nan ya k'ara zuwa inda kike saina shari'a dashi. ina sanki matata Allah yabarmu tare. Ameen ya Allah👏🏻"

"Hmm Alhaji kenan baka da dama. Ameen ya Allah."

••••••••••
Zaune suke a 'kasaitaccen falon su wanda ya gaji da had'uwa da kayan k'awa, hirarsu suke cikin nishad'i da annashuwa, shiru yayi ya rufe idanunsa tamkar mai yin barci, amma ba barci yake ba yana jin duk abinda suke cewa,, farine kyakyawa ne na wuce musali,, fad'ar ma kyawunsa da had'uwarka b'ata bakine dafa kad'arsa yayi yace:
"D'an uwana lafiya kake kuwa nafa fuskanci kanan biyu ka rage walwalar kamar da??"
"D'an uwa kenan ina ji a jikina cewa kamar na rasa wani abu mai mahimmaci a rayuwata,, tun safiyar yau nake jin jikina yayi wani iri sanyi."
"Ka kwantar da hankalinka d'an uwa insha Allah babu wani abu mai da haka da zai faru,, zancen kuma sanyi da jikinka yayi ka ri'ka maimaita kalmar inalilahi wa'ina ilaihiraju'an.."
"Nagode sosai d'an uwa insha Allah zan yi kamar yadda kace.."

Cikin murmushi ya fad'i tare da dafa kafad'un 'yan uwan nasa guda biyu.....

_See me next page✍🏻_

_*Vote*_
_*Like*_
_*Comment*_
_*#Realtakowa*_️

Okumaya devam et

Bunları da Beğeneceksin

39.4K 3.5K 19
A Royal family renowned for their illustrious name and fame, A family full of pride and rage, A Family for which everyone bows their head - The Agnih...
248K 7.4K 59
I could say this is one cliché story. A college girl died and transmigrated into an otome game she once played. Unfortunately she becomes the villain...
297K 40.2K 20
လက်တွေ့ဘဝနှင့် နီးစပ်ချင်ယောင်ဆောင်ခြင်း
1.2M 40K 59
Princess Nymeria is well aware that her kingdom is in decline. It has been for hundreds of years after all. Unlike her ancestors, she's willing to re...