NAZLAH

By Salmeert

235 32 2

Labarin Wata Fitinanniyar Yarinya da bata barin bashi, ko mai ka mata sai ta rama, har sai ta ci gyara, gata... More

CHAPTER 1-2
Chapter 3-4
chapter 7-8
chapter 9-10
chapter 11-12
chapter 13-14
chapter 15-16
Chapter 17-18
Chapter 19-20

CHAPTER 5-6

22 2 0
By Salmeert

☘️☘️NAZLAH☘️☘️


     *DAGA ALƘALAMIN*

SALMAJI / ƳAR LELEN ROYAL STAR CE🧚‍♀️🧚‍♀️🧚‍♀️




*WANNAN LITTAFIN TUN DAGA FARKO HAR KARSHE SADAUKARWA NE GA YAYATAH (MARYAM YUSUF), WANNAN LITTAFIN WAKE NA RUBUTASHI, ALLAH YA RAYA MIKI ZURI'ARKI , ALLAH YA RUFA ASIRI DUNIYA DA LAHEERA*


*WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE, #300 NE KUDINSA   KI DAURE HAJIYA KI BIYA DAN SHAN KARATUNKI CIKIN KWANCIYAR HANKALI,KUMA YANZU NE ZAN KARA GANIN MASOYAN YAR LELE 🧚‍♀️🧚‍♀️, WANDA SUKE CEWA SU  MASOYANA NE, TO KU NUNA NIN KAUNA TA HANYAR SIYAN WANNAN LITTAFIN NAWA, KAR KU MANTA #200 NE KAWAI*

1499884120
UMMASALMA SANI
ACCESS BANK



*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
       {R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
  *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* ( DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN KAI, YAH RAB YARDA NA FARA LITTAFIN NAN LAFIYA ALLAH KASA NA GAMA LAFIYA, ALBARKACIN ANNABI DA AL-QUR'ANI)



5-6.



""""""""""""""""""Ta fada tana gyara Kwanciyarta", Shiru Jamseey tayi bata ce da ita komai ba, a taƙaice dai ranar a gidansu Sadiyya ta yini, gashi ko abin ci basu bata ba itama kuma bata damu ba, sai dai aiki wannan Yaron siyan Maƙulashe ta aiki wannam haka ta ri gayi har rana ta faɗi, kallonta Jamseey tayi tare da cewa "Aminiya tashi nu tafi gidanki", kamar raƙumi da akala haka ta bita zarai-zarai har gidan nata, palon tsaf-tsaf mai aiki ta gyara ko ina tar, bedroom dinta sula wuce, anan naga zalar ƙazanta komai a harmutse babu gyara, zama sukayi kan bed din, jona wayarta tayi a charge tare da mikewa, gurin da take ajiye tsintsiya ta nufa, zata dauka ta tattare ɗakin..............



               Kallonta Jamseey tayi tare da cewa "mai zakiyi da tsintsiya haka ?" , kai tsaye ta bata amsa da " tattare ɗakin zanyi naga ya yi kura da yawa", cikin zuciyarta tace anzo gurin, kallonta tayi tare da cewa "shara kuma yanzu ɗakin nan mai ya yi haka ?", yatsina fuska tayi tare da cewa "sai naga kamar ya yi datti"  zare ido Jamseey tayi tare da cewa, "anya kuwa baki makance ba ina dattin ni banga wani datti ba sai dai idan idanunki ne suke nuna miki, to nan mai ɓa zaki share, ko da yake share", ta fada tana kallonta................



                 "Ah'ah barshi kawai dama ɗakin ne naga kamar Ya yi kura shi yasa amma barshi kawai dan ni kaina nauyin jikina nakeji ", ta fada tana fadawa kan bed din, wani kill smile Jamseey ta saki tare da cewa  "da kuwa kon hutawa kanki," ta fada tana latsa wayarta............



                      chan kuma ta ɗago tare da cewa, "Aminiya Yunwa nakeji", kallonta tayi tare da cewa, "to kije kitchen ki girka abinda kikeso mana",,ta fada tana mayar da hankalinta kan wayar hannunta da ta gama bawa amanar kanta...............



                   Mikewa tayi ta nufi hanyar barin bedroom din, tana fita kitchen ta nufa, tana zuwa ta bude store kayayyakin abin ci ta fiba, sai da ta ɗibi komai kafin ta bude kofar baya ta cikin kitchen din ta zura kayan waje, Indomie  shidda ta ɓare ta zuba a cikin tukunyar da take tausa, cikin minutes kaɗan ta gama ta juyo cikin tray tsayawa nayi ina kallonta ganin ta fito dashi ta ajiye a tsakiyar palo ta wani dai-daita zama..................




                 fitowa Sadiyya tayi, zama tayo lan kujera  duk da taga uwar Indomien da kwan da Jamseey ta dafa amma bata ko daga kai ba, ci ta farayi, sai da tayi naƙ kafin ta juye sauran a leda ta ce, "ni fa zan tafi muyi chart dan naga haɗari na haduwa, "okay to shi kenan Ƙawa bari na rakaki ko bakin get ne", girgiza kanta tayi tare da cewa , "ah 'ah ba sai kin rakani ba kiyi zamanki", jin hakan yasa ta koma ta zauna, ficewa Jamseeyn tayi da sauri,,sai da ta zagaya ta dauki abin da ta fitar kafin ta wuce gida abinta................




                   tana fita da wasu yan mintuna, sai ga jiniyar motarsu Hamid mikewa Sadiyya tayi daga in da take, yana bude kofar ta nufi in   da yake, mamaki ne ya cikashi na ganinta da kaya da ya fita ya barta dasu,sanan palon kacha-kacha da alama bata gyara komai, fadawa jikinshi tayi tare da cewa "Welcome back My Solder", wani ƙarin rana ne ya daki hancinshi, numfashinshi ne ya tsaya chak na tsawon lokaci kafin ya ci gaba da aiki, da sauri ya matsa da ita daga jikinshi ya wuce sama...............



                 da sauri ta dauki wayarta, ganin Jamseey ta turo mata sako yasa ta bude voice note din sai da ta gama saurara ta mayar mata da amsa kafin tace, "ban fada miki ba My Solder ya dawo yanzu, mai kike ganin ya kamata nayi", dariyar kyeta Jamseey ta saki, kafin ta fara cewa, "to yanzu abun da zakiyi, kice kiyi wanka ki shirya, sai kije bedroom dinshi" mikewa tayi ta shiga bedroom dinta, wankan tayi ta shirya tare da cewa, "to na gama gani zanje bedroom din nashi", ta fada tama tura kofar shiga, ko da ta shiga baya ciki,hakan yasa ta zauna kan bed tare da cewa "gani nazo ma  baya cikin bedroom din da alama wanka yake", murmushi ta kara saki tare da cewa, "to in ya fito ki tarɓeshi da salo, ki kwantar dashi ki mishi tausa, sannan ki ringa shafashi sai  ya hau network  ki gudu dan banason ki bashi sai kin wainashi, yarda zai fi rikeki da daraja" dariya Sadiyya tayi tare da cewa "gaskiya ne Ƙawata nagode da shawararki",,tana gama voice note din Hamid na fitowa daga wankan da ya shiga................



                   da sauri ta mike ta taroshi, mamaki ne ya kamashi sai dai da yake shiɗin Namijim duniya ne bai yarda ta gane mamakinshi ba ko kaɗan,tsane mishi ruwan jikinshi ta shiga yi, bayan ta gama ta shafa mishi lotion  vest da boxer ta bashi ya sanya, kallonshi tayi tare da cewa "nasan ka gaji kwanta na maka tausa", ta fada tana kashe mishi ido, ba musu ya kwanta tare da ringinginawa, hannunta ta daura kan tattausar fatar jikinshi ta fara tausa mish a hankali, cikin minutes kadan yanayi ya chanja gaba daya ya fita a hayyacinshi, tana ganin haka ta,zame jikimta tare da ficewa da gudu, ta datse bedroom din ................



                     rasa yarda zaiyi ya yi, hakan yasa ya shiga bathroom ya sakarwa kanshi ruwan sanyi mai sanyi, hakan kuma ya yi dai-dai da saukar ruwan sama mai karfin gaske, wanda gaba daya ya kara dagula mishi lissafinshi................



          **********


            Asubar fari Jaririya ta fara tsanyara kuka, mai matuƙar sauti, da firgitarwa, sai kace wadda ake yankar naman jikinta haka take kukan da ihu , kukan da takeyi kuma shine ya yi sanadiyar tashin Lawan daga bacci,cikin ruwan masifa ya fara kiran "Maryama! Maryama!! Maryama Wallahi ki tashi ki dauki Yarinyar nan ku fita a ɗakin nan in ba haka ba,zanyi ball daku ke da ita,haba wannan wace iriyar masifa ce, kinzo kawai kin haifar wa mutane Yarinya mai masifar kuka, ki tashi ki dauketa nace ko", ya fada yana shurin hannunta, a firgice itama ta farka tare da daukar Babyn ta sanyata a jikinta tana rirrigawa..............



                    tsawa ya daka mata tare da cewa"tashi ki fice ki bat ɗakinan nan da yarinyar nan , kafin na ɓaɓɓalaku ke da ita", a hankali ta mike ta fita da Babyn a hannunta, gefe chan ta samu ta zauna, tare da fara feeding din Yarinyar, dan-danan kakejin Yarinya tayi shiru, sai da ta ƙoshi kafin ta kona cikin ɗakin jikinta na karkarwa kasantuwar  har lokacin lemar da aka kwana da ita na ruwa bai tsane ba, kwantar da Yarinya tayu tare da kwanciya itama, bacci ne ya kara daukarta...................




                 tun 7 Iya tazo ta daura musu ruwan wanka, wannan karon Maryama da kanta tayi wankan Babyn kawai Iya tawa wanka, Maryama na fitowa ta Umarci Haleeem maza yaje ya yi, baya ta gama shiryawa ta fito tare da fara tsaftace tsakar gidan da shara ta fara kafin ta haɗa yan kwanikan wanke-wankensu ta haɗu kunfa wankewa ta shiga yi, sai da ta gama fes ta kikkife, kafin ta fara kiciniyar haɗa wuta, Iya ce ta shigo, zare ido tayi tare da cewa ",duk wa ya yi wannan aikin haka ?", kafin Maryama tayi magana Haleem yace "Umma na ce Iya", zare idanu ta karayi tare da cewa.........



                "Maryama aiki har haka, tashi kije ki huta bari na haɗa wutar", ta fada tana ƙarasowa, girgiza kanta tayi tare da cewa "ah'ah Iya bari nayi ai tama kusa haɗuwa",ta fada tana mata murmushi, shiru Iya tayi har Maryama ta haɗa wuta, kallonta tayi tare da cewa "to akwai abun Sarrafawa ne ko kuwa", "akwai Iya",  da sauri Haleeem yace  "Ummu babu fa,  kece kika ce karya babu kyau, wanda ya yi ana ƙonashi a wuta"  ya fada yana rike baki, shiru Maryama tayi, kallonta Iya tayi tare da cewa "mai yasa ba zaki faɗamin ba", kamar ba,zatayi magana ba sai kuma tace, "nayi tunanin kafin na gama hura wutar zai kawo abinda za'a sarrafa ne", "kema kinsan indai Lawan ne bazai kawo ba, bada ban kar na mishi baki ya ƙara lalacewa ba , na sai na mishi," da sauri tace "kiyi hakuri Iya dan Allah kar ki misi baki, danbin kika mishi ba'asan yarda abun zai kara komawa ba, kiyi tayi misho addu'ah insha Allahu zai daina", ta fada,tana mayar da kwallar idanunta.................



             ficewa Iya tayi tana jinjina wa halayya irin ta Maryama , dan ita ko bata da abu bazata taɓa fada tace babu ba, kuna duj irin ƙuntatawar da Lawan yake mata bata fadawa kowa sai dai ta shanye, amma da yake shi din ba dan goyo da tari bane , ko gaban mutane sai ya duketa ko zagi, Iya kanta da take Mahaifiyar Lawan tana Alah tur da halayarshi, amma ita ba zata tama budar baki tace kaza ba, ko ya mata sai dai tayi Murmushi, kuma ko zaka kasheta ba zaata fadi sirrinsu ba ita da Mijinta...............



              hakan kuwa yasa take mugun shan wuya gurin Lawan din, garin kunu ta kawo musu, ƙadan ta ɗiba ta dama, zubawa Haleeem tayi, yana gama sha ya fice makaranta, zubawa Iya tayi tare da dibar dan kaɗan ta sha, tana gama sha Lawan ya shigo, ko sallama babu ya wuce ɗaki................



                  kunun ta dauka sauran wanda ya rage, ta shiga dashi ciki, ɗurkusawa tayi har ƙasa tare da cewa, "Mai gida ga kunu", mikewa ya yi, tare da daukar kofin, bude kunun ya yi, kallonta ya yi tare da cewa "Dan wannan kunun", dukar da kanta tayo ƙasa dan in yana guri ko ɗaga kanta bata iya yi...............


            a bakinshi ya  kafa kofin, da sauri ya cire bakinshi tare da furzo na bakinshi akan fuskarta, da sauri ta dan daga kanta, masifa ya fara mata akan ta bashi kunu ba sugar, "dan iskanci sai ki bani kunu ba sugar, dan kawai salon rainin wayau, yar iskar banza to wallahi zaki gane kurenki",  ya fada yana zare belt din jikinshi...............




                 ganin haka yasa da sauri ta kwznce Yarinyar  da take bayanta ta matsar da ita chan gefe, tsula mata belt din Lawan ya shiga yi, duk da da zafi amma ko uhummm bata de ba saboda biyyaya, kuka jaririya ta fashe dashi, tana ɗaga kafafunta........



              kukan ta shiga yi sosai, tsagaitawz ya yi da dukanta tare da cewa "Dauke min wannan shegiyar Ɗiyar kafin na bugeta a gurin nan"da sauri ta dauki Yarinyar ta fice da ita, jikinta ya yi ruɗu-ruɗu , da shaidar  belt,  rirriga Yarinyar ta shigayi..............



               Haka suka ci gaba da kasancewa har satin da ta haihu ya zagoyo, sai dai babu huɗuba, dan Lawan ki kallon Yarinyar bai taɓa yi ba balle har ya dauketa ya sanya mata wani Suna, ranar Iya na tambayar Haleeem ya fada mata, da sauri ta tafi da Yayah Lawan wanda suke Uba daya, karɓar Jaririyar tayi  tare da cewa "yi mata Huɗuba", karbar Yar ya yi, Addu'ah ya mata tare da cewa  "Wani suna za'a sanya mata?", da sauri Haleem da yake gefe yace " *Nazlah* Kawu ?",  kallon Iya ya yi, jinjina mishi kai tayi, hakan yasa ya raɗa mata sunan............


                  
               har maraice Lawan bai kawo Ragon Haƙiƙa ba, hakan yasa Iya daukar dan Bunsurunta ta bada aka yankawa *Nazlah* , ba wani taro dan Lawan baya barinta fita ko nan da chan hakan yasa, babu wanda ya zo mata , sai Yan uwa..................


                   soye naman akayi aka ɗibar wa duk wanda ya kamata, sauran aka bawa Maryama, janta Iya tayi tare da cewa "Maryama kar ki sake ki bawa Lawan naman nan, in yazo ma kice ba'a yanka komai ba, tunda shi bashi da mutunci", jinjina kanta tayi..........


                 bayan fitar Iya sai gashi yazo, kallon Maryamar ya yu tare da cewa "Ke ina naman da aka soya" , daukoshi tayi gaba daya tare da ajiyewa a gabanshi kanta a ƙasa tsinta ya fara yi sai da ya gama kafin, kalleta cikin muryarshi yace "Ga sauran nan ki ajiyemin ko hanji daya kika ci ban yafe ba",,ya fada yana ficewa...............



                 Naman da ya,zama haramiyarsu kenan ita da Haleem da ko yanka daya bai ci ba sai dai tayi ta bashi haƙuri, haka har kwanaki suka dan fara haurawa komai Iya take musu.................



                     Sai dai kullum Lawan sai ya ta zagin Maryama har makwabta baji saboda kukan *Nazlah* dan gaba daya bata bacci  da daddare sai kuka, hakan yasa gaba daya rayuwar Lawan yaji babu abun da ya  tsana a duniya sama da *NAZLAH*...........



                 hakan yasa Yarinya ta tashi cikin tsana da tsangwamar Mahaifi, bata da ƙatabus a fabanshi, tun tana Yar wata biyar, yake dukanta in tana kuka,  a haka har Nazlah ta fara girma , tana da wata 10  gona cif ta fara tafiya, a lokacin kuma sai Allah ya daura mata kwaɗayi na masifa............


               ba damar taga bakin mutum na motsi ta ringa mika mishi hannu kenan nata bakin shima yana motsi, tun suna dauka zata daina har Yarinya ta fara magana bata buɗi baki da konai ba sai "Yanman", hakan yasa Ummu bata fita da ita sai dai ta barta gurin Iya in zata fito.........



             wata rana, Lawan ya shigo da ledarshi cikin gida, tun da ya shigo idanun Nazlah nakan ledar nan har ya nemi guri ya zauna, mikewa tayi ta nufi gurin da yake dan nesa kaɗan ta zauna, indomie ya bude cikin ledar sai  turiribtake da zafinta, ƙamshin Indomien ce ta daki hancin Nazlah wani mugun miyau ta haɗiye Kuttt tana kallon ledar, Lawan na lura da ita, daga ledar ya yi, sama da kallo ta kara bin ledae tana leqe tare da haɗiyar yawu...............


                 mikewa tayi ya nufeshi, tsna zuwa gurinshi ta mika mishi hannu tare da cewa "Yanman",,ta fada tana kara mika mishi hannun,kallom tsana ya watsa mata tare da daukar garwashin  wutar da take kusa dashi tare da daura mata a hannunwanta, ya rumtse mata hannunwan sosai yarda ba zata iya zubarwa ba..............



                 A zabar da ta ratsata ce tasa , ta saki kuka da azabar karfi , har cikin zuciyar Maryama sai dai tasan dama dole hakan zata faru tun da taga Lawan ya shigo da leda sai dai batayi zaton zai iya ƙonata ba.............



                   sai da fatar hannunta fa fara salewa sosai kafin ya saki hannin izuwz lokacin kuwa kukanta ma baya fitowa da kyau...........





             *********


                  dakyar da siɗin goshi Hamid ya samu natsuwa, wanka ya yi tare da fitowa daga bathroom din, kwanciya ya yi ko abinci bai nema ba, haka ya kwanta coke da tunanuka sosai cikin ranshi..........



                washe gari ma unguwa ya sake zuwa , kamar jiya Yau ma a gidansu Jamseey ta yini sosai, sai Yamma ta dawo, ko da ya dawon yau ba laifi kayan palon tsaf , nashi kuwa dama babu wani datti kuma kullum sai an gyara mishi...............



          Shawararta ta nema akan zai tafi da ita partcourt gurin aikinshi kasantuwarshi na Sojan ruwa (NAVY) sai da ta fadawa Jamseey kin amincewa tayi da tafiyar tata, hakan ya tace mishi ita ba zataje ba, jin hakan yasa ya ci gaba da shirin tafiyarshi..........


           kwana biyu tsakani ya yi chanewarshi Part court, nima kuma sai na tsaya anan sai kuma mun kara haɗuwa a page din gaba...........



*karfa ku manta Nazlah na kuɗi ne #300 ne kuɗinsa , ki biya ki karanta cikin jin dadi da annashuwa🥰*


wannan shine account details din.

1499884120
Ummasalma Sani.
Access bank.

sai ki turamin da shaidar biyanki tanan....


07033371851


~DAGA TASKAR SALMAJI / ƳAR LELEN ROYAL STAR CE🧚‍♀️🧚‍♀️🧚‍♀️~

Continue Reading

You'll Also Like

1.2M 66.1K 59
𝐒𝐜𝐞𝐧𝐭 𝐨𝐟 𝐋𝐨𝐯𝐞〢𝐁𝐲 𝐥𝐨𝐯𝐞 𝐭𝐡𝐞 𝐬𝐞𝐫𝐢𝐞𝐬 〈𝐛𝐨𝐨𝐤 1〉 𝑶𝒑𝒑𝒐𝒔𝒊𝒕𝒆𝒔 𝒂𝒓𝒆 𝒇𝒂𝒕𝒆𝒅 𝒕𝒐 𝒂𝒕𝒕𝒓𝒂𝒄𝒕 ✰|| 𝑺𝒕𝒆𝒍𝒍𝒂 𝑴�...
841K 27K 68
"Real lifeမှာ စကေးကြမ်းလွန်းတဲ့ စနိုက်ကြော်ဆိုတာမရှိဘူး ပျော်ဝင်သွားတဲ့ယောကျာ်းဆိုတာပဲရှိတယ်" "ခေါင်းလေးပဲညိတ်ပေး Bae မင်းငြီးငွေ့ရလောက်အောင်အထိ ငါချ...
853K 71.3K 34
"Excuse me!! How dare you to talk to me like this?? Do you know who I am?" He roared at Vanika in loud voice pointing his index finger towards her. "...
138K 7.6K 40
𝐁𝐎𝐎𝐊 𝐎𝐍𝐄 𝐎𝐅 𝐓𝐇𝐄𝐈𝐑 𝐅𝐀𝐈𝐓𝐇 𝐒𝐄𝐑𝐈𝐄𝐒 Aarohi and Siddharth's tale began unexpectedly at her brother's wedding. Their connection spa...