MAHAUKACIN KISHI

15 0 0
                                    

🌺🌺🌺🌺🌺🌺
BISMILLLAHIR
RAHMANIR RAHIM

💔💔💔💔💔💔

*MAHAUKACIN KISHI*

🌺🌺🌺🌺🌺🌺

    *MALLAKIN*👉zaynerb Muhammad kabir *(MUM FU,AD)*

      *FREE BOOK*

   *(TRUE LIFE STORY*)

Wattpad , zaynerb Muhammad kabir
Facebook zaynerb Muhammad kabeer
Email address zainab m kabeer,s @gmail.com..
*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga  shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

https://chat.whatsapp.com/IaEiILApyqN6ePQRzOPT7


  *PAGE 22*

*wanene sadik*
   Abubakar Sadik sulaima shine cikakken sunanshi , haifaffen garin bauchi ne,
  Mahaifinshi  alhaji sule mai turare, babban mutum ne  a garin , kasancewarshi babban  mallami , mai fada ajii  kuma dan siyasa , sannan me tarin dukiya , Abaya yayi sana ar siyar da  turaruka shiyasa , ake mishi lakabi da mai turare,

    Alhaji sule mai turare yana da mata biyu , hajiya saude da hajiya asma ,u 
Hajiya saude itace farko, mahaifiyarsu sadik , tanada yara biyu  , sadik  shine na  farko sai kanwarshi budurwa , wato salma  , sadik allah ya fara bata , kasancewar ta dade bata haihuba daga baya sai ta kara haifan salma tundaganan haihuwarta ta tsaya .

  hajiya asma ,u  itace  ta biyu tanada yara biyar mata uku maza biyu , Inda matan  kowacce  na gidan aurenta.

  Sadik yaro me matashi me ji da kanshi , kyau kaurjin ba a magana , uwa uba iya daukan wanka da iya sanya turare , sadik irin black beauty dinan ne , in har yafito , yana takun kasaita kamar bazai taka kasa ba.
Sadik na aiki ne a wani banki na NDIC ,
   Shiyasa 'yan mata suke rubibi a kanshi , kowacce mace na burin mallakarshi a matsayin mij.
  Sun hadu ne da rukkaiyya a layi , kasancewar  gida jan iyayensu basu da nisa tsakani.
Rukkaiyya farace doguwa, ba laifi tana kyau iya gwargawado , tunda sadik ya ganta yaji yana matukar san ya mallaketa a matsayin mata , koda yaje ya tunkareta da bukatarshi, bai sha wani wahala a gun rukkaiyya ba, dan itama ta dade tana sanshi , tarasa yanda zata tukareshi da maganar ,
Shikanshi  yana yawan ganinta amma yakasa mata magana , akan bukatarshi .

  Duk da Cewar yana jin kananan maganganu mara dadi  akan tarbiyyarsu  da kuma halin mahaifiyarsu.

Amma  hakan baisa ya fasa idda aniyarshi ba, a  cewarshi ai balaillai hali yazo dayaba dan mahaifiyarsu bata da hali ba lallai Rukkaiyya ma tazama  hakan ba .

  Rukkaiyya  murna a gunta ba a magana ,kamar ta zuba ruwa a kasa tasha dan murna , cikin Sauri da rawar kai taje ta sanarwa da mahifiyarta cewa tayi saurayi me kudi dann babban mutum kuma yace da aure  yake santa .
Mahaifiyarsu Rukkaiyya cikin farin ciki da murna  tace ""ke da gaske kike waye? dan waye kuma a garinan?
  Cikede zumudi Rukkaiya ke sanar da mahaifiyatata , cewa ai dan gidan Alhaji sule mai turare, cikin farin ciki Hajiya Amina tace a lallai  zama baisamemu ba , maza maza shirya mutafi gurin  boka yayi mana aiko dan mutum irin wanna sai mun taahi tasaye kinsman mahaifinsu mai addu a ne kar yazo ya gano wani Abu yasa a fasa Auranan , maza maza kishirya muje yayi mana aiko mai zafi , dan so name kema kizuba muliki A gidan auranki kamar yanda sauran yan uwanki sukey.

   Rukkaiyya kuwa cewa tayi uhmmm kinga mama kibari kar muyo gaggawar mallakanshi yanzu kibari ayi auran tukun kar idon mutane ya dawo kanmu , koh ba haka ba ?

Hajiya Amina tace" ke wacce irin yarinyace,ance miki ana wasa da irin wanan damar ne , ke yarinyace bakisan me kike ba .

  Rukaiyyace tace" kai mama dan Allah ba sai munje ba nafiso ayi auran tukkun,  in anyi sai muje bokan yayi mana aiki yanda ya kamata.
  Dakyar Rukkaiyya ta shawo kan mahaifiyarata, amma bida sharadin cewa ana daura auran zasuje boka yayi musu aiki.
Ciki. Saudi Rukkaiyya tace ehh ehh na amince mama ,ai hakan nakeso dama, Cikin ran Rukkaiya kuwa ba komai ne yasa tace wa mahifiyartata kar ajhe gun boka ba saidan sanda take mai, kuma itama ta hango tsantsar , San da yake mata , Acewarta ya fi San ta ma akan San da take mishi   hakan yasa taji ba lallai bane  sai sun  mallakeshi ba .

   Sadik ne zaune a gaban mahaifiyarshi , yana shaida mata cewan yana Neman are , cikeda jin dadi , mahaifiyarshi tace " kai sadik a ina kasamota , gaskiya nayi matukar farin ciki da hakan , a ina take kuma 'year waye !!
Cikeda kunya , Sadik ya so kai yace uhmm mama year gidan Alhaji muhammadu mai dala ce ,
Da sauri Hajiya ta dago kai tace yar gidan Alhaji muhammadu ?'yar waye a cikin Matan ? Cikida jin kunya sadik yace uhmm ai yar, Hajiya Amina ce , dasauri Hajiya tace kai karkafara , kashiga hankalinka , na rantse da Allah bazamu taba hada zuri ,a fa 'yar da ta fito daga tsatsan Hajiya Amina ba , kai kasan waye Hajiya Amina kuwa!! Hajiya tafada rai A bace takara da cewa, kai ladan halin da mazajan 'yan uwanya suke fama da su kuwa?? Toh tun wuri inaso ka farga , kasani Hajiya Amina ba mutanen kirki bane , Takara da cewar wai ma tukunna!!ko ka manata da halin Hajiya Amina ne , kodayaike ka dade baka gari shiyasa bazakasan wasu abubuwan ba .
  Amma ni nagama magana bazaka auri 'yar gidan Hajiya Amina ba sabida haka kaje ka nemi waya , nafikowa San ganin kayi aure amma hakan bazaisa in barka ka aikata, Abun dazamuzo gaga baya muna danasani l.
 
Sadik kuwa in hankalinshi yayi dubu ya tashi, cikin tashin hankali yace"" Hajiya kidubi girman Allah kar kice bazan Auri Rukkaiya ba Hajiya wlhy ina Santa , Hajiya , ballai halin su yazo daya da mahaifiyarta ba , Hajiya ballallai yazo daya ba , Hajiya Allah fa yakan fidda matacce cikin rayaiyye , sanna yakan fidda rayaiyye cikin matacce, Kidubi wanan Ayar , Hajiya dan Allah, yayi shuru kamar me shirin yin kuka .

Hajiya takalli dan nata Wanda duk yagama bata tausayi , tafara magana cikin tattausan lafazi tace " Sadik tafada da muryar mai sanyi , Sadik yadaga ido ya kalleta , tafara magana " Sadik kasan cewa bazan taba yin abun da zai cutar da kaiba ko ?? Sadik ya daga kai alamar eh , takara da cewa , sannan kasan duk duniya babu Wanda yakaini sanka ko ?toh Allah yasani sadik bazan taba San Abin da zai cutar da kai ba ,Sadik nasan Hajiya Amina farin sani , matace wacce bata tsoron Allah ta manta da Allah, sanna matace me San duniya , sadik inaso kayi duba na tsanake akan wannan maganar , Sadik koda ace Ita'yar da kakeso bata da wani mugun hali amma mahaifiyarta fa ,?? kamanta zata iya daurata akan hanya maras kyau ,sanna in ita yarinyar batayi abun da zasu mallakeka ba to nayi imani sai mahaifiyarta tayi Sadik nagama magana kaje ka nemo wata amma matukar ina da rai Rukkaiya ta haramta a gareka!! 

   Sadik yayi shuru kamar ya ji nasihar da mahaifiyartashi tayi mishi , amma da mamaki yatashi   Cikeda tashin hankali yabar dakin bai zarce ko ina ba said gun mahifinshi ,
  Yanashiga ne yatarar mahaifinshi na adduo,i kamar yanda ya saba ,Sadik yazauna gefe yana jiranshi ya idar.  bayan ya idarne , ya juyoo ya kalli Sadik yace lafiya kuwa yaro , kasancewar tun yana yaro sunan da mahaifinshi ke kiranshi kenan, Sadik yace " Aaa baba ba lafiya ba ,  Alhaji sule yace toh menene?
   Sadik ya kwashe komai ya fadawa mahaifin nashi , yakara da cewar kuma har tayi rantsuwa wai bazan aureta ba ,
Alhaji sule mai turare yayi dariyarsu irin ta manyya yace , hummm dama Akan wannan kadaga hankalinka ?Tabbas nasan Hajiya Amina ba macece da za aso hada zuri, a da itaba amma kuma hakan ba lallai ace yarta ma nada irin halin ba , amma kuma inaso kanutso kagane , nasan cewa mahaifiyarka , bazata taba yin abun da za ta cutar da kai ba , amma ni a shawara ta yaro ka hakura da auranan , amma kuma yaro in kaga zaka iya jure halin su toh shikenann Allah ya tabbatar da alkhairi , sannan in matarka , ko munki ko muso sai ka aureta, amma zamucigana da tayaka da addu a, sannan zan sami mahaifiyarta KUYI magana , inahallahu zata fahimta ,
  Cikin jin dadi Sadik yace nagode babba Allah saka da alkhairi  , Alhaji sule yace" kaji zaka aureta a haka kuma zaka jure halinta koh, cikefa jin kunya da sanyin Jiki  sadik yace eh , Alhaji yace to shikenna Allah tabbatar da alkahiri , Sadik ya amsa  da Ameen ya bar dakin
  Ba yan yafita Alhaji sule ya gigiza kai yace hummm yaro , Allah yasani bakomai ne  dalilin dayasa Alhaji sule Barin sadik ya auri Rukkaiyya ba said dan bayason ko Kadan ya takura ma yaro bayason ya ma yaro dole , kuna yaga tsantsar San  dan da yake ma Rukkaiyya a kwayar idonshi amma zai taa tayashi da addu ar zabin alkhairi .

  *Muje xuwa*
*MORE COMMENT'S*😎😎😎
*MORE TYPING*✍️✍️✍️

*STORY AND WRITTEN BY( MUM FU,AD*)

*PLSS SHARE*👏👏

Du hast das Ende der veröffentlichten Teile erreicht.

⏰ Letzte Aktualisierung: Nov 29, 2020 ⏰

Füge diese Geschichte zu deiner Bibliothek hinzu, um über neue Kapitel informiert zu werden!

MAHAUKACI  KISHIWo Geschichten leben. Entdecke jetzt