MAHREEN PAGE 33

En başından başla
                                    

Yah Maheer ya Kula ina yawan tunani, tunda ya tambaye ni sau ɗaya me ke damu na, se kawai na ga lokaci ya yi na in fita daga gidan na je kitso dan in ba haka ba to fa daga tambaye tambayen nan zan karya magana ta zan sanar da shi komai, dan ni ko laifi na yi se na fada masa hankali na ke kwanciya.

Kitso na tafi cikin unguwar gidan su Fateema, ana min kitso ina tunanin anya ba za mu gwada ba? Wataqila mu dace tunda an ce ana dacewa a haihu lafiya.

Sanda ta gama min kitson ma ban sani ba saboda na tafi yawon tunani hankali na baya wajen kwata kwata.

Magana ta min dan na san cewa an fa gama kitson, wannan na miqe na bada kuɗin kitso na musu sallama na kamo hanya na yo gida, ko da na zo Yah Maheer ya fita Masallaci dan yin sallar la'asar, hira mu ka fara da Suwaidatu can na d'akko carpet ɗin da aka malala a tsakanin parlour kitchen da sauran dakuna, qofa na bude na fitar da shi na baza a tsakar gida na hau wankin shi, se da na wanke tasss na shanya sannan na hau aikin cire yana duk da ba bu wani yanar sosai dan ina qoqari matuqa wajen cire ta akai akai, duk aikin nan da nake tiqa  wai dan duk na manta maganar IVF ne, dan ji nake wata zuciyar na fizga ta akan ko za mu gwada ne?

Kwana uku tsakani na kasa faɗa wa kowa kuma na kasa dena tunanin abun, Yah Maheer ya gaji da bin kai na na faɗa masa me ke damu na, qarshe da kai na na zauna na yi wa kai na karatun ta nutsu, cikin rai na na ke faɗin,

'Wai me ke damun ki ne Mahreen? Ki nutsu kar ki sanya wa kan ki wani ciwon saboda tunani, duk abinda Allah ya yi nufin zai faru da bawa, bawan nan be isa ya wuce qaddarar shi ba, sai dai addu'a na sauya wasu abubuwan, dan haka ki ci gaba da addu'a akan zabin alkhairi daga wajen mai bayarwa Allah, ina ki ka bar halayyar ki ta roqon Allah kuma ki saddaqar ki sakankance ki kwantar da hankalin ki dan kin san matsalar ki ta je inda za a yi maki maganin ta? Dan Allah ki manta da komai ki yi facing rayuwar ki ta gaba'

Ina gama wannan tunanin na sanya waya na kira Ameenah na ce yaushe za ta zo? Sanar da ni ta yi ko yaushe nake son ganin ta zata zo, nan take na ce dan Allah ta zo ko gobe ko jibi, alqawarin zuwa gobe ta min, aiko na ji dad'i sosai, domin ta jima ta na min alqawarin duk sanda za ta zo zata zo da garin dankwake mu yi danwake, dama na kwana biyu ban yi wa Yah Maheer favorite food ɗin shi ba wato dankwaken saboda ba flour,this is my chance da zan masa danwaken in ta kawo garin.

Washegari kuwa muka tashi da murnar Ameenah za ta zo, dan kuwa weekend ne Suwaidatu na gida, Yah Maheer na da lecture safe da yamma, ya kuma tafi tun takwas saura dan shi mutum ne da baya so ace wai sai ɗalibai sun jira shi, ya na iya zuwa ya zauna na minti talatin ya na jiran daliban shi ba tare da ya damu ba, fashi kuwa ba halin shi bane se in ya zama dole.

Mu na nan zaune ina ta zuba ido in ga ta ina Ameenah za ta fito ne shirun ya yi yawa, ga yunwa muna ji, bana so na dafa abinci ta zo a sake yin danwake a matsayin mu na waɗanda ke lallaba rayuwa zai zama an yi barna.

Da misalin sha biyu na rana Ameenah ta zo bana mantawa, sai ga ta da garin danwake irin haɗin gidan nan me kyau da dad'i da kan ta ta haɗa ta tankad'e, ko da ta zo sai ta ce za ta yi mana da kan ta, ruwa na je zan d'ora ta ce kar na damu za ta yi komai da kan ta, miya ta ɗora mana miyar gyad'a domin da shi ta ce za a yi, duk ta zo da komai, ta na girki ta na karatun Hausa novel.

Ameenah ba irin girkin mu na 'yan zamani take yi ba, duk da cewa na girme ta a shekaru amma zama da Mama ya sa ta iya girki irin na gargajiya,ko tuwo ta yi maka sai ka san ka ci tuwon da ya dahu da kyau ba irin tuwon mutanen mu na yanzu ba tafashi tuqa, tun ina jin yunwa har yunwar ta tafi ba a gama ba, kukan shagwab'a na fara yi wa Ameenah ina buga qafa daga inda nake a zaune ina faɗin,

"Ni yunwa nake jiiii Ameenah, yunwaaaaa, Allah zan faɗa wa Yah Maheer in ce qanwar shi ta bar ni da yunwa,"

"Ke dai qara hankuri gama wa akai yanzun ga,"

MAHREEN Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin