Chapter 1-2

145 10 4
                                    

*FALAK🍒*
_Gajeren labari_

Zainab Habib (Mom Islam

E.O.W

_Bismillahir rahmanir rahim_

morning 11:30am Thursday 29/12/2022

Iska ce ke kad'awa a hankali, garin yad'auki sanyi sosai, yawancin mutane suna sanye da rigar sanyi.
Tafiya take tana yarfe hannu kamar karamar yarinya,
"Falak"
Taji an kira sunanta cikin kausasashiyar murya, da sauri ta waiga ga mamakinta sai taga babu kowa, juyowar da zatayi taga wasu mutane guda uku ko wanne ya yane fuskarsa da bak'in k'yalle, a tsorace tace "suwaye ku mekukazo yi nan?"
'Daya daga cikinsu ya d'agata cak yasata a mota suka shiga dukkansu suka yiwa motar key, sosai take ihu tana had'asu da Allah babu wanda ya saurareta, wanda aka kira da Oga ya mika saletif aka manne mata baki, tare da wani baƙin k'yalle shi kuma aka rufe mata ido.

•Da sauri  ta sauko daga kan gadon da take kwance tana share zufar dake sintiri a fuskarta, jiki a mace ta nufi k'ofar da zata sadata da d'akin sauran yan matan, tana buɗe k'ofar ta hangosu a kwance sunanta sharar bacci, cikin d'aga murya tace "Munira  Hibba Saudart ku tashi nayi wani mummunan mafarki"
Suna jinta sukayi mata banza, dole ta k'yalesu ta nemi guri a gefen gado ta zauna, sbda bacci ya kauracewa idanuwanta,
A hankali taji ana cewa "ga dakunansu nan ku shiga"
Falak ta waro ido kafin ta shiga tashinsu a hankali, abin mamaki suka jingina wata sanda a jikin Falak suka fice da ita kaf gidan babu wanda ya motsa, sai da aka fice da ita daga gidan.
Cikin tashin hankali Ummu ta bod'e k'ofar d'akinsu Munira, sbda jikinta na bata babu lafiya, kallon agogo tayi taga k'arfe 1:20pm tace "yakamata ku rage wannan barcin ranan da kuka sanarwar kanku, Hibba tayi juyi tana mutsuke ido kafin tace "Ummu ai Falak ma yazo tana ta damun mu bansan lokacin data fice ba"
Ummu tace "na d'auka ko tashiga wanka ne dan naga babu kowa a d'akinta"
Saudart ta diro da sauri ta bud'e k'ofar toilet, wayam tagani babu kowa, cikin tashin hankali dukkansu suka fito sunata Zagaye kowane sashe na gidan Ammae babu ita Babu alamar ta, Ummu tasa hijab taje gurin Mai gadi ta tambayeshi, yace "tun safe yake zaune anan baiga kowa ba.....

Inaso inga inda zaku amshi littafin, inhar naga anyi shar'i da comments read more da yawa zan dingayi duk da labarin bame tsayi bane 08141799224

FALAKрдЬрд╣рд╛рдБ рдХрд╣рд╛рдирд┐рдпрд╛рдБ рд░рд╣рддреА рд╣реИрдВред рдЕрднреА рдЦреЛрдЬреЗрдВ