ABUNCIN WANI PAGE Three

666 24 0
                                    

Tana kaiwanan a labarinta ta fashe da matsanancin kuka😭.

Abu ladan ya numfasa sannan yace tabbas wannan labarin  yanada abun ban mamaki.to yanxu ina mahaifin nasa.

Inna tace tun bayan tafiyar
nasiru a lokacin inada  cikin🤰 LADO mahaifinsa yashiga damuwa matuka ba kadanbah.

Yakoma yau lafiya gobe ciwo.Bayan hahuwar LADO da shekara daya shima saiya fara cin qasa wanda mahaifinsa yasam cewa tabbas LADO ya dauko halin yayansane.

Da wannan damuwar dayake fama da ita itace tayi ajalinsa.

Abu ladan yace tabbas wannan al'amari akwai ban tausayi.

Yanxu dai bazaiyi a zauna a  dinga kallon abunda yafaru da nasiru ya cigaba da faruwa da LADO bah.

Sbd haka zan taimaka muku akwai wani malami👳wanda ya shahara ta fannin aikin aljannu👹.

Zanyi tafiya gobe zuwa garin🏘️ wannan malamin👳domin nasanar dashi matsalar ku da ikon Allah komai zai wuce.

Inna da iya ladi ba qaramin jin dadi😀sukayibah da kuma yi masa godiya sosai🙏.

Washe gari🌅da sassafe abu ladan ya hada kayansa🎒yayi sallama dasu ya kama hanya.

Saida yayi tafiya ta tsawon kwana biyar sannan ya isa garin🏘️wannan malamin👳.

Bai wuce ko ina bah sai gidansa🏚️.

Akayi mishi izinin shigowa ya shiga aka tarbeshi da girmamawa.

Bayan ya samu nutsuwa ya huta sannan yake sanar da malamin👳abunda yake tafe dashi.

Malamin👳dukda kasance warshi kwararre a gurin harkar aljanu👹amma saida yayi mamakin wannan labarin.

Sannan yake sanar da abu ladan cewa wannan tabbas aikin aljanar qasace amma zasuyi iya kokarinsu.

Yanxu zai shirya  nanda kwana biyu saisu kama hanya zuwa wannan garin🏘️.

Bayan kwana biyu suka kama hanyarsu zuwa qauyen su LADO.

Suna isa basu tsaya ko inabah sai a gidansu LADO.

Inda iya da inna suka tarbesu hannu bibbiyu.

Bayan sum huta sannan malamin👳yasaka aka kawo masa LADO.yana kallonsa yaui wata adduah sannan yace zaka iya kaimu inda yayanka nasiru yake rayuwa.

Da budar bakinsa yace eh.

Mamaki yakama iya da inna sosai.

Sai iya ladi tace tun kafin a haifi wannan yaron yayansa yabar gida yake rayuwa a daji taya kuwa zaisan inda dan uwansa yake a yanxu.

Malam👳yace tabbas wannan yaron shikadai ne zaikaimu har inda dan uwansa yake.

Umma tace to amma tayaya kenan.

Malam👳yace kawai kudai kusaka ido kuyi kallo yanxudai dukansu kutashi mutafi.

Suna isa bakin dajin malamin yace yanxu LADO kai zaka jagorancemu.

ABUNCIN WANIWhere stories live. Discover now