A MAFARKI NASANTA

5 0 0
                                    

  💫A MAFARKI NASANTA💫
      I know her in my dreams
                          By
       Pha'eezah Almustapha
         Daga Alkalamin✍️✍️
           💫Fa'eeh BG💫

               Firstlady 🙌🙌

Dedicated to my lovely sis lailat Almustapha Murai💔

------------------------------------------------------------------
--------------------------------------------------------------------
*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCITION📚🖊️*
  
                 *💫P.E.W.A💫*

*Home of perfect essential writer's together we stand🤝*

           *ESSENTIAL WRITER'S📚🖊*

*Pen🖊️*is migthier than the sword *🗡️*

  *Free* 📙

EPISODE1️⃣
PAGE4️⃣5️⃣

TYPING📲📲📲

*Noted edited*

*INDIA*

Zaune suke cikin motarsa shida Dr Aj sunata Bada horn abakin wani makeken gate na Alfarma,Bayan d'an lokaci sai ga wani tsoho ba indiye ya fito daga cikin gidan Yana Furta Aah d'an yaro kasake dawowa cikin sakin fuska  da harshen India  yake maganar inda yak'ara furtawa bayan Dr Ammar ya Amsa da ehh tare da gaida tsohon cikin mutunci shida Aj,"Har yanzu Dai Ba'a sallamo sir ba",cikin yar damuwa Aj ya Furta yanzu baka San Hospital din da yake ba ma'ana inda akayi admitting nasa,"ehh gaskiya bansani ba
Kuma d'azu da hajiya tadawo mancewa nayi in tambaye ta".

Kai Dr Aj yad'aga sannan suka sake yin musabuha tare da barin unguwar gaba d'aya,suna Hawa kan titi...

A Cikin motar  Aj ne  ke ndriving sun Sanya k'ira'ar shekh  Muhammad afif  suna sauraro..cikin  Jan k'aramar tsuka Dr Ammar ya Furta naso ace kafin mubar garin nan nagana da iyayen su Lubna,duk sai nake Jin ba dad'i araina yakai karshen maganar cikin sauke wata ajiyar zuciya,cikin damuwa Shima Aj ya Furta gaskiya yakamata ace munyi sallama dasu kafin mubar k'asar nan.Dan Shima Aj yad'an Saba dasu Lubna sosai Kuma Shima ya hango kamar Ammar dasu Lubna d'in tun lokacin da suka fara had'uwa,sai dai kowa yasan yadda Allah ke nuna iKon sa ta hanyar yin kamannin Yan Adam iri d'aya wasu idan kagansu zaka ce tawaye ne sai dai ko jini basu had'aba hasalima mabanbantan k'asashe Suka fito.

Maharashtra 24hrs hospital suka zarce Dan Bada resignation letter d'insu,cikin jimamin Rashin ganin su Lubna.
Bayan shigarsu Asibitin ne Suma bodyguard dinsu suka parker nasu motocin agefen harabar Asibitin dan suna biye dasu dama,sai dai su sukayi driving da kansu ta hanyar nunawa drivers din nasu Rashin Ra'ayin tuk'in nasu.

Basu zarce ko Ina ba sai office d'in medical director  na hospital din Wanda yake shine shugaban likitota awannan hospital din
Suka Bada takardar barin aiki sannan sukayi signing suka fito,kowannen su office dinsa ya zame,Dan d'aukar Abunda yake Mai mahimmaci ne agare su.

DR . AMMAR  ne  tsaye acikin office dinsa, tsaye akan wata had'add'iyar locker,Yana binciken wasu takardu,locker ce Mai kyau
wadda ta k'ara k'awata office din.cikin shigarsa ta bak'in trouser da t-shirt fara ya tsuke abunsa gwanin burgewa a irin shigar da dai kuka San Doctors  nayi,sai shoes bak'ake Samfurin boot suma masu kyau...

A hankali ya dakatar da Abunda yakeyi  Jin an fad'o Masa office ba Neman izininsa bare sallama,A hankali kuwa  ya juyo Dan ganin wani isasshen ne,Domin bayan Dr Aj yasan Babu wani Mai Masa irin haka.

Da kyakkyawar fuskarta Dr.Malini ya ci karo inda dama zarginsa na itace ya tabbata ta hanyar Jin k'amshin turaren mata a office din nasa da yasan dai nurses basu shigowa Kai tsaye, sai dai ko a telephone a Kira idan wata matsalar ta taso kafin a isko sa a office din. 

💫A MAFARKI NASANTA💫I know her in my dreams Where stories live. Discover now