A MAFARKI NASANTA

2 0 0
                                    

💫A MAFARKI NASANTA💫
I know her in my dreams
By
Pha'eezah Almustapha
Daga Alkalamin✍️✍️
💫Fa'eeh BG💫

Firstlady🙌

Dedicated to my lovely sis lailat Almustapha Murai💔

------------------------------------------------------------------
--------------------------------------------------------------------
*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCITION📚🖊️*

*💫P.E.W.A💫*

*Home of perfect essential writer's together we stand🤝*

*ESSENTIAL WRITER'S📚🖊*

*Pen🖊️*is migthier than the sword *🗡️*

*Free* 📙

EPISODE1️⃣
PAGE4️⃣4️⃣

*Note edited*

TYPING📲📲📲

Sorry guyz for keeping you waiting🙏

K'arar wayar Halee ce Dake chan yashe gefen gado wadda Dr Yusuf yasaya mata Dan su rik'a communication,k'irar itel 160 key pad bayan Neman izinin Baba Adee da yayi inda ya umurcesa da k'aramar zai bata ba Babba ba,in har Android din zai saya mata to ya bari sai tagama makaranta,hakan kuwa akayi yakawo mata k'aramar wayar fara Mai kyau tare da Sabon simcard da yayi register da kansa ya kawo mata.

Ahankali ta cire hannunta daga abincin,Dan dama taji cikin nata yad'auka har tana batun yin Amai saboda Rashin Sabon cin abinci Mai nauyi da yawa.

Wani Kiran ne yasake shigowa alokacin wayar na hannunta ta jawo ta. HUBBI ne ya bayyana akan screen din wayar, Kara wayar tayi akunnenta tare da yin sallama cikin zazzak'ar muryarta,Amsawa Ta D'ayan B'angaren akayi inda Muryar Dr Yusuf ta Bayyana cikin farin cikin da annashuwa Jin Muryar ta Mai cike da natsuwa,"Alhamdulillah shine Abunda take ta furtawa Akan tambayoyin da yake mata cikin farin ciki,yajikin mu yak'ara furtawa cikin murmushi inda "Cikin Kara yin k'asa da murya ta furta uhm Naji sauk'i cikin shagwab'a da sakin guntun murmushinta Mai kyau na Jin kunyar maganar tasa..

Masha Allah,Allah ya K'ara muna lafiya.. ya furta cikin wani yanayin da ya tsinci kansa na Jin sakuwar da tayi Masa wadda har ya fara sabawa da ita domin Halee akwai shagwab'a dama ce kawai da bata samu.

"Amin"

Halee ta furta cikin natsatsiyar voice dinta

Shiru ne ya biyo Baya a tsakaninsu..

A hankali ta tsinkayi Muryar sa yana furta Luv Baki Yi missing d'ina ba Koh??

Cikin d'an Jin kunya da shauk'in soyayya ta furta" nayi man takai karshen maganar tana rufe fuskar ta kamar tana gabansa..

Murmushi yasaki

Sannan ya K'ara furta meyasa kik'a mun flash ko ki Kira ni Dana ce kimun bayan kundawo school yakai karshen maganar cikin Jiran Amsar da zata fito bakinta..

"Aiki ne ya rik'e ni"ta furta Masa cikin sanyinta Wanda sai yanzu Kuma taji wani rauni yataso mata.

Duk da bata fad'a Masa ko wane irin aiki bane yasan tabbas na wahala ne domin A d'an zaman da sukayi ya fahimci Halee ba 'yar Baba Adee bace sai dai ko d'iyar D'an Danginsa sace,Dan dukan da take Sha da tsangwama agurin Baba Asabe yasan kaso guda acikin Uku,domin A wasu lokuttan in ya Kira yana samunta cikin k'uncin yanayi, wani lokacin har takan kasa iya d'aga Kiran nasa,Kuma idan tasamu Iko ta kan d'an sanar dashi wani abun in yafaru,sai dai A duk lokacin da irin hakan yafaru yakan kwantar mata da hankali,shiyasa Ya d'au Alwashi ko ta Halin k'ak'a sai ya Mallaki Halee A matsayin matar sa uwar ya yansa data gama secondry school ko Dan yarabata da zaman gidan hak'urin da takeyi da matar wan na mahaifinta a cewarsa, Ajiyar yasauke a boye ba tare da yak'ara furta mata komai ba kan aiki da tace tayi...
Bayan gama tunanin zucinsa da magana.

💫A MAFARKI NASANTA💫I know her in my dreams Where stories live. Discover now