A MAFARKI NASANTA MALLAKIN FA'EEH BG EPISODE 1 page 1 to 42

17 1 1
                                    

💫A MAFARKI NASANTA 💫

In my dream I know her

By

Pha'eezah almustapha

Daga alkalamin✍️✍️Fa'eeh Bungudu

BISIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Wannan shine littafina nafarko Dana fara wallafawa Allah Ina rukonka daka bani damar kamalashi lafiya kamar yanda nafarashi lafiya👏

*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCIATION

💫P.E.W.A💫

Home of Perfect Writer's together we stand🤝

ESSENTIAL WRITER'S 📚🖊️*

Pen 🖊️is mightier than the sword🗡️*

Dedicated to my lovely sis Laila Almustapha Murai💔

Yaa Allah ina rokon ka kabani damar rubuta abunda Al umma zasu yi aiki dashi kuma su Amfana, kabani ikon rubuta shi cikin koshin lafiya na kammala shi lafiya👏👏👏

Warning!!!Banyarda wani ko wata su juyamin labarina ba ta kowace siga batare batare da an nemi izini na ba wannan dokace kuma duk wanda yayi ban yafe ba wannan labari kirkira ne bada gaske bane duk wanda yayi dai dai da labarinsa to yayi hakuri akasine. Daga cikin abund littafi na ya kunsa
*Tausayi*
*zumunci* *zazzafar soyayya*
*sarauta* *cin amana* *ta,addanci*

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJINKAI

EPISODE 1️⃣

FREE PAGE1️⃣

Natsatssiyar budurwa ce ke tafiya anatse bata kallon komai face inda take sanya kafafunta, tayi nisa acikin tafiyarta kenan ta tsinkayi muryar wata budurwa na kwala kiran Halee! Halee! da jin wannan murya ta budurwar dake kwala kiran Sunan halee ko ba,a fada mata ba tasan khady ce tsayuwar ta da minti biyu sai ga khady ta iso inda take atsaye.

Isowar khady keda wuya ta furta haba Halee kinsan bakya da issashiyar lafiya ya za,ayi kije Aiken baba ta ta maimakon ki fada mata gaskiyar cewa baki da lafiya nasan zata k'yaleki ni sai intafi kinga ko yanzu gudo wa nayi bayan bayan tashiga bandaki,nasan da kin sanar mata da ni sai intafi koh haka ke da dadi ga uwar rana gashi bakya da lafiya,har taga ma mitar ta kyakkyawar budurwar nan da aka kira da halee bata tanka mata ba.. Daga ni dai yarinyar miskila ce😄 chan bayan kamar minti biyu haka ta cigaba da tafiyar ta kamar bataji abunda khady ke fada ba duk da kuwa tana jinta rass kuma tasan tabbas ko ba,a fada ba khady gudowa tayi tabiyo ta.

Da khady taga alamar ba tsayawa zatayi tabata kudin aikar ba na baaba tsaibe,kuma taga alamar yan miskillancin sun motsa dole haka tabita suka cigaba da tafiya atare har suka iso kantin da zasu yi siyayyar ta kayan miya

Sallama sukayi atare amsa musu sallamar tsohon dake tsaye akan tebir na kayan miyan yayi cikin sakin fuska Dan dama baba tsohon yasan su musamman halee ya saba da ita sosai tunda kusan kullum sai an aike ta yin cefane da sauran aikace aikacen akasuwa.

Washe baki tsohon yayi yana furta a,ah Haleematu sadiya ce kayataccen murmushinta tasaki jin ya ambaci cikakken sunanta Wanda mutun daya ne ke kiranta da wannan Sunan sai kuma mutun daya Wanda bata San ko wanene shi agareta ba Amma tabbas aka ambaci cikakken sunanta tana jin wani iri ajikinta

Muryar baba tsohon ce tadawo da hankalinta agaresa yana furta na nawa za,a bada cikin Dan murmushi ta furta baba tsohon ina wuni lafiya,ita ma halee haka amsa musu yayi duka yana dariyar halee aransa najin ga tambayar da yayi mata ga abunda ta furta masa shiyasa yarinyar tashiga ransa Dan akwai tarbiya gata kamila anatse kara mai maitawa yayi" na nawa za,a bada"cikin Dan yin kasa da kai ta furta acikin zazzakar muryar kamar ana busa sarewa ko algaitu gata da sanyi Wanda intana magana zakaji har tsikar jikin ka natashi na Dari uku da ta furta ne yasanya ni dawo wa daga sumar tsayen danayi tun lokacin da ta buda baki ta gaisar da tsohon.

💫A MAFARKI NASANTA💫I know her in my dreams Where stories live. Discover now