Page 23

791 43 10
                                    

"Yanzu kina nufin Ustaz bai san kin watsar da tarbiyar da ya yi miki ba, ba shi da labarin kin bawa saurayi budurci tun a waje saboda soyayya da ganin idan ba ki ba shi ba zai aure ki ba?"

Ridayya ta kasa magana sai wani irin ajjiyar zuciya da take saukewa, a kawo biyar na damuwa da ƙuncin data wanzu da shi tun haɗuwar ta da Zameer yau babu kaso ɗaya. Zainaba ta girgiza kai kawai har yanzu kuka take ita har yanzu tana ɗorawa Ridayya laifi, dukda cewa rayuwa da ƙaddara suna tafiya daidai ne kamar shaƙar numfashi ne da bugun zuciya.

"Wallahi ji nake kamar na ja ki ka zaune na yi miki mahaukaciya dukan kawo wuƙa, to kar na ƙarasa gawar da bata wa ba, amma Ridayya ba ki wa kan ki da Ustaz adalci, ba ki wa zuciyoyinku halacci ba, ina da tabbacin duk sanda Ustaz ya yi baki babu shakka sai ya biki, ya yi miki abinda uba da uwa ba su yi ba, ya raine ki da tafukan hannunsa, ya ciyar dake daga dukiyarsa, ya ba ki ilimi daga baiwarsa, ya ba ki tarbiyya daga cikin abinda ya sani, ya nemi aiki domin ya kula da rayuwarki. Ya yi miki wanka, ya yi miki tsifa ya gyara wannan sumar kan naki mai kama da bishiya, ya goya ki kin zama tamkar bakwaini amma haka zai yi amfani da ɗumin jikinsa domin ki ji shi tamkar cikin uwa mahaifiya, kin yi babban zunubi Ridayya. Da na san abinda kikai masa kenan wallahi tallahi ba zan barshi ya kai ki asibiti gwara kawai ki mutu ya yi jinyar zuciya da kuma mantawa dake bakiɗaya"

Shassheƙar kukan da sai yau ta samu damar yin mai isarta ta ci-gaba da yi tasan ba kowa zai yi mata uzuri ba, ba kowa zai fahimci dalilinta ba.

Zainaba ta ja tsaki tana zabga mata harara ta ce "Wallahi hannuna rawa yake ki daina wannan kukan banzan ko ka kwasa miki mari mtwsss" Ta girgiza kai ta ce

"Samarin yanzu? Wannan gantalalliyar soyayyar da kalaman da mazan zamani ke amfani da shi haka yake ruɗa ƴan'mata fa, musamman a ga namiji fari tas da shi yana saka suttura a tsayar da gemun da wani mai yake shafawa na bana Allah da Annabi bane, da kalaman ƙarya na bugi da zarar ya samu nasarar a kan mace kuma shikenan fa, wata mara kan gadon ma ki na da saurayi amma ba ki san tuni an yi masa baiko da wata ma. Uhm! Soyayya har haukata ɗiya mace na yi tafi talauci barazana ga rayuwar yara mata......,"

"Ai ita ma a haukace take, ta haukace a lokacin" Usman mijin Zainaba ya katse maganar matarsa ta hanyar ɗaga labulen ɗakin ya zuro kai yana faɗa tare da face majina.

"Kai fa Baban Hajjo ba zan taɓa yi wa Ridayya uzuri ba, Allah ɗaya kawai za ta ce mini na yarda. Ka yi tunani idan har Ustaz ya ji labarin abinda ta aikata na yin iskanci da wani ya sai tsinci kan shi? Tsaf zuciyarsa zata buga kwarankwasa"

Ras! Zuciyar Ridayya ta bada sauti ita koda wasa  bata taɓa zama ta yi tunanin abinda hakan zai haifar wa Abbiey ba, bata taɓa tunanin kuskure ta aikata ba domin a lokacin mahaukaciya ce ita, ta samu makantar zuciya data kunne aure, soyayya, da Zameer ɗin sune kawai a idanunta.

"Don Allah mu bar maganar nan Maman Hajjo, ki ɗauka ban taɓa faɗa miki ba, don girman Allah kar ki kalle ni da wannan sigar"

"Wannan zunubi kike faɗa kina wasa ne don ba ki san yadda nake jin zuciyata ba, uwa ce ni fa? Wallahi ina miki kallon wacce ta wofintar da kan ta a waje tamkar tsirara haka kike a idanuna" Wani abu ya caki zuciyar Ridayya ta runtse idanunta zuciyarta na yi mata zafi da raɗaɗi na maganganun Zainaba ta san kuma ba ita kaɗai ba duk wanda ya yi da kalar maganar da zai jefe ta da ita take, ta yi kuka har ta gaji a ranta tana karkarta tubalin ginin ƙaddararta da Ahlinta.

Da ƙyar ta miƙe ta yi sallar asuba domin daman ba bacci ta yi ba. Zainaba ta lallaɓa ta tare da cewa ta yi wanka da ƙyar da ta yi domin ita yanzu tana jin bata wata wani saura banda jiran ranar da mutuwarta zata rusketa. Bata tsaya ta ci abincin da Zainaba ta bata ba ta lallaɓa tare da ficewa daga cikin gidan.

Tunda ta fara take tafiya ta ji faɗuwar gaba na tsananta a ƙirjinta, ta dinga addu'a tana jin komai ya kusa zuwa ƙarshen ta kusa isa gida babu mamaki ma ta tarar da Abbiey yana ciki. Ta faɗaɗa murmushinta ganin gate ɗin gidan abu tare da ƙara tafiyar da take zaton sauri take har ta shiga cikin gate ɗin lokacin Maigadi yana cikin ɗan ƙaramin ɗakinsa. Ridayya ta wanzu tana tunanin ina zata fara zuwa wajan Mami? A hankali ta girgiza kai ta nufi ɓangaren Baba ƙarami kai tsaye bedroom ɗin Ustaz ta nufa da siririyar muryarta tana faɗin.

MUNAFUKIN MIJIWhere stories live. Discover now