Seven

126 13 3
                                    


Dukkaninsu tsaye suke a front yard gurin motoci guda uku da zasu mayar da Governor Sufi Adamu airpot shi da masu tsaronshi tare da wasu tsiraran mutane da suka mishi rakiya daga Nigeria zuwa USA don duba lafiyar ƴar autarshi da ta faɗi ta suma bayan students sun mata prank.

Sufi Adam tsayawa yayi yana kallon Jidda da ke tsaye a front porch ta saƙala hannayenta a cikin pockets ɗin loose jeans ɗinta tana kallonshi fuskarta babu yabo babu fallasa.

"Ba zaki canja ra'ayi mu koma gida ba Mamana?" Ya faɗi hakan cikin tsigar rarrashi amma sai ɗiyar tashi ta kaɗa kanta.

"Daddy mun gama maganan nan tun jiya gashi har ka fito zaka tafi kar mu koma baya please." Ta faɗi hakan tana sauƙowa kan steps ta nufi gurinshi ta tsaya a gabanshi.

Har Governor Sufi Adam ya buɗe baki zai yi magana sai kuma ya rufe kana ya dafa kafaɗarta yana kallon cikin idanunta cike da sonta da kuma tausayinta ya ce,

"Ki kula da kanki." Da haka ya juya ya shige motar da aka buɗe mishi sauran ma suka yi saurin shiga tasu kana motocin suka fita daga front yard ɗin har suka ɓace mata da gani.

Wata wawuyar ajiyar zuciya Jidda ta sauƙe kana ta koma cikin gidan inda ta bar Haajar a sitting room tana zaune tana jiranta.

"Ya tafi ko?" Haajar ta tambaya tana mai gyara zamanta yayin da Mrs Smith take kwashe tray na cups ɗin tea da ta kawowa baƙin nasu da suka tafi yanzu.

"Da kyar. Wallahi har na fara tunanin zai yi forcing ɗina in shiga mota mu tafi." Tayi ƴar dariya nervously.

"Allah Ya tsare wani accident ɗin don na sani sani in aka sake samun akasi Daddy ba zai barki ki ƙara kwana a ƙasar nan ba."

"Amin dai. Zan je in fara assignments ɗina." Da haka Jidda ta miƙe tsaye tana mai ɗaukar wayarta da ke kan couch ta haura stairs tana tuna draman da kuma ɓacin ran da kowa ya shiga kafin Daddy ya barta.

Yana sauƙowa daga jirgi direct ya nufi hospital ɗin da aka kwantar da ita, a can ya samu an yi discharging ɗinta bayan an duba bata da matsalar komai illa tsorita da tayi. Tun daga asibitin bai bari ta koma gidan Haajar ba ya tafi da ita gidanshi da yake sauƙa wanda ta sha zuwa hutu cikinshi, a can ya sakata a gaba da tambayoyi akan yanda ake treating ɗinta a school ɗin amma ta faɗa mishi basa zaginta kawai dai basa shiga harkarta ne, sannan ta faɗa mishi tana da friends har biyu Alice da kuma Christ wanda ta faɗi sunan shi ne don Daddy ya ga abokan nata suna da yawa ba mutum ɗaya ba ce. Tun a ranar ya yanke hukuncin cewa zamanta ya ƙare a USA sannan School ɗin sun tsananta bincike akan wanda yayi aika aikar zai fuskanci hukunci daidai laifinshi. Daddy ya san ba wani horo za'a yi na kirki ba musamman in ya kasance wanda yayi hakan Minor ne ba wanda ya ƙetare shekara sha takwas ba, hakan yasa ya dage cewa zata koma saboda idan wani ma yana da niyyar yin hakan zai yi nan gaba.

Matakin da Jidda ta ɗauka don nuna rashin yardarta da hukuncin Daddy shine ƙin cin duk abincin da aka kawo mata kama daga Dinner, breakfast da kuma lunch na washegarin ranar, a nan ne mai kula da gidan ta aikawa Daddy saƙon halin da ake ciki kan cewa Jidda was starving herself.

Rayuka sun ɓaci domin Jidda kuka kawai take yi ta ƙi sauraron Daddy da yake mata faɗa akan halin da ta saka kanta a ciki wanda zai iya jawo mata rashin lafiya, ganin ba zata ci abincin ba ya dawo rarrashi wanda a nan ma ta botsare daga ƙarshe ya haƙura amma da sharaɗi tare da rantsuwar in dai wani abu ya sake faruwa ko kashe kanta tayi zai ɗauki gawarta ya mayar gida. And she agreed! Again!

School kuma Governor Sufi Adam ya je da karan kanshi ya samu mai makarantar akan wannan cin mutunci da kuma zalunci da aka yiwa ƴar shi ba zai bari ba zai kai ƙararsu kotu saboda rashin kulansu ne ya jawo haka, wanda in hakan ya faru ba ƙaramin ɓata musu sunan makaranta zai yi ba kuma ba zasu so hakan ba. Wannan dalili ya sa mai makarantar ya mishi alƙawarin tsananta bincike don gurfanar da mai laifin tare da cewa hakan ba zai sake faruwa ba. Wannan yasa hankalin Governor Sufi Adam ya kwanta kaɗan sannan ya janye batun ƙara ya kuma gargaɗesu akan taɓa mishi lafiyar ɗiya.

CANJIN MUHALLIWhere stories live. Discover now