Four

148 34 2
                                    

Alarm clock ɗin da Jidda ta saita ya tasheta sallan Asuba shi ya fara ihu da iyakacin ƙarfinsa. Cikin magagin bacci ta miƙar da hannunta saitin bedside inda take tunanin ta ajiyeshi amma bata kama komai ba, hakan ya sa ta buɗe idonta a hankali don ta ga ina ya ke amma sai ta ga ashe a cikin bacci ta juya ƙafafunta sun koma gurin da ake ajiye pillow.

"Kina mace amma kina birgima a kan gado, Allah Ya kyauta amma irin ku ne in kun haihu kuke danne jariranku in baku yi hankali ba." Wannan faɗin mahaifiyarta kenan a wata rana da garin juye-juyenta ta faɗi ƙasa har ta fasa bakinta.

Murmushi ta yi wanda cikin seconds kalilan murmushin ya ɗauke dalilin tuno abun da ya faru wanda shine silar dawowarta USA. Nan take kuma zuciyarta ta tuna mata cewa yau monday, kenan yau dai zata fara zuwa makaranta a matsayinta na sabuwar ɗaliba. Ji ta yi zuciyarta ta buga da ƙarfi domin bata san yanda mutanen ciki zasu ƙarɓeta ba. Nan ba Nigeria bane da zata nuna musu cewa ubanta mai kuɗi ne kowa ya bita kamar shazumamu da sugar ba, nan kowa cin gashin kanshi ya ke yi wanda ta wani gurin sai ɗan talaka ya fi ɗan mai kuɗi popularity, domin in dai yana da kyau da kuma charms magana ta ƙare.

Da wannan tunanin ta shige banɗaki ta yi alwala sannan ta gabatar da sallah tana mai roƙon Allah Ya sauƙaƙa mata rayuwar da zata yi a sabon gurin. Sai da gari ya fara haske sannan ta ƙara shiga banɗaki ta yi wanka ta fito zuwa walk in closet ɗinta jikinta ɗaure da robe. Suturun da ta fitar ta adana akan su zata sanya ta ɗauko tana jujjuyasu nan da nan zuciyarta ta bata cewa ta canjasu ta ɗauki wasu.

A gaban jerin suturun da suka sayo ita da Haajar ta tsaya tana nazarin wanne zata ɗauka domin an ce first impression matters. To bata son a ranar da zasu fara ganinta ya kasance an ga wani aibu game da suturarta. Haka ta yi ta ciro kaya tana canja ra'ayi har ta gane cewa in dai ta ci gaba da haka zata yi lattin zuwa makaranta wanda hakan shi ma bad first impression ne, ƙarshe dai kayan da ta fara adanawa tun jiyan shi ta ɗauko tana dubawa a karo na ba adadi. Green straight pants ne sai green pullover, da white shirt and sneakers, sai kuma green hijab.

Tana cikin saka kayan ta jiyo ana knocking can ƙofar ɗakinta, ta leƙa ta ce a shigo kana ta koma ta ƙarisa saka kayan.

"Miss Sufi, yayarki ta ce in zo in taimaka miki in kina buƙatar hakan." Faɗin Mrs Smith da harshen turanci.

"A'a ki je kawai, nagode." Ta bata amsa ba tare da ta fito ba.

Tana jin Mrs Smith ta rufe ƙofa ta isa gaban mirrow ta yi simple kwalliya wanda powder ta shafa sai mascara da kuma nude lip balm. Jidda tana da kyawu da kuma skin mai kyau da bata buƙarar heavy make up don ta yi kyau, she look simple yet elegant.

Duk abun nan da take yi zuciyarta na bugu sa'i da lokaci idan ta tuna gagarumin aikin da ke gabanta. Kallon kanta ta yi one last time a mirror sannan ta ce,

"You can do it Jidda. Just be nice and everyone will love you."

Da haka fito daga ɗakinta hannunta ɗauke da fancy white backpack ta nufi dinning room inda ta samu Haajar na shan coffee lokaci guda kuma tana karanta jarida.

"You look old Sis, tun kafin ki tsufa kike riƙe jarida da safiyar Allah?"

"Good morning to you too Sunshine. A yanzu da nake da twenty seven jin kaina nake yi kamar ke ƴar sixteen. Karatun jarida kuma Hamza ne ya koya mini nima nace bari in gwada yau. By the way, yace a faɗa miki that he wish you all the best a ranar ki ta farko a school, wai try not to stare at people's ear."

"Ohh mai jan kunne, ina yake?" Faɗin Jidda tana dariya kana ta samu guri ta zauna Mrs Smith ta kawo mata breakfast ɗinta wanda toast ne da omelette sai banana smoothie da plain water.

"Yau ya fita da wuri suna da wani meeting da zasu yi. Breakfast ɗin ya miki ko? Don jiya kin ce bakya son mai nauyi."

"It's perfect." Da haka ta fara cin abincin suna hira sama-sama dalilin Haajar na karatun jarida.

CANJIN MUHALLIWhere stories live. Discover now