😢😭

31 4 0
                                    

🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
A kwana kadan umar ya chanza kamar ba shi ba saboda yadda yake jin jiki ba kadan ba, kasan idon har purple yayi. Kana ganin shi kasan yana jin jiki don Ya rame yayi baki.

Alh ibrahim da ke zaune a kusa da shi yaji umar yace
"Dad"

Yadda ya kira shi ya matukar bashi mamaki saboda a iya sanin sa tun bayan mutuwar sarah umar ya dena ce masa dad.
Idanun Alh suka cicciko da hawaye. Da sauri ya kama hannun umar tare da fadin
"Ina jin ka my son kana bukatar wani abu ne"

Umar ya girgiza kai sannan yayi magana da kyar
"Nasan nayi maka abubuwa da yawa na rashin kautawa da basuyi maka dadi ba. Bana so na tafi ban roke ka gafara ba akan kura kuren da nayi da maganganun masu zafi da neke maka. Kayi hakuri ka yafe min"

Hawayen da suka taru a idon Alh ne suka zubo ya kara rike hannun umar ya matse gam tare da fadin
"Ni ne zan nema gafara a wajen ka, ni zan ce ka yafe min. Ba kai ne kayi min laifi ba nine nayi maka. Decisions din da na dauka a rayuwa ta sunyi affecting dinka sosai and i am to blame. Nayi su a bisa jahilcin fakewar da nakeyi akan rayuwar ka nake so ta inganta. Ka yafe min umar, ka yafe min"

Kuka ne yaci karfin Alhaji ya ci gaba da yi wiwi, umar ma kukan yakeyi.
"Na yafe maka dad Allah ya yafe mana baki daya"

Suna cikin wannan kukun ne khairi ta fito daga toilet, da sauri sauri suka fara share hawayen su saboda sun san idan khairi ta gani zata kafa nata, kuma nata kukan baya jin rarrashi. Kullum a cikin kuka take haka yasa kullum fuskar ta a kumbure take.
Tana ganin su taga emotions kala kala a kwance a faces dinsu. Ta samu guri ta zauna suka ci gaba da tagumi, bini bini se ta share hawayen da ke fito mata ta gefen ido.

Umar ya taba kumatun ta yana murmushi, kana ganin murmushin kasan na wahala yake yi sannan yace
"I have missed seeing your bright face"

Khairi tayi murmushi me ciwo, hawaye na biyowa kan kuncin.
Umar ya sa hannu ya share mata hawayen da ke zuba yana girgiza kai alamar tayi shiru.

Alh ibrahim yana ganin abun na masoya ne ya tashi sum sum ya bar dakin don ya basu space.

Khairi ta rike hannun sa da yake share mata hawayen tana kissing ko ta ina.
"Please get well soon, i want us to be back home. Ina so much koma gida mu ci gaba da rayuwar mu yadda muka saba"

"Do you love me?"
Umar ya tambaya yana kallon cikin kwayar idon ta

Wani zazzafan hawaye ne ya kwace mata, bata taba zaton ze bijiro mata da tambayar nan ba. Murya na rawa tace
"I do, wallahi i do. I love you soo much"

Umar ya sake murmushi sannan yace
"And that's enough for me, nayi ta son naji wannan kalaman daga bakin ki and finally naji su yau"

Khairi ta rakwafo tayi hugging dinshi yana kwance tana wani irin kuka me ban tausayi, shi kuma umar yana shafa bayan ta yana cewa
"shhhhhh its okay"

A haka umma da Abba da Alhaji ibrahim suka tarar da su, basu san ma sun shigo dakin ba se da Alh ibrahim yayi gyaran murya sannan khairi tayi saurin tashi daga rungumar da tayi ma umar.

Gaba daya jikin abba da umma yayi sanyi ganin umar a condition din. Jikin ya rikice gaba daya, ga wasu machines da aka jojjo na masa. Umma kasa daure wa tayi ta fashe da kuka. Tana tuno yadda yar uwar ta zarah ta rasu da yarintar ta gashi yanzu danta ma rai a hannun Allah.

Da kyar abba ya iya rarrashin umma tayi shiru. Umma ta zauna a gefe kan gadon umar tayi mishi addu'a hawaye na zuba, har zata tashi umar ya riko hannun ta sannan ya rada mata wani abu a kunne wanda yasa umma ta kara fashewa da kuka.

Da gudu gudu ta tashi ta nufi hanyar waje kukan yaci karfin ta

Bayan lokaci kadan Abba yayi ma umar da Alh ibrahim fatan samun Lafiya sannan yayi musu sallama gaba daya. Khairi da Alh suka biyo bayan shi suna masa rakiya
Ko da suka fito bakin dakin abba yace musu su koma tunda akwai mara lafiya ba se sun raka su ba. Ya kara yi musu sallama sannan ya fita wajen umma wanda tun da ta bar dakin bata kuma dawowa ba.

SarkakiyaWhere stories live. Discover now