13

104 5 0
                                    

*ZAMANIN MU A YAU*

NA

JEEDDAH ALIYU
&
NANA DISO

*PAID BOOk*

_Team Tagwaye Biyar Novel_
_____________

013

Tunda maryama ta baro gidan anty zuciyarta ke tafarfasa saboda ƙalmar kishiya dataji mahaifiyar tata ta ambata tasani ko da wasa tayiwa abah maganar to tabbas zaiyi biyayya ballantana yadda taga anty ta ɗauki zafi, cikin zafin rai taƙarasa gidan nasu tunda tafito daga mota ma'aikata dake aiki suketa faman gaisheta amma babu wanda taƙula acik'in su, ita dazatayi nasu bangaren sai ƙawai ta nufi bangaren dattijo, salma tayi wacce ko fitowa batayi ba, mamakin ganin dukkan ƴan gidan tayi har hajaru ƙanwar abah itama tazo batare da ta ƙalli ƙowaba ta zagaya inda dattijo yake ta zauna, haka su ismail suka shiga gaisheta tana amsawa ciki ciki, sai data ƙalli mama sannan tace sannu mama ta ƙauda ƙanta hajiya ƙam batabi ta ƙanta ba saima gyara zama datayi tace " kuntaramu Isma'ila amma kunyi shiru lafiya kuwa?" Mama ce ta ƙalleta tace " ai hajiya tunda kikaga antara ƙowa anan aikinsan maganace mai mahimmanci." Ƙallonsu dattijo yayi yace ina sauraronku yau ƙuma dame kukazo?." Mama ce tayi dariya tace " alhaji maganar hadin ƙai ne wannan zaman tunda Ahmad yaƙawo dukiyar ka da ƙomai ƴan uwansa basa samun nutsuwa shine suƙace yanzu tunda bashida ƙomai ko zasu bashi manaja a kamfanin?" Wani mugun ƙallo abah yayi musu dan shi baitaba jin zafin maganganunsu irin yanzu ba.Hajiya ce tace " Eh to kunyi tunani gaskiya" maryama dake gefe tace " saboda wulakanci ismaila yayan nakune manajan? Tunda kun ƙassarashi ai sai ku ƙyaleshi ko yaji da abunda ke damunsa, cikinku dai babu wanda ya'isa ya wulakantamin miji wallahi." Hajaru ce tasa dariya tace " wulakanta na nawa? Ai daman kudin alone kuma anƙarba tun.." maryama ce ta fusata tace " dallah maalama yimun shiru har ƙyayi magana ke idan maganar wulakanta ake akwai wanda yakai mijinki ne? Nace akwai? Naga mijin nawa yasamar masa aikinyi..." Mama ce ta ƙatse zancen da faɗin " To ai mairo sai kiyi hakuri tunda dukiyar ubansu ce inaga ko?" Maryama ta harzuka zatayi magana Abah yagyara murya cikin bacin rai sannan yace " inaso in tambayeku yau shekara nawa da mutuwar ƙakanmu?" Hajiyace tace " shekara 4kenan." " To ƙafin mutuwar kakan namu munsamu kudin dattijo ne? Ina da tabbacin da kudina kukeyin komai kai ismaila tundaga karatunku na secondary har jamia wanene yabiya muku? Wayayi muku aure? Wayabaku sana'a? Wayake ciyar da gidan ? Kunmanta ne? " yada gori Ahmadu cewar mama tana zabga harara." " Ai idan nace zanmuku gori to komai ma sai nayimuku aƙanshi maganar kudin alhaji ficiƙarsa bantaba ciba gashinan azaune million 30 akasamu agadonsa wacce gona ta samar dakudin da wasu runfunan mahaifinsa, ashekaru 4 munsamu riba ninkin tada, wanda gabadaya ƙudinsa na riga na bashi, idan acikinku da mai tunanin inaci da sha da suttura da ƙudin dattijo to tabbas bashida tunani ko ƙadan kai kuma murtala mai bani mañana ba rainawa nayi ba amma zan ƙoma aikin gwamnati na danakeyi abaya, ina muku fatan Alkhairi gaba daya, zakuma ku iya tafiya inason ganawa da mahaifina." Wani murmushi maryama tayi wato dai Abah wayo yayi mata yanada kudi amma ya hanata kudin surgery tabbijan ai wallahi yau sai ya bata ƙudin, tashi tayi tafita inda ƙowanne acik'in su yafita yarage daga mama sai hajiya itama dan Abah yace ta zauna ne. Alhaji daman inason In sanar daku zanƙara aure. Gaban mamane yayi diff diff wane irin aure kuma Ahmad?" Banza yayi mata yace " nayiwa su kawu magana in shaa Allahu jibi za'a kai kudin aure da sadaki." Ai babana kayi kokarima ina addu'a ubangiji yasa albarka yakuma baka ikon adalci." Mama kuwa cewa tayi Allah yataimaka sannan tafita." Datijjo kai yakamata kakira maryama kayimata nasiha danwallahi ina gayamaka hakuri yaron nan yakeyi da'ita." " haka kuma zaicigaba da hak'uri da'ita kamar yadda nafada babu batun saƙi tsakanin sa da maryama dan diyar anty abunda tayimana Allah ne kadai zaibiyata." Murmushi kawai abah yayi sannan yabar daƙin.

Murtala Isma'il akwai matsala fa, mun hadashi da ƙaruwan sun ƙasa galaba akansa har nagaji da bin malaman nan suma babu nasara , yau kuma bakuji me naji ba? Aure abah zai kara aure wai har yaushe ne zanga bayan abah? Yaushe ne tafashe da kuka, tafi akasaka abaynsu wanda yasaka kowanne jiyowa tare da firgici da tsoro yanzu ne loƙacin da zakuga bayan abah yanzu ne, muke da dama." Mama ce tace hajaru? Har yanzu kinada kudiri daman akan dan uwanki?" " Tunda kikaganni anan aikinsan ban hakura ba, hamida itace matar da zai aura dan haka aikinmu zai ci ta hanyar yaudarar da zamuyi mata." " hamida kikace hajaru kowannen su yatambaya da mamaki!. Kwarai kuwa dan haka plan dinmu ta bangaren hamida zai fara.

ZAMANIN MU A YAUWhere stories live. Discover now