Part 3

15 6 0
                                    

Ko awa d'aya ba aiba Ahmad yaqaraso gidansu hameed afalo ya tarar da abokinnasa kwance akan cinyar Ammi ya qurawa TV ido,ganinsa kuma yasa hameed saurin miqewa yana "seyanxu zaka zo ko??nafi awa goma inajiranka "

Zaro ido Ahmad yay yana "haba abokina awa goma fa kace ,to tindaga lokacin da Ammi tamin waya zuwa yanxu ba ai awa d'ayaba "

"Bawaninan qaryane "hameed yafad'i lokaci guda kuma yana had'a rai.

Dariya yabawa Ahmad saboda yasan halin hameed, yau kukai magana dashi gobe zece sati d'aya kenan ko wata gudama shiyasaka yace masa "tom shikkenan hameed na yarda,kaqi barina mugaisa da Ammi ma kana tamin qorafi "yafad'i yayinda yake juyowa gurin Ammi yana gaisheta,cike da fara'a Ammi ta amsa tace "ai ni dama jiranku nake ku gama abinku semu gaisa ,yanxu ina zaku to ??"

Kallon hameed Ahmad yay yace "ina kake so muje "

"Ohoo nide kakaini irin wajen rannan "yafad'i yana d'auke kansa gefe guda

Murmushi ahmad yay yakalli Ammi yace "Ammi inaga yana maganane akan inda mukaje rannan calypso garden wajen a wuse 2 yake "

"Ohk to badamuwa Amma dan Allah ahmad karkwi dare "

"Inshallah Ammi ba zamu dad'e ba ,to zaka sauya kaya koda wad'annan zamu tafi??"ahmad ya tambaya yayinda yake kallon hameed.

"Banyi kyau bane ahakan "hameed ya tambayeshi

"A'a fine shigan yy tashi muje "yafad'i lokaci guda kuma yana miqewa tsaye,shima hameed miqewa yay sannan sukawa Ammi sallama daga haka suka fice.

Motar Ahmad suka shiga qirar range rover kana yajuya sitiyarin motar yad'au hanyar wuse 2 ,waqar Ayrahh star yakunna amotar "Blood samaritan,"ahankali Ahmad kebin waqar yana nishad'i kallon abokinnasa yay inda yaga hankalinsa gaba d'aya yana kan street da alamu wani tinanin yake wanda kuma ba'ason yadinga shiga wannan yanayi saboda likitoci sun tabbatar da hakan yana qara dagulamai lissafine saboda chronic over thinking can also alter brain functions by changing it's structure and connectivity ,hakan yasa Ahmad saurin tab'ashi yana "abokina tinanin me kake? Duk da tab'ashin da yay hameed hankalinsa be dawo kansaba,kuma tab'ashi yay sosai yana "kai wai me kake tinanine?"ai firgigit cikin razana hameed yajuyo yakalli ahmad yana wani irin ajiyar zuciya kamar wanda yaga miciji ajikinsa,"hameed wannan razanar fa "ahmad yatambaya ganin yacce ya birkice duk da yasan hakan ba wani baqon abune ahalayyan hameed d'inba.

"Kaine ka bani tsoro ai na d'auka nikad'ai nake tafiya akan titin senaji kuma antab'ani shine na tsorata "hameed yafad'i fuska ahad'e damashi ba wani ma'abocin dariyabane,sedai inyana tare da likita zaka iya ganin fara'arsa dan ita kad'ai Ke sashi nishad'i ko in yana kallon cartoon inyaga tom and jerry suna wa junansu mugun ta.

"To aishikkenan kagama mun qaraso gurin as usual da nake gayama dan Allah abokina in yarannan sunzo kadena had'a rai kaga qawayena ne koda bazaka kulasuba Amma kana sakin ranka "

"To kace musu su dena kallona se sita kallona haka kurum "hameed yafad'i yayinda yake qoqarin sakkowa daga mota

"Tom shikkenan zan gayamusu kasaki ranka "Ahmad yafad'i yayinda suke qoqarin shiga gurin.

Coffee kawai sukai order nan danan waiter takawo musu saboda dama abinda hameed Ke so kenan,aikwa Ahmad kamar yasan za'arina yasan tabbas inde wannan mayyar yarinyar taga hameed seta zo gurin shiyasaka tinda ya hangota ta tawo ya d'auke kai.

"Hello sannunku shine shan  coffee ba gayyata "meemi tafad'a lokaci guda kuma tanajan kujera domin ta zauna.

Ko kallonta hameed beba ballantana yabata amsa,se ahmad ne yakalle ta yace "to ai gashi kin kawo kanki ko "

Satar kallon hameed tai kana ta wani gyara riga ta na wani kashe ido na banza saboda wanda take danshi be masan tanayiba "to shi abokinnaka be maganane?naga tin rannan yaqi sakin fuska bare yay magana "

"Look sorry meemi be cika son surutu da yawa ba more especially mara ma'ana "ahmad yafad'i yayinda yake kai mug din coffee bakinshi.

Ai tsaye meemi ta tashi kana ta buga tebirin dake gurin harseda coffee dinsu yay rawa tace "look Ahmad bara kaji in gayamaka nasan kome  kake nufi wato zeenat ta bika ta bayan fage domin neman soyayyar hameed ko shine zaka wulaqantani to kasani cewa wallahi matuqar ina numfashi ba wacce hameed ze aura face ni mu zuba mugani " tana gama fad'in haka tad'au jakarta fuuu tabar wajen.

Shikwa hameed dafe kansa yay saboda maganarta datake masa yawo akunne ahankali yace "Ahmad tashi mubar gurinnan,meyesa zatana kiran sunana alhalin nibansantaba ,kaima kadena fad'a da mata kaga zata zubar min da coffee Kaga tashi mutafi "

Ahmad daya riqe baki dan takaici kallon abokinnasa yay yace to mutafi aransa yana ayyana cewa baze qara fito da abokinnasaba sedai guri privacy saboda yasan halin'yan matan nan ba hankali garesuba,kuma sarai yasan wataran suka damu hameed ze iya tsinkamusu mari ko ya farfasa komi nagurin dan when he was angry he has no control.

—————-b'angaren Airahh kuwa tinda tashiga d'akinta bata sake fitowaba kayan bacci tasaka tai kwanciyarta,hakana mutanen gidan duk sun kwanta,momy ce takalli daddy yayinda suke shirin kwanciya tace "Engr anyakwa Airah tanason had'innan daka yanke musu? Bama wannan ba ina tsoron ranar da Airah zata San gaskiya kana tinanin zata iya cigaba da zama da hameed koda ya warke?"

"Hajiya nafisa kenan,abinda babba ya hango yaro ko yahau sama ta bakwai baze gansaba,ninasan dalilin dayasani shirya wannan auren ,domin wannan shine hanya d'aya da zan shafe duk wani abu tsakanin malam sani da qanina suraj "

Gyara bargo momy tai tace "Amma dai duk ranar da Airah tagano cewa mahaifin hameed shine sanadiyar rasa iyayenta to tabbas Kasan meka had'a "

Afusace daddy yakalleta yana "nafisa wannan wace iriyar maganace da alamu Ke zaki gayamata ko ,to wlhy duk ranar da kika bari ayrah tasan wannan maganar abakin aurenki "

Riqe baki momy tai tana "me yay zafi daga fad'ar gaskiya Kaga seda safe "tana fad'in haka taja bargonta ta kwanta.

———-ahmad seda yamaida hameed gida tukunna ya wuce gidansu dake gwarinfa yasha albarka wajen Ammi,ahanya kuwa seda zeenat ta mishi wajen missedcall goma , qarshema test tamasa "naji ance kunfito tare da hameed inata kiranka kaqi d'agawa kuma kaikamin alqawarin zaka had'a ni dashi plx ka d'aga wayana "yana gama karantawa yaja wani dogon tsaki kana yakashe wayan gaba d'aya dan inta fara kira setai missedcall hamsin.

Washe gari d sassafe iyalan Engr mukhtar balah suka tashi saboda yau sunada taro agidan na graduation d'in shuraim hakan yasa kowa kintsawa d wuri daganan suka fara zuwa makarantarsu wato noble hall academy,inda suka halarci graduation d'in bayan ankammalane suka dawo gida,agidan suka tarar da Ammi har tazo se abokan shuraim da ba arasaba,a babban falon daddy akai decoration yayinda chef Airah ana kitchen ana had'a cake ,flour ta zuba 3cups , se sugar 1/5 ,se butter simas guda biyu sannan ta zuba kwai guda 12 ,se vanilla da baking powder sannan tai mixing nasu sosai kana tai baking na cake d'in sannan tazo ta had'a whipping cream nata kana taiwa cake d'in decoration me kyau inda aka rubuta happy graduation shuraim,cake din ba qaramin kyau yay ba kowa seda ya yaba,ba kamar shuraim me gayya me aiki,haka akai walimar graduation d'in cikin farinciki anci ansha anyi walwala,bayan kammala waleemanne daddy yakira Ammi da momy domin su tattauna akan zuwansu azare dan tambayo lokacin da za asaka ranar auren Airah da hameed,Ammi ce tace "
"To ina ganin muje next week me zuwa a weekend tinda ranar ba aiki kuma ita kanta Airah tana off setaje tinda ta dad'e batajeba "

Daddy ne ya gyara zama yace "eh shawaranki yayi Amma inaga Airah agida zamu barta domin ba lalle aranar zamu dawo ba nasan halin baba balah baze bari mutaho ba kuma kinga anan za'abar hameed seta kula dashi koya kuke gani "

Momy ce tace "eh yayi sosai "

"To Allah yakaimu nextweek "daddy yafad'i
Ammice ta amsa da "Ameen"

ABDULHAMEED 2022Where stories live. Discover now