Page 2

15 3 0
                                    

Bayan Airah ta sakko d'akin Ammi ta nufa direct inda tasameta tafito daga toilet da alamu alwalar magriba tai "Ammi nizan wuce "airah tafad'i tana kuma gyara mayafinta.
"Doctor bazaki tsaya ki sallar magriba ba???ya mutuminnaki nasan ya cinye abincin ko ?"

"Ehwlhy Ammi dama yunwa yakeji Amma dakyar nashawo kansa,Ammi inajin innaje gida kawai nayi sallar dan zan biya supermarket kuma banso nai dare "
Ganin qarshen watane yasa Ammi bata matsa dole setayi sallan ba ,bata saniba ko tana hutun sallah ne kallonta tai tace "to Airah badamuwa,amma Airah inason mi wata magana dake duk da naga bakison ki dare Nima kuma inaso na tada sallah Amma maganar ba ta wani Jan lokaci bane ,kigayamin gaskiya doctor da amincewarki da son ranki zaki auri ABDULHAMEED,dan Allah karki ji kunyata ko ki b'oyemin ked'in tamkar 'yata kike dan Allah kigayamin gaskiya??"

Sunkuyar da kanta qasa Airah tai banda abin Ammi taya zata iya dubanta tace batason d'anta fisabillahi "Airah bakice komiba,karki b'oyemin koda kin b'oyewa Engr saboda nasan halinki da kawaici gayamin gaskiya kinji 'yata "

Aigaba d'aya Ammi ta d'aureta da jijiyoyin jikinta wannnan baiwar Allah me tsananin karamci da mutuntawa agareta taya zatace batason auren hameed taya zata iya cemata itad'in bazata iya rayuwa dashiba hakan yasata cewa "Ammi meyasa ni zanqi amincewa da aurenmu da hameed ,atinani ba wacce tafi da cewa dashi kamata saboda ninasanshi da yanayin halayarsa Ammi karkiji komi da amincewata "

Ajiyar zuciya Ammi tai wacce ta bayyana matuqar farincikinta tace "Allah yayi miki albarka kinji,ki miqan gaisuwa wajen hajiya nafisa da Engr "

"Inshallah zasuji Ammi "Airah tafad'i yayinda take qoqarin bud'e qofar d'akin domin tafiya .

—————-tana shiga motarta tafashe da wani matsananci kuka me tab'a zuciya,"Innalillahi ina zansa kaina ni Airah ba uwa ba uba wazan gayawa cewa banson ABDULHAMEED duk wad'anda zan gayawa damuwata su sharemin hawaye sud'in sune iyayen hameed shin waye ze fahimci cewa duk abinda nakewa hameed tausayi ne ba soyayya ba da kuma sanin cewa abinda yashafi aikinane dole nasan yadda zan shawo kansa ,yanxu nida nake da burin samun zuri'a wayaga ranar haihuwata shida bayajin sha'awa kwakwata Innalillahi nashiga uku "wani zazzafan hawayene yakuma gangaro mata ,ahankali tasa tissue ta goge hawayen kana taja motar tafice daga gidansu hameed super market ta nufa inda ta dad'o always guda biyu sannan tasiyo kayan cake wanda zatawa shuraim kana ta ja sitiyarin motar zuwa gidansu dake unguwar maitama abuja.

Horn biyu tai securities suka bud'e mata gate takutsa kanta cikin gidansu ta ajjiye motarta aparking space kana ta nufi cikin gida koda tashigo falo ba kowa hakan yasata saurin hayewa sama,afalon sama ta tarar da momy nafisa da shuraim suna kallo,"momy barka da gida kingani seyanxu ko ??kinsan halin yaya hameed gashi kuma seda nabiya super market "

"Aikwa daga ganinki kingaji kishiga ki watsa ruwa dama ke muke jira kizo mi dinner "momy tafad'i tana kallonta

Shuraim ne yakalleta yace "aunty Airah Wai dan Allah bazakimin cake dinba ne gobe fa graduation d'inmu na school "

Da sauri tace "kwantar da hankalinka shuraim ai saboda kai nabiya super market nasiyo kayan cake d'in Kaga ta bud'e masa ledar hannunta su whipping cream ne da sprinkles se ragowar kayan cake d'in tace "ina zanmanta shuraim anzama babban mutum angama secondary school za ashiga jami'a "

Murmushi yay yana "Yawwa aunty Airah ai na d'auka kin mantane "

"Maza kitsaya kina daka ta shuraim karkije ki wanka ki huta danni innagaji abincina zanje naci "

Tace "haba momynmu ganinan zuwa sharp sharp "tafad'i tana dariya yayinda take kutsa kanta cikin d'akinta,rayuwarta itada momy kwatakwata bazakace ba ita tahaifetaba,hakana inba agayamakaba bazaka tab'a cewa ba 'yar gidan bace tinda tana shekara biyar daddy ya d'akkota ranar da akai sadakar bakwan iyayenta inda suka rasu ahanyar komawarsu gida daga abuja zuwa bauchi azare ,mutuwar ta daki daddy da momy ganin cewa ahanyar kawo musu ziyara suka rasa ransu sedai abin Allah Airah ce kawai ta tsira daga had'arin hakan yasa daddy d'akkota tareda alqawarin riqeta har qarshen rayuwarsa saboda baban Airah wato Malam sani babban aminin daddy ne tin yana qarami dan in daddy yaje gidan kakanninsa dake azare rabin zamansa agidansu sani yake wanda suke fulanin usili hakan yasa basa banbatashi da sani saboda kara irin tasu tafulani kuma hakan yajawo d'orewar amintakarsu har girma,duk da Kasancewar familynsu daddy akwai kudi hakana shikansa Engr mukktar (daddy)Allah yabashi kudi da wadata Amma hakan be tab'a komi a abotarsuba ,sedai akwai wani sirri wanda banda daddy ,Ammi da momy ba wanda yasani kuma sirrine wanda yashafi qaninsa suraj mahaifin hameed da malam sani mahaifin airah ba wanda yasan wannan sirrin duk duniya bandasu,hakan ne kuma yabawa daddy qarfin gwiwar had'a auren Airah d hameed ,amma yana tinanin meze faru alokacin da airah tasan gaskiya........wannan kenan...

  ——-agaggauce Airah tai wanka ta shirya riga tasaka mara nauyi se hular data saka akanta,kana tafito  dining ta tarar dasu kowa na gidan ya hallara saboda al'adar daddy shine ahad'u aci abinci musamman na dare shiyasaka kowa ya hallara,daddy,momy,Airah wacce take itace babba agidan inka cire aunty khadija babbar 'yar daddy dake aure akano se me binta hisham wanda airah tabashi shekaru uku inda yake karatu a Oxford university dake ingila wacce Airah tai graduation shima yazo gida hutu se qaraminsu shuraim wanda shima yayi candy ,daddy d'an bokone sosai hakana matarsa hajiya nafisa hakan yasasu cewa yara uku sun ishesu ga kuma Airah wanda suka zama su hud'u ,cikin raha da annushuwa suke cin abincin daga ganinsu Kaga gidan farinciki.

Daddy ne yakalli shuraim yace "tokai yaza aine da graduation d'in naka ?"

"Eh daddy aimuna kammala graduation dinmu na school gida zamu dawo aunty Airah zatamin cake inyaso senai shagalina agida "

Daddy yace "banda ka wahalar da ita meyasa bazakaje osis kasiyaba "

Murmushi Airah tai tace " daddy ai wannan cake din na alqawari ne tin yana SS 2 nace in yay graduation zammasa cake "

Hisham ne yace "caff aikwa dole cake yakamaki yacce shuraim keda naci kace zaka masa abu "

"Ainasan me na tarowa kaina shiyasa tin jiya nasiyo komi "

Mom ce tace "mude ai cake muci "

Dariya daddy yay yace "anan kikafi kauri ai "

Gaba d'ayansu dariya suka saki inda mom tahad'e rai.

"Daddy Wai yaushene d'aurin aurenne anyakwa zan koma school base anyi bikinba "muryar hisham ce kewa daddy tambaya.

Wani harara Airah ta watsamai ,shima kashe mata ido yay saboda yana sane so yake ai maganar bikin.

Daddy ne yakalli hisham yace "ai inaji seka dawo kam Dan se munje azare,munji yaushe yakamata asaka tukunna Amma de duk da haka baze wuce zuwa nan da 3 month ba "

Wani rasss qirjin Airah yabuga hakan yasata kasa had'iye abincin bakinta.

"To doctor ina zakuje honeymoon?? Dubai ko ina??"muryar momy taji ta watso mata tambayar,aranta tace "honeymoon dawa??? Hameed ?? Honeymoon ko wahala "

"Kinyi shiru ko de  a ingila zakwi "muryar daddy takuma ji ya watsomata tambayar,hakan yasata saurin miqewa d'aga kan dining d'in tana "uwa ringing d'in wayana nakeji bara naje naduba "daga haka ta samu ta sulale saboda batada amsar dazata basu.

Tana shiga d'aki ta kulle yayinda tai rub da ciki akan gadonta wasu hawaye ne masu d'umi yafara gangaromata saboda da tana ganin abun kamar wasa Amma yanxu kam ta tabbatar da cewa aurenfa ba fashi se anyishi.....

—-B'angaren hameed kuwa bayan yatashi daga bacci,nan Ammi tazo tasashi yay alwala yay sallah,sannan ta sashi agaba suka sakko qasa saboda likitocinsa sunce adena barinsa shikad'ai hakan yana qara sawa yadinga yawan tinane tinane,kallon TV yake Amma hankalinsa kwatakwata bekai kallon Ammi yay yace "Ammi tashi kikaini gurin Ahmad "
Hameed da daddarennan me zakamasa?? Kawai naji dad'i rannan damuka zaga yauma inaso yafita dani,Ammi taji dad'in abinda yafad'i wato d'an fitan da sukai yaji dad'i ,Amma abinda take tunani shine ,duk da ahmad yakasance abokinsa kuma amininsa wanda hameed d'in be tab'a mantawa dashi to amma yau da gobe se Allah kamar yana takuramasa ,muryarsa taji yana "bafa wani gurin zamu ba Ammi gidansu likita ze kaini "

Tace "haba hameed ba d'azu likitan tazoba "

"To Shikkenan coffee zai kaini nasha "ganin de ya matsa yasa Ammi d'aukan waya tare da kiran Ahmad inda tagayamasa halin da ake ciki hameed yace lalle seyazo sun fita,shima be damuba Dan yasan halin abokinnashi sedai shi matsalar sa d'ayace inde suka fita da hameed 'yanmata ke damunshi a lalle dole seya had'a su dashi shiyasa be soma yafita dashi saboda yacce 'yan mata ke crushing nashi ,amma yazeyi haka ya amsawa Ammi da cewa gashinan zuwa yanxu ze shirya yazo su fita,godiya Ammi tamasa kana takatse wayar sannan takalli hameed tace "to gashinan zuwa "murmushi hameed yay sannan yay lamo akan kujerar dayake kai yana dakon abokinnasa.....

ABDULHAMEED 2022Where stories live. Discover now