PAGE 75-76

18 1 0
                                    

              ♻️♻️HAJNA ♻️♻️

Mallakin :Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya
https://www.wattpad.com/user/QUEENNASMERH08?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
PAGE 75-76
**********************
Wayar shi ya ɗauka, Hajna bata ce komai jira take taji me zai ce, taɓa wayar ya shiga yi, can sai ya kara ta a kunnenshi, “hello baby ", ban ji me aka ce ɗayan ɓangaren ba, sai ji nayi yace “ina fatan dai kina lafiya, kuma tana kularmin da ke", shiru yayi dan ya jira me zata ce, sannan yace “ohk babyna ki kula sosai, kuma idan kin dawo kin tashi da wuri ki kira ni ", kashe wayar yayi yana kallon Hajna da ƙura mishi ido, bata san miyasa ba amma ranta ya ɓaci sosai, kuma ba zata iya ɓoye yanayinta ba, kallonta yake yi, a hankali yace “lafiya dai kike kallona haka, abokiyarki ce fa", cike da ƙulewa ta tashi, “Hajna " ya kira sunanta, amma bata juyo ba, dafe kai yayi, yace “Ohhh Allah me na aikata kuma haka" sai kuma yayi murmushi dan shi be ga dalilin da zai sa ranta ya ɓace tunda ita ba budurwar shi bace, sai kuma zuciyarta tace idan fa itama tana sonka, to yama zai yi ya shawo kanta bayan kishi yasa tayi fushi.

   Tana shiga ɗaki, ta shiga watsi da kayan ɗakin, bata san dalili ba, amma ranta ya ɓaci, cikin rashin sani taji hawaye su sauko mata, da sauri ta goge tace “wai me yake damuna ne ", zuciyarta tace so, Hajna tace “ina bazai yuyu na so wani ba, Qaseem ya cire min wannan kalmar a rayuwata", da sauri kuma ta rufe bakinta tana jin wani yanayi game da Farween, da wannan tunanin ta gyara makwacinta, sannan ta kwanta, ta jima tana juyi akan gado, kamar yadda shima Farween ke yi, ya rasa ganewa ba dai Hajna son shi take yi ba, murmushi yayi yace “Allah ya kare min ke Halia "addu'a yayi sannan ya kwanta, dan ƙa'ida ce kafin ya kwanta barci Halia yake fara ma addu'a sannan shi, abun ya zama jinin jikinshi.

Washe gari da safe, Hajna ta shiga kitchen ta shiga yanka naman kaza, sai ta gama sannan ta tafasa shi, bayan ya tasafa, ta zuba kayan miya da sauran kayan ƙamshi ta ƙara ruwa ciki sannan ta rufe, doyar da monica yanka ta ɗauka, soya ta tayi, sannan ta soya ƙwai, ruwan zafin tea ta ɗaura lokacin da ta sauke pepper soup ɗin, sannan ta zube a kula, itama doyar cikin kula ta zube ta, sannan ta zuba ƙwai, ruwan zafin ta duba har sun tafasa, dan haka ta juye a flask, tare da Monica suka jera kayan cikin kitchen, sannan ta koma ɗaki ta sake yin wanka, ta canza kaya, dan Aunty Farwa ta koya mata yin wanka duk ta shiga kitchen.

   Ƙamshin girkin da Hajna tayi ya daki kunnen Aunty Farwa, murmushi tayi, sannan ta ƙaraso gaban dinning ɗin ta fara cin abinci, dan sauri take zata fita, Aisha ce ta fito, itama zama tayi ta fara cin abincin.

  HAJNA ce ta fito daga ɗaki, “ina kwana Aunty Farwa "ta faɗa tana zama, “lafiya ƙalau ƴar nan ya gajiyar jiya", “Alhamdulillahi "Hajna ta faɗa tana zuba abinci, har ta gama ci su Aunty Farwa basu gama ba, kwashe kwanon da ta ci abinci da shi tayi, tana fitowa daga kitchen idonta suka yi tozali da Farween, murmushi ɗauke a fuskarshi, bata san lokacin da ta sakar mishi murmushi ba, “a zuba min abinci "ya Faɗa, Aunty Farwa tace “Hajna zuba mishi", bata ce komai ba ta shiga zuba abinci, a kan center table ta aje abinci, zata wuce yace “zauna ki taya ni fira mana", ba musu ta zauna dan bata so Aunty Farwa tayi tunanin wani abu, roƙon Allah take Allah yasa Aunty Farwa ta fita ta samu ta tafi.

  Abinci ya kai bakinshi, wani daɗi ya bugi kunnenshi, yace “ummmm wannan abinci haka waya dafa", Aunty Farwa dake iya jiyo su tace “aikin Hajna ne", gaɗa kai yayi yace “kin iya abinci gaskiya " abinci ya shiga ci hankalin shi kwance, Aunty Farwa kuma ta ɗauki jaks tace “ni zan fita, sai anjima, Aisha ki ɗaura abincin rana, Hajna tayi na dare, kice ma Monica zata iya tafiya gida idan ta gama aikinta sai gobe kuma", “to mommy a dawo lafiya "Aisha ta faɗa.

  Wayar Farween ce ta shiga ringing, kallon sunan da ke yawo kan wayar Hajna tayi, Baby taga an rubuta, wani zafi taji ranta, da sauri ya ɗaga “hello baby sai yanzu kika tashi", “eh se yanzu "ta faɗa, murmushi yayi yace “to ki ci abinci kin ji, take care" ya faɗa yana kashe wayar, tashi Hajna tayi zata wuce, taki biyu yayi ya kama hannunta, “me yake damunki ne, duk lokacin da nayi waya da Halia sai kin yi fushi ", shiru tayi, “ki faɗa min miyasa", hannunta tasa ta ture shi, sake riƙe mata hannu yayi yace “ faɗa min miyasa", “ ina sonka! "ta faɗa da ƙarfi ba tare da ta san ta furta, da sauri ta rufe bakinta, cike da mamaki Farween ke kallonta, “nima ina sonki Hajna, ina sonki" ya faɗa yana murmushi, Aisha da ke zaune tana kallon ikon Allah ta tashi daga inda take tace “kuna son juna tun yaushe ", “na ɗauki tsawon lokaci ina sonta, a taƙaice ma shekaru" Farween ya faɗa, Hajna kuwa cikin sauri ta shige ɗaki, ko kaɗan bata da niyyar faɗar haka, a taƙaice ma bata san ta faɗa ba, murmushi tayi, sai kuma ta ɓata rai da tuna da Halia, yanzu ya zata yi, tana kishin Farween sosai, fiye da tunaninku.

“ Uncle Farween miyasa take fushi da kai " Aisha ta faɗa, Farween yace “saboda Halia", Aisha tace “miyasa baka faɗa mata wacece ita ba", Farween yace “saboda bansan tana sona ba, kuma yanzu bazata saurare ni ba", Aisha tace “zan faɗa ma mommy, nasan zata mata bayani yadda zata gane, ka kwantar da hankalinka, zata haƙuri, indai akan aunty Halia ne "murmushi yayi yace “to Allah yasa, nima zan yi farinciki", Aisha tace “ni zan fika farinciki, sannan ka je gobe ka ɗauko Aunty Halia yadda Aunty Hajna zata fahimta, yanzu bazan faɗa ma mommy ba sai ka ɗauko ta ", Farween yace “har Abuja kike so naje", “eh mana ke hau jirgi zuwa da dawowa zaka yi sauri", Farween yace “gobe da safe zan je insha Allah ", Aisha tace “Allah ya kaimu", “ashe kina da hankali "Farween ya faɗa yana jan kunnenta, “hmmm naji, ni dama nayi missing Aunty Halia gashi baka barin ta yawo" , “eh so kike ta dinga yawo kamar ke, ai ƙarƙashin Farween take ba ke ba sarkin" yawo" Farween ya faɗa yana murmushi, “hmmmm amma ai kai kana yi ", yace “ni namiji ne ita mace".

Anan zan dasa aya........... ✍️
Queen ɗinku a ko yaushe.

Kar ku manta kuyi following account ɗina na Wattpad ta link ɗin da ke sama.

Haɗin guiwar :Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya

ALQALAMI YAFI TAKOBI ✍️♻️♻️♻️♻️♻️♻️💃🏻

♻️♻️♻️HAJNA ♻️♻️♻️Where stories live. Discover now