TAFARU TA K'ARE......Anyiwa m...

נכתב על ידי 68Billygaladanchi

172K 15.1K 1K

"Mesa kake ambatar mutuwar nan wai, idan akan nace banasan kane kayi hakuri ina sonka wlhy, fiye ma da tunani... עוד

page 1
page 2
page 3
page 4
page 6
page 7
page 8
page 9
page 10
page 11
page 12
page 13
page 14
page 15
page 16
page 17
page 18
page 19
page 20
page 21
page 22
page 23
page 24
page 25
page 26
27
page 28
page 29
page 30
page 31
page 32
page 33
page 34
35
page 36
page 37
38
39
page 40
page 41
page 42
43
page 44
page 45
page 46
page 47
page 48
49
page 50
page 51
52

page 5

2.9K 293 14
נכתב על ידי 68Billygaladanchi

*🙆🏻🙅🏻TAFARU TA K'ARE🙆🏻‍♂🙅🏻‍♂.......Anyiwa me dami d'aya sata*

*Billy Galadanchi*

*Haske writer's Association*

*Sadaukarwa ga Ameena jibril muh'd (Slimxy)*

*Barka da sallah*

                  05
Haka ta zauna wurin jugum jugum se kiran 'yan gidansu takeyi da kuma maman shi tana cewa su masa adu'a...mahaifiyarsa makam se a sannan tasan cewan baida lafiya, koda yake tasani amma bata zata abin yakai cenba dukda yake ta kula sosai baya cikin walwalar sa kuma yana rama a tsaitsaye, adu'a suka duk'ufa yi har Meenal d'in wacce duk tagama firgicewa....sa'o'i kusan goma sha biyu akayi ana gudanar da aikin kasancewar case ne wanda basu saba gani ko sanin irin saba, Sanyine ya tab'a masa huhunsa abin mamaki kuma yaketa dagargajewa, yana matuk'ar ban tausayi, sunsha mamakin ganin yanda yaketa kumbura ma, da k'yar da yardar Allah suka daidaita inda zasu iya d'in kannan aka sallame wannan aikin....

    Tunda aka fito dashi daga aikin be farfad'o ba har kusan sa'o'i sha biyar, hakan ce ta sanya suka mik'ashi ICU inda ze samu wadatacciyar kulawa me ma'ana....Meenal hankalinta yakai k'ololuwa wurin tashi tashiga diririta ainun, haka ya kwana biyar acen batare daya farfad'o ba, dukta fice a hayyacinta  tashiga walahaula...se a kwana na biyar ne ya farfad'o Alhamdulillah kuma ya samu sauq'i sosai, danma lokaci d'aya ya soma magana tasha murna ba kadan ba, haka sukayi satuka hud'u da kwana uku kan suka baro garin yana cike da jin dad'in samun lafiyar sa.

Wannan kenan.

     ***********
Samuwar lafiyan muhammad da dawowarsu gida shine ya baiwa meenal daman komawa halayyar ta nada, a india sukan kwana a d'aki d'aya harma kusa dashi amma suna dawowa ranar farko shishi kad'ai ya kwana a d'akin sa, be damu da hakan ba sabida shi tunda ta damuwarta akan ciwon sa ta kula dashi ta gama masa komai, yasani ko baso aranta nasa to kuwa akwai Tausayi wanda yake fatan yakoma k'auna me tarin yawa.....

   Zaune yake a main parlor na gidan wanda acikinsa ne d'akunan gidan k'ofofinsu yake, yana jan carbi dake hannunsa idansa a lumshe yana tunanin yanayin dayakeji ajikinsa, harga Allah a 'yan kwanakin nan ya tsorata da abinda yake fitar wa a hancinsa, seyake fito da tsoka ja jajir a hancinsa kota mak'oshinsa, kwanajinsa 32 kenan da dawowa k'asar amma acikin kwana goman data wuce yana cikin tsoro me tsanani ya gama fitarda yin wata rayuwa me tsayi aransa ya sani yanayin dayakeji akwai illa kam, zuwa tai ta zauna a kujerar dake fuskantar tasa tana taunar cingom dake bakinta a hankali, k'amshin turaren ta ne ya sanar masa zuwanta  wannan ne ya sanya ya bud'e idanshi sosai ya diresu a kanta, hango tai yanda sukayi jajir wannan ne ya sanya da sauri ta taso ta zauna kusa dashi, hannunsa ta rik'o taji zafi rau ta kai d'ayan hannunta saman wuyansa nanma zafi sosai cike da damuwa ta furta 

"Yaa moh kaddai jikinne? Kaga idanka kuwa, menene yake damunka kuma?" K'ura mata ido yae na kusan 20 seconds kanya dire numfashi yace

"My meena so nakeyi ma in kwanta, amma kwata kwata na kasa motsa koda d'an yatsa nane, zazzab'in jikina har mamaki yake bani, ga ciwon kai sosai  dayake damuna" cikeda tausayi tace masa

"Sannu yaa muhammad, Inshaa Allahu zaka samu lafiya, dama akan fitar danace ma zanyi ne gidansu zulaiha shine na shirya da zanje amma bari kawai namata waya akan bakada lafiya se wani lokacin" Gyaran zamansa yae

"Jeki abinki my Meenal, ai sauki a wurin Allah yake, ki tayani naje na kwanta a d'akina amma dan Allah karki dad'e kinji" murmushi tae sannan ta mik'e tsaye ta tayashi ta rakashi har d'akin sa, tafita tabar gidan jikinta a sanyaye haka bata wuce awa d'aya ba ta dawo masa gidan, tasha mamakin rikicewar jikinsa lokaci d'aya, tayi masa kuka sosai yanda bemasan inda yake ba, Dr. Sa dayazo ma yayita complain daganan akaje dashi hoton huhunsa emergency, A gaskia babu wani ceto daza'a iya yiwa muhammad a wannan lokacin, hoton ya nuna duka huhunsa na b'angare biyu ya gama nunnugewa, shine ma yake fitarwa a hanci da mak'ogwaron sa, ya gama tashi aiki, wano zubin abubuwan se ajali ciwon nan daba'a tunanin hakan, likitan ya shiga rud'u kasancewar sa amininsa, zamansa asibiti ma b'ata lokacine da wannan ya mayar dasu gida yake bashi pain reliver  sabida babu wani abunyi ba'a dashen huhu bare a dasa masa, sosai muhammad yake da ban tausayi....

*Bayan kwana bakwai*

Kallon sa takeyi cikeda tausayi hannunta ya rik'o mata yana musmushin k'arfin hali ya furta

"Ameena ki sani bani da burin daya wucemun in rayu dake acikin aminci, amma banida yanda zanyi da rayuwata kasancewar inagani lokaci ne daya dace na komawa mahaliccina, bansan gaibuba kuma babu wanda yasan ranar mutuwarsa amma ninasan menakeji ajikina, numfashina kawai ya isa ya nunamun banida sauran lokaci, keda kanki kinajin yanda saukar sukuwar doki, tsakanina dake babu abinda kikamun tun aurena dake se biyayya da bautawa ciwona,abinda yakemun zafi shine yanda zan mutu ban sauke haqqinki daya rataya a wuyana ba, ki yafemun Ameena, banida k'arfin dazan iya miki komai a yanzu amma ki sani zan tafine da k'ishiruwan rashin samun ni'imar matar sunna ta, duk girman kare mutuncina danai da addinina ashe bazan rayu da ni'imar sab'anin jinsina ba har in mutu dan Allah ki yafemun Ameena, ina rok'on Alfarma ki dinga mun adu'a ki kuma sanyani a ranki, kike yawaita aikamun saqon ayyukan lada a madadi na ina jin tsoro Ameena, banida ayyukan alkhairin daze cikasamun mizanin daze rinjayi zunubaina se rahamar Allah, dayake shi me gafara ne, na yafe miki dukkanin abinda kika aikata agareni, Allahu ya baki ladan jinya, akwai wata ma alfarmar danakeso kimun my meenal" Mik'ewa tai tsaye tana kuka

"Idan kana ambatar kalmomin mutuwar nan wlhy ni zaka haukatar dani ne, kasani banason ka mutu bazan saurareka ba wlhy, zaka saka zuciyana ya fashe,yaa muhammada ka dena surutun nan haka kayi bacci kaji".......juyawa tai ya d'aga murya da k'yar yace

" My meenal kizo mana" bata waigo bama bare yasaka ran zata dawo, gashi cikin darene, sha biyu ta gota ma, haka yaeta kiranta amma bata waigo ba, tai tafiyarta tana ta rusar uban kuka........

************
    Wuraren k'arfe ukun dare wayanta ya soma ruri, dama ba bacci take ba, salla takeyi tanawa yaa moh adu'a Allah ya bashi lafiya me d'orewa, tana kuma adu'a idan mutuwace tafiye masa  Allah ya anshi ranshi cikin aminci...acikin sujjadar dataja da tsayi take jiwo rurin wayan  nata,taso ta share wayan nata amma setaji k'irjin ta na dokawa sosai, wannan ne ya sanya ta sallame sallan cikin sauri ta rarumi wayan nata, missed call uku kuma duk yusuf ne qanin muhammad, d'agawa tai jiki a mace ta kirashi back

"Meenal bud'emun gida ina waje" da mamaki tace

"Lapia dai?"

"Danla malama ki bud'e mun k'ofa, yayana baida lafiya kin barshi a d'aki shishi kad'ai sannan kice lapia, jinyarshi nazoyi" Da sauri ta ajiye wayan taje ta bud'e masa, suna zuwa k'ofar d'akin da muhammad yake yusuf ya shige ya danna key dole ta koma d'akin ta, D'are kan gadon yae yace bayan ya rarumo hannun d'an uwansa

"Yaa muhammad kodai nawa likitan ka wayane', murmushi yae me ciwo yace

"Babu wani bawa daya isa ragemun zogi da azabar danakeji a yanzu yusuf, ni nasan tawa ta k'are kuma se wani badai niba, abinda yasanya nai kiranka shine inaso kamun wani taimako" kallon sa yusuf yae jikinsa duk ya mace yace

"Haba yaya muhammad, ba kyaufa irin wannan abun, kasani ciwo bashi bane fa mutuwa, ka dena magana mana kagafa yanda numfashin ka ke d'aukewa" murmushi yae yace

"Yusuf so nakeyi idan Allah yamun rasuwa ka auri matata Ameena, kaga yarinyace k'arama kuma idan ba namiji na gidaba sekaga bazata ji dad'in zama da kowa ba sabida  halayenta akwai gyara, banaso taje inda zatasha wahala" kallon maganganun shirme yayansa keyi yake kallo, shidai so yakeyi kurin yae shiru da sauri ya d'aga masa kai....umarni ya masa akan yabashi biro da takarda acikin durowa, ya mik'o masa , kishingid'ar dashi yae ya zauna yae rubutu me yawa gaba da baya  sannan ya ninke ya kalli yusuf yace

"Ka bani ruwa ina jin qishiruwa, ka kuma je ka kiramun meenal"  kallonsa yae ya mik'e tsaye seda ya bude qofar yaje yakira Ameena sannan ya dawo ya ebo ruwan ya kawo masa, k'arb'a yae ya sha da kanshi, adaidai lokacin da Ameena ta shigo, tari ya tarnaqe sa yana gama shan ruwan da k'yar suka samu ya lafa, se kuka Ameena keyi,  ita kanta ta sare da wannan al'amarin

"Ameena ki kawomun lipton me zafi yunwa nakeji" tasani kwanan sa biyu bayacin komai dama cen ruwan tea kurun yake sha da sauri ta mik'e taje ta had'o masa yana kallon tea d'in yace

"Ameena nifa lipton nace idan kika bani tea da madara aciki wlh mutuwa zanyi"  taga alamar ya miyarda kalmar mutuwa kamar salati wannan ya sanya tace

"Kwana biyu bakaci bakasha yau kuma sena baka tea ba madara, hanjinka ze qara kwakwarewa dan Allah kasha wannan" girgiza kanshi

"Nasani mutuwa zanyi idan nasha banason madarar ne Ameena karki bani ki canjo" Dagewa tai akan dole ya karba yasha aikam yana gama shanyewa se tari komai seya birkice musu, kuka ta saka ba itaba ba yusuf ba, yana k'ok'arin kiran likita moh ya damk'o hannun Meena ya saka mata takardar hannunsa yace da k'yar

"Tun d'azu nakeso na gaya miki wata magana amma kika gudu Ameena, naso sosai in gaya miki wata maganar...se kuma tarin ya k'ara tasowa " kinga yanzu mutuwa zanyi kimun adu'a....

"Haba yaa muhammad, mesa kake ambatar mutuwa ne? Idan akan nace banasan kane kayi hakuri wlhy ina sanka fiye da tunanin ka ka tausayamun karka mutu kaji" murmushi yae me ciwo dukda azabar daya ke ciki, wanda yake nuni da tsantsan jin dad'in kalaman data furta sosai sannan yace

"Naso ace kin furtan kalaman nan tuni, amma ko yanzu naji dad'i sosai.... Zo nan my meenal matso kusa dani kiji" hannunshi d'aya ta k'ara kamowa

"Kaji yanda jikinka yae zafi sosai  dan Allah kadena magana numfashinka se sama sama yake save ur strenght plss yaa muhammad , kafin likitan Yazo" hannunsu dake had'e ya matse ya furta a hankali

"Me ikon bayarda numfashi ya buqashi abinsa my meenal, lokacinane yae Ameena bamuda yanda zamuyi, kimun adu'a kinji" Tama kasa magana se kuka takeyi itad a yusuf

"Yaa muhammad yaya kake mun magana a baud'e ne wlhy yau na soma fahimtar kalaman ka, dan Allah karka ce zaka mutu"

"My meenal wlhy tsoro nakeji, tsoron daban tab'a jin irinsa ba nima banaso in mutu kinji" kasa magana tayi suna ji suna gani haka yasoma yin magana basajin meyake cewa har yau shiru lokaci d'aya hannunsa ya sake komai najikinsa yadena motsi mutuwace lokacine, dolece mutuwa kuma ya mutun....kasa fahimtar komai tayi har sanda yusuf ya k'walla k'ara...a hakan yakira waya tanata kuka har aka fita dashi, seda safe  ma tukunna aka shirya shi zuwa makwancinsa.......!!!!!!

****************
    *Dawowa cikin labarin*

Tunda aka mata alluran bacci ba ita ta farka ba se washe gari da asuba, lokacin kam har muhammad yafi awanni goma sha biyar a makwancinsa, a razane ta farka cikin tsakanin kuka.....

Mom Nu'aiym

המשך קריאה

You'll Also Like

333K 19.3K 41
You live in a different time zone Think I know what this is It's just the time's wrong
601K 1K 22
Smexy One shots😘 Got deleted twice 3rd times a charm🤦🏻‍♀️😭
5.3M 46.3K 57
Welcome to The Wattpad HQ Community Happenings story! We are so glad you're part of our global community. This is the place for readers and writers...
36.8K 2.9K 60
Hamza Siddiqui- The new student in the school, whose smile made every girl lose her heart but he is a cold , ruthless and rude demeanor person Fiza...