A SIMPLE DARE (WASA DA SO)

Door marteybee

431 7 16

Meer

new book
Page 2
Page 3
Page 4
Page 5
Page 7
Page 8
Page 9
Page ten
Page 11
Page 12
Page 13
Page 14
Page 15
Page 16
Page 17
Page 18
Page 19
Page 20/21
Page22/23
Page 24/25

Page 6

10 1 0
Door marteybee

✨✨
        A
SIMPLE

DARE

                              ✨✨

(WASA DA SO)

WRITTEN AND STORY
                BY
NERNAH MARYAM
          (MEEMARH)

 
             Kofa a bude take ga duk me son yin joining group dina😌,Amman Hajiya don Allah in kin san ba yin comment ko karanta littafi na zai kawo ki ba I beg you in the name of Allah kiyi zaman ki ba sai kin shigo ba!!haka zalika wanann group din na mata ne zalla don Allah Maza should stay away from my group👏

       My What's app group link👇🏻

           https://chat.whatsapp.com/EUrVVaKJnIBDTlQsxurZv0

Bismillahi Rahmanin Raheem............

(    In the name of Allah the most beneficient,the most merciful)

 
  Kofa a bude ta ke ga duk wani me good quality product da ya ke son Advertising ɗin shi,as Kaya masu kyau,da inganci (TALLAH) should contact me via :
                              08100046388

       Page 6️⃣

    TALLA!!TALLA!!TALLA!!!

       https://chat.whatsapp.com/ImtxMSS1tuSKqvBpPqc03P

Assalamu'alaikum sisters🤗
KAMSHI* mace Mai kima, mace Mai daraja, mace Mai izza, mace Mai aji itace tasan darajan kamshi, if your perfume is not unique hajiyata you're just using ordinary air freshener🤣, hajiyata ko nawa Zaki kashe indai a turare ne baki Fadi ba😘 matan da suka gane suka San yanda zasu kankaro da martabar su, suke amfani da turare, a *BAKHOOR BY FAIXY* Zaki Sami Main chic, Bachelor, Husband snatcher, Her royal sexiness, Mysterious girl, Pleasure, Boovilous, White khumra, Maroon khumra, Black khumra, Hair perfume, Turaren wanka, Turaren  wuta, Turaren tsuguno, Turaren mopping,Turaren carpet Shu'umat khumra,and more, yar uwa kar kibari abaki lbr, (wholesale and retail) WhatsApp 09067621681, siyan na gari Maida kudi gida🥳

Instagram @Bakhoor_by_faixy

******************************

"Goofy angel!!"shine abinda Zuhra ta iya fadi bayan ta zuba wa Sabeeha idanu na mintuna,ita din ma Sabeehar ita din take kallo domin duk wani iya tunani tayi amman ta kasa samun amsan da take so a cikin zuciyar ta, "Zuhra what is this guy up to ne??For God sake i can't get to understand him at all,why on earth is he paying for my candies?"ta kare a raunane.

Hannun ta Zuhran ta riko sanann cikin sanyin murya tace "ni kai na Sabeeha Wlhy ban ma san me zan fara tunani ba,as in kai na baki daya ya kulle na rasa gane wanann irin abun,da farko ya taimake ki gurin yi wa Mal Jirbril magana,yeah for that I can think maybe saboda Humanity yayi maybe ya ga abunda ya faru da ya zo wuce wa,but why on earth zai na aikowa ana siye alawar madaran ki harda baki kudi extra?"

"Hmm Zuhra Wlhy nima nan abunda nake tunani ke nan,in har zan tuna ban san shi be sanni ba,besides da muka hadu ma ba haduwar mutunci muka yi ba balle ace sabida haka ne yake taimako na,dole akwai dalilin shi na yin hakan,coz ba ni kadai bace mace ke ma mace ce in za a ce mata yake taimako ya ci ace ke ma ya taimaka miki,why on earth upon all matan BUK ni Sabeeha zai ware yana kyautata wa,and sanin kan ki ne ke da kan ki kika ce mun FIK ya ke ko wa baya taba barin abu ya tafi freely ina ta tunani kullum ta wani way zai biyo ta daukan revenge din shi don kin ce da ni sam baya mantuwa haka ma yafiya but why yake kyautata mun instead ya dauki fansan sa?"

"Nima dai abunda nake gani ke nan,Sabeeha Wlhy a yanda nake jin labarin yan Rocket gang barin ma FIK wlhh ko jinjiri ne ya shiga harkan su ba barin sa za suyi ba,by now nima na dauka Wlhy har yayi taking revenge din shi ya gama,amman sam ban gane inda ya dosa ba,to ko dai ya mance ne?Ko kuma ya yafe miki ne?Domin hanyar da ya dauko sam ba ta nuna alamun daukan fansa bane"

"Zuhra ke nan,ke fa da kan ki kike sanar da ni Waye FIK kullum,sam ba irin mutane da Allah yayi su da hakuri da yafiya bane,Wlhy ko kaffara ba zan yi ba FIK be yafe mun abun da nayi musu ba,and I never regret what I did because kan daidai nake,ya sanya har ya na kasa ba su hakuri kamar yanda Umma tace,dan numfashi ta sauke sanann tace ko ma dai miye yau za a yi ta ta kare don sai mun yi face to face da shi,coz so nake muyi magana ban ga dalilin yi mun abubuwan da yake yi ba"

"Sabeeha kina ganin facing din nashi shine best solution?What if trap suka hada mana,so suke mu kawo musu kan mu su ci mana mutunci fa?"dan murmushi Sabeeha tayi sannan tace "Zuhra Besty ta me uwar tsoron masifa,don't worry okay jiki na be bani trap suka hada mana ba,koma trap din ne I got you Goofy angel so babu amfanin tsorata,come let's go and face the Rocket gang members and end all this nonsense for good"

"Sabeeha wlhh in wani abu ya faru ni da ke gaba har jikokin mu,kuma wlhh sai na kwana ina ja miki Allah ya isa", "ke dai Zuhra anyi yar iska wlhy,dallah wuce mu tafi a irin tsoron nan naki ake cutar da ke kullum ana yi miki kallon wawiya,nothing will happen okay just trust me babe I got you I won't let anything bad ya same ki"da haka ta samu ta shawo kan Zuhran don fir cewa tayi bata zuwa don tsoro take ji,saida Zuhra ta tambayi wani kan ko ya ga yan Rocket gang?Inda yake sanar da ita yanzun nan ya ga wucewar su a mota,sun nufi Cafeteria,godiya tayi mishi sannan ta ja hannun Sabeeha suka nufi Cafeteria din.

Zaune suke duk su biyar din,inda abinci ne da lemuka a gaban kowannan su duk cikin nutsuwa suke cin abincin su banda FIK da ya zuba wa guri daya idanu,Nabeel ne ya tabo shi sanann yace "Gee how far?Ko dai abincin be ma dadi bane a canzo maka"

Kai ya girgiza sanann ya amsa da "Ni fa a koshe ma nake,am just waiting for this Sadeeq boy ya dawo da robar candies din yarinyar nan"idanu Nabeel ya zaro sanann yace "Faizan are you in your normal senses kuwa?So kake kace da ni kan wannan stupid candies din ka ki cin abinci,so you prefer eating them akan wanann abinci me tsadar da muka yi order"

"Man but ba laifin FIK bane yasin the girl tana da magic hand ni kaina na kosa Sadeeq ya dawo na samu na sha don ba karya alawar madaran ta is one of the best"Jawad ya kare yana murmushi.

Tsaki Nabeel ya ja sanann yace "wlhh kuwa indai da gaske kuke maganar nan tabbas da sai na muku hauka ba dai mu za ku zubar wa da mutunci ba,Farouq kana jin wani maganar banza da wanann wawayen ke yi,nan gaba duk su biyun I think fadawa soyayyan ta za suyi"ya kare a hasale.

Kafadun shi FIK ya dan buga sanann yace "sip some water ko za ka ji sanyi a ranka,Beel dadi na da kai gaggawa Wlhy sam baka da hakuri,wai tunanin ka akan na sha wancan banzayen kayan Milk din nata ne har na kasa cin abinci?Funny you!!ai I think Beel don yanda ka tsani yarinyar nan to a baya na ne,coz har yau na kasa mance marin da ta sauke mun a face dina,Mom da kan ta saida ta tambayan satin hannun Waye a face dina,akan dole nayi creating excuses ban sanar da ita ba,and kake tunani so easily zan manta komai har na fada son ta?Naahhh you are mistaken that will never happen,not in this life even in my next life ba zan taba son wancan ugly bitch din yarinyar ba me suffar mayyu,so chill okay am just so curious ne in san yanda suka yi da ita,coz na san yau duk yanda aka yi sai ta so sannin waye ke siye candies din ta harda bata extra kudi haka,and I told Sadiq ya fada mata ni ne,na san halin ta sarai she will go around looking for me like a fool just to show how brave she is,and I will be here patiently waiting for her like a king,daga sanda ta zo wasan zai fara,am gonna take my first step today,so you guys should seat back and watch kawai"ya kare yana karkada kafa.

Sai a lokacin Nabeel ya sauke wata wawiyar ajiyar zuciya tare da sakin murmushi,domin kaf fadin duniyar nan baya jin akwai wanda ya tsana a yanzu irin Sabeeha da wanann shegiyar kawar nata,sam idea din Faizan yayi dating din ta na 3 months tare da breaking heart din ta at the end be kwanta masa a rai ba,domin in ba deceiving kan su suke son yi ba,Sabeeha is damn pretty 🤩 what if daga WASA DA SO abokin na shi ya fada tarkon Soyayya da gaske fa,shike nan revenge din su ya bi ruwa,ya sanya tun farko be so wanann idea din ba ganin ya matsa ya sa ya amince,sai yanzu ya dan samu kwanciyar hankali ji da yayi FIK ya sanar da shi babu abinda zai yi da Sabeehar ya kuma san FIK sarai baya taba fada be cika ba,duk cikin su babu wanda ke yin magana biyu,hakan ne ya sanya shi sakan murmushi tare da bude baki don yin magana ya ji muryan Akram ya katse shi.

"FIK kamar me alawar madaran mu nake hangowa tare da baby elephant suna tahowa inda muke"dan gefen lip din shi na kasa ya tsotsa a hankali kamar wanda baya son magana sannan yace "let's the game begin"duk zama suka gyara kowa ya hade rai tare da jiran isowar Sabeeha don jin da me take tafe.

Saida ta gama kare musu kallo cike da tsana bayan sun iso inda suke da Zuhra sanann ta bude baki da kyar ta ce "Assalamu Alaikum"ta fada ne kawai don sauke hakkin musulinci domin ta san su sarai ba amsa ta za su yi ba kila ma su kuma zagin ta kalan na wancan ranar,amman hakan sam be dame ta ba,domin ko ba su amsa ba akwai Mala'ikun Rahma da za su amsa,saidai da mamaki ta tsinkayo deep husky voice din FIK ya amsa da fadin "Wa'alaiki Assalam wa Rahmatul Lahi Wa Barkatuhu"idanu ta dan zaro a hankali don sam bata yi expecting jin hakan ba,hakan ya sanya FIk sakin murmushi wanda ya yi matukar qawata fuskan shi,sannan ya mike a hankali tare da takowa dan da inda take

"Hello Barbie doll!!kinda surprise na amsa miki sallamar ki ko?C'mon miye abun zaro idanu kamar wani ni ba Muslim ba,guys what are waiting for da baku amsa sallamar ta ba ko ba ku ji Amincin Allah ta nema muku ba"ya kare yana kallon su Nabeel a tare duk suka hada baki tare da amsa sallaman,sanann ya ja chair "Have a seat Mi lady"ya fada cikin tattausan murya,juyawa tayi ta kalli Zuhra da ta saki baki da hanci akan face din FIK sanann ta juyo ta kalle shi.

"I don't think akwai bukatar bani seat in zauna da kayi"da sauri ya katse ta da fadin "of course there is,na san you might be tired trekking from your department to here dole ki gaji Ai ko?Now have a seat let me get you something soft to drink and maybe something light to eat,don da alamun kina bukata in ya so in kin gama then we can talk"

Kallon shi take kan yi har yanzu ba tare da kuma
ta zauna a chair din ba,saida ya kuma maimata "C'mon Barbie doll seat down pls"ya kare kamar me shirin kuka,ba ita ba har su Nabeel kan su mamaki ne ya gama kashe su,ko wuka za a daura a wuyar su a tambaye su daman FIk can be this soft and over romantic to za su ce karya ne,coz actually this is the first time da suke ganin haka ko in ce suke ganin wannan side din na shi,the greatest FAIZAAN ISMAIL KWAIRANGA ne wai ke offering mace seat harda rokon ta kan ta zauna,dan dariya Nabeel yayi a ran shi sanann yace wa su Jawad "Shege Gee ku duba ku ga yanda yake ta wani kakkarya wuya da murya kamar wani chicken da ke shirin shiga ruwan zafi"duk dariya suka kwashe da shi a tare.

Saida ta dauki mintuna tana kan kallon shi,sanann cikin sassanyar muryan ta ta iya budan baki tace "can you drop the act?Wa kake son fooling you pretending to be nice to me,do you think am a fool da zan dauki wannan play din da ka gama displaying yanzun nan?Ko da ya ke ba abunda ya kawo ni ba ke nan so save your chair to yourself you might use it later"

Murmushi ya sakar mata sanann ya daga mata gira "go on Barbie doll me kike son fada mun am all ears"harara ta watsa mishi "can you stop calling me Barbie doll!!and for Allah sake why do you keep on stalking on me?"

Da sauri ya katse ta da fadin "but I never did that"harara ta watsa masa sanann tace "of course you did,look you have helped me out with my assignment issue and am so so grateful for that,but I don't see any reason da za ka na siye kayan madara na kullum,let's assume siye wan ma kake I have nothing against that,but zuciya ta bata kwanta da extra money da kake bada wa kullum ba,hauka ne ma ace within 3 days over 60k for just abun 7k that is to much,besides me and you ain't friends balle nace you are doing that for our friendship"da sauri ya katse ta da fadin "trust me I mean no harm🥹and we can be friends bro,so I don't see anything bad akan abun da nayi"

Wani hararan ta kuma maka masa "that one mentality na yaran masu kudi na daukan duk abunda suka so yi shine daidai ba zai taba barin kan ku ba,FUK or FIK kake or whatsoever!!I don't care about kana meaning harm to me ko aa,and I don't like you balle har na yarda nayi friendship da kai,and I don't like the way kake son shiga rayuwa ta can you maintain our distance and stay away from me coz I don't like anything to do with someone like you"a harzuge Nabeel ya taso yayi kan ta "Keeee shegiya yar talakawa jikar tsiya har kin yi isar da za ki fada wa FIK magana dan uban ki"a zafafe ta juyo don ganin wani mara mutuncin ne ke fada mata magana haka,sai ta ji muryan FIK caraf yana fadin

"Beel me and you go get issues in har ka sake raising voice din ka akan ta,and this should be your last and first da za ka kuma insulting din ta ko da kuwa a bayan idanun ta ne,miye ta fada ba daidai ba,bayan abunda muka mata in wata ce ma da yanzu ta cika complain a gun mu gurin yan sanda but saboda soft and kind heart din ta she let go of komai,and maganar Gaskiya she has all rights to be curious about all this damn things coz duniyar yanzu babu tsaro ko kadan so kul kar ka kuma maimata something like this again in the future"

Daga Nabeel har Sabeeha da Zuhra baki duk suka sake cike da dumbin mamaki suna kallon FIK,saidai ya sake mata murmushi sanann yace "pardon my friend's behavior Beel is kind of wired at times so as I said Barbie doll na ji dadi sosai and you are the first girl ta taba fuskanta na face to face to talk to me in my entire life,I think akwai Magic din da kika yi performing akai na"

Dan tsaki ta ja sanann tace "Allah sauwaka for someone like you na je nayi wasting Duniya and Akira na gurin yi maka black magic,duk wanann kai ka san su,all I know is that you should stay away from me domin me and you bana fatan wani abu ma
Ya kara hada mu,jaka ta budi tare da ciro kudaden shi,hannu ta mika gaba sanann tace take back your money bana bukatar shi Alhamdulilah am okay with the little da nake da"a zafafe Nabeel ya bude baki zai yi magana ko me ya tuna kuma sai na ga yayi shiru.

"Zuhra!"FIK ya kira sunan ta a sanyaye kamar ba shi ba,da sauri ta dago ta kalle shi,sanann yace "you are Zuhra right?"kai ta daga mishi alamun eh domin tongue din ta ji take sun yi mata nauyi,ji tayi yace "go on and talk to Miss Grumpy akan cewa babu kyau maida hannun kyauta baya,ni actually kyauta na bata just to make up for what we did to you both,and I already know tunda na san kuna da ilimi sosai maida hannun kyauta aikin shedan ne ake cewa so talk to her na ji ko she won't ever talk to me again let her hold back the money and ba wai na bata don na raina nata arzikin bane kawai ina jin dadin candies din ta ne sosai,so she should consider this little gift from her number one huge fan"ya kare yana murza ring din hannun shi

Da sauri Zuhra tace "Ke ko Goofy angel miye kike yi haka don Allah"kasa kasa tayi maganan inda Sabeeha ce kawai za ta jiyo ta,harara ta maka mata sannan tace "Zuhra ya karbi kudin shi bana son duk wani abunda ya shafe shi eheee"

"Aa Sabeeha baki ji me ya ce bane maida hannun kyauta babu kyau,ko Manzon mu yana karban kyauta Sadaka ce baya karba,so ke wacece da za ki maida hannun kyauta baya,don Allah ki bari"

"Yauwa Fada mata dai maida hannun kyauta baya babu kyau,and trust me with pure intentions na bada kyautar nan so ba zan ji dadi ba in ta dawo mun da shi"

Murmushi Zuhra tayi masa sanann tace "mun gode FIK Allah ya kara budi",da Ameen ya amsa shima yana murmushin tsaki Sabeeha ta ja kasa kasa sannn tace "ki wuce mu tafi tunda ke dai ba kawar kirki bace,and back to you na fada maka to stay away from
me from now on ko kuma nayi maka abunda ba zai maka dadi ba"daga haka ta ja hannun Zuhra suka yi wucewar su,da kallon tsana FIK ya bi bayan su,saida ya ga wucewar su sanann yace da Akram ya mika masa bottle water da hand wash saida ya wanke hannun sa tsaf sanann ya shafa Sanitizer tare da goge face din shi sanann ya koma ya zauna yana jin kamar ya janyo Sabeeha ya rufe ya da mugun duka

"Geee Wlhy you are just going to waste your time on this little silly plan of yours amman wanann rude arrogant yarinyar bana jin za k iya shawo kanta Wlhy,tana da mugun taurin ki tare da tsaurin idanu,dan uban ta shegiya yar talakawa wai har ta iya maido kudaden da ka bata,a wanann marran ta hada over 100k within 3 days kar ka mance kullum 50k kake bada wa a bata,amman har ta iya dawo wa da shi har wai ana rokon ta ta rike tana wani tirjewa sai kace ko saida ta da wanann shegiyar kawar nata aka yi za a samu over 100k"Farouq ya kare rai a bace

Dariya FIK da su Nabeel duk suka fashe da shi jin statement din shi na karshe sanann FAIZAAN yace "kana shirun ka Gee haba kamar ba ni ba Wlhy tallahi ban taba shiga DARE kuma na fadi ba,balle wanann ma abinda na ke so Nabeel yace zai bani,ba dai Sabeeha ce ko Nafeesa!!just relax all and watch wlhh 3 months ba zai wuce ba sai na sanya da bakin ta ta fada mun ba za ta iya rayuwa babu ni ba,dallah duk ku Kyalle burgan karya da take yi na san irin su,shegen fadin kai ne kawai,just don't worry I swear to my living God I will break her Ego,I will make sure to give her the taste of her on medicine,I will break her down daga wanann ranar bakin tsiwa zai mutu,hanzarin me kuke all?FIK ne fa Ai ban taba fada ban cika ba,so ku gama cin abincin ku mu tafi filin polo"daga haka ya ja kwantar da kan shi jikin kujera tare da lumshe idanun shi don tunanin next step din shi,ya dauka a yanda ake cikin matsi da yunwar nan cikin sauri zai siye zuciyar ta da kudi cikin sauki,amman ya ga alamun yarinyar ba me son abun duniya bane,dole ya canza takun shi domin be hango kan shi ma ya fadi ba,wallahi ko tana so ko bata so sai ta fada son shi,sunan shi da Nabeel ya kira ne hakan ya tabbatar mishi da magana zai mishi ya sanya shi saurin katse shi da fadin

"Not now Beel allow me to think straight just finish up your food"hakan ya sanya duk suka ja bakin su suka yi shiru tare da cigaba da cin abincin su.

***********************

Da sallama su Sabeeha suka shiga gidan su Zuhra,inda suka tarar da Baban Zuhra tsaye kan Maman su yana ta auna mata zagi,tare da shirfa mata buhun masifa kamar wanda zai rufe ta da duka,inda kan ta na kasa banda hakuri babu abinda take bashi,inda kuwa kamar dada tunzura shi take sai fadi yake

"Ba zai yu ba wlhh za ki bar gida na,akan me ya sa ma,ni da gida na amman ba za a bani abinci na ci na koshi ba saboda mugunta da bakin hali irin naki,ace har yanzu ban ga abincin karyawa ba to miye amfanin cigaba da zama da ke"cikin kuka tace

"Haba Mal Wlhy in har baka yaba mun cikin gidan nan ba to ba za ka tsine mun ba,haka yau muka tashi sisi babu a guri na yaran ma ban samu komai gurin su ba,ga duba su Faisal tun dazu ko motsi basu iya yi domin tun jiya da rana rabon su da su ci abinci,amman ba shine damuwar ka ba kai dai kan ka kawai ka sani,Hakkin ciyar wan nan a kan ka yake amman ka sakar mun ragamar gidan nan komai ni nake yin shi sanann a hakan ma ban tsira ba?Ya kake son nayi sabida Allah duk dan jarin nawa ya bi ya kare"saukan marin da ta ji ne ya sanya ta yin difff

"Keeee dan uwar ki har ni za ki yi wa gori?Amman matar nan sam ke ba matar arziki bane,ke dai ba matar rufin asiri bace,ba bautar aure kike ba?Ko ba Aljanar ki kike nema ba,kar ki ga don yaran da kika tara kiyi tunanin zan raga miki Wlhy zan iya kwabewa nayi miki bugun Bura uba"da sauri Zuhra ta nufi inda yake a zafafe tace "Haba Abba tsakani da Allah wanann wani irin rayuwa ne kake gudanar wa a cikin gidan nan??A gaban su Faisal ka tsaya kana zagi tare da dukan Mahaifiyar mu?duk abunda matar nan take yi kace ba matar rufin asiri bace?ko bautar Auran haka ake yin ta?Ai In bata ci darajar aure da zama uwar yaran ka ba Ai ta ci darajar matar da ke ciyar da kai da yaran ka abinci"

Da sauri yace "Ke Zuhra dan uban ki ni kike maida wa magana son ran ki?"ya kare yana nufo ta a harzuke don rufe ta da duka,da sauri Mama ta janyo Zuhran tare da boye ta a bayan ta domin in ta bar ta sai ya karya mata yarinya ba damuwar da bane kuma ita zai bari da jinya.

"Malam don Allah kayi hakuri kar ka dauki abinda Zuhra tace har zuciya ka san halin yaran yanzu wani lokaci magana kawai suke ba tare da suna sanin abinda suke cewa ba"

"Ke dallah rufa mun baki munafukan banza munafukan wofi,Wlhy duk abinda yaran nan ke yi a gidan nan ke ke daure musu gindi and Wlhy gaba daya kar ku fasa ku cigaba da yi mun duk iskancin da kuka dama duk uban ku zan ci shege mara sa mutunci"ya kare a zafafe tare da daukan buta yana me shigewa bandaki yana cigaba da mita kamar bakin shi zai fado.

Kai Maman Zuhra ta girgiza sannan tace "Zuhra!!me yasa sam kin kasa sanya wa kan ki hakuri ne?Kin san halin Abban ku sarai akan wani dalili za kina tan ka shi?In da ya buge ki fa?Duk abinda za kuyi kuna tunanin kaina fa yake dawo wa daga karshe sanann Zuhra duk lalacewar shi kar ki mance Mahaifin ki ne fa,shi ya haife ki,inda nake da hakki akan ku kuyi mun biyayya haka shima akwai hakki akan shi dole kuyi mishi"cikin zubda hawaye Zuhra tace "na sani Mama na sani,Wlhy wani lokacin zuciya ta ne take gaza daukan abubuwan da yake miki,Mama ana aure ne don samun farin ciki da kwanciyar hankali ba irin yanda Abba yake miki ba,Miji shine Allah ya danka wa amanar mata da yaran shi a wuyan shi,amman Mama fada mun hakki guda da yake saukarwa na ki ko namu?"Ta tambayi tana kuka sosai

Dafa ta Sabeeha tayi a raunane tace "ya isa Habeebty daina kukan haka nan don Allah kar kan ki yayi ciwo,duk tsanani akwai Allah and maganar Mama haka ne,sam bamu da daman hukunta iyayen mu ko da kuwa me za suyi mana kamar yanda ba mu da ikon hukunta mazajen mu in sun mana laifi,don Allah ya riga da ya daura su sama da mu,Abba Mahaifin ki ne,kamar yanda ya ke Mijin Mama so duk ku biyun baku da ikon hukunta shi,kuyi ta hakuri kuna fada wa Allah in sha Allah komai zai zo da sauki"

Murmushi Mama tayi sanann tace "Allah ubangiji yayi miki Albarka Sabeehatu Allah ya kara mana hakuri baki daya,kiyi ta tausan mutuniyar ta ki in sha Allah komai zai wuce,Wlhy da badun ku ba da tuni na dade da fice wa a gidan shi,domin ban ga abunda nake tsinta ba,zaman ku nake Zuhra don Allah in ba za kina karfafa ni ba don Allah kar ki zamo weakness dina"ta kare tana goge kwalla,rungume ta duk su biyun suka yi suna me goge mata hawaye kafin Zuhra tace "Mama abunda ke kashe 99 percent of mata a yanzu ke nan,mace bata jin dadi ko in ce bata san dadin zaman aure ba amman kika taba ta sai ki ji tace wai zaman yaran ta take yi,wanda Wlhy har a musulunce ma haramun ne babu kyau,aure ana yin shi ne don samun farin ciki da kwanciyar hankali,sanann bauta ce kuma wani tsani ce na shiga aljanna daga inda mace ta fara zaman yaran ta to fa ke nan ta aje wanann ibadar da bautar da ya kawo ta,kwata kwata abun is not making sense in har ba za ki iya hakurin zama ba let's yourself out kar ki kashe kan ki a sunan zaman yara"baki Sabeeha tayi saurin rufe mata kasa kasa tace da ita "watch your tongue silly"murmushi kawai Maman tayi sanann ta girgiza kan ta,Zuhra har yanzu akwai yarinta a tattare da ita ba lalle ne ta fahimci abunda ke faruwa ba,yanzu in ta fita daga gidan shi da uban yaran nan ina za ta fara nufa?hakan ya sanya ta saurin kauda tunanin ma ta hanyar bude labulan parlor din ta ta shiga sannan tace "Sabeehatu ku shigo ku zauna,ya Umman naki take?"

"Tana lafiya Mama ta ma ce na gaida ki", "to Masha Allah Ubangiji ya kara mana lafiya baki daya,na kwana biyu ma ban je ba ita ma bata zo ba"

"Eh Wlhy Mama kuma kullum tana wakan za ta zo za ta zo amman Allah be yi ba", "Ke kam bari ai abubuwan ne yanzu duk sai a hankali,in baka kai ranka nesa ba ba za ka iya zumunci ba,in kin koma ki ce ina gaida ta kuma in sha Allah zan dai leko ku"ta kare tana kallon Zuhra da ke ta kumbure kumburen fuska,ita dariya ma ta so bata hakan ya sanya ta yi kamar bata ma san tana yi ba.

Jaka Sabeeha ta bude tare da irgo 10k daga cikin kudaden da FIK ya bata ta aje kusa da Umma sanann tace "Mama ga wanann babu yawa kudin da muke boye wa ne ni da Goofy angel"idanu Mama ta zaro da ta gama irga kudin ta ga 10k ne

"Sabeehatu haba haba Ai tayi yawa,in na karbe wanann duka ku kuma yan makaranta kuyi Yaya ke nan?ai in ba mu baku ba ba ma karbe wanda kuka samo ba,maza karba"ta kare tana mika mata kudin,kamar wanda aka jefo shi dakin sai ganin shi suka yi kan su yana zare idanu,kafin su kai ga magana har ya sanya hannu ya fauce kudin a hannun Mama

"Ahh Sabeehatu harda wahala haka,Allah yayi albarka ya jikan Uthman"ya kare yana jefa kudin aljihun shi,da sauri Mama tace "Haba Malam!!Haba Malam wanann abunda kake sam be da dace ba,saboda Allah yaran nan yan makaranta kai ba abun kunya bane ka karbi abun hannun su"tsaki ya ja dogo kamar wani karamin yaro sannan yayi fice war shi daga dakin ko kallo bata ishe shi ba,in ran Zuhra yayi dubu to duk sun baci ganin haka ne ya sanya Sabeeha saurin riko hannun ta,tana mamakin Zuhra sosai ta san sarai yarinyar akwai hakuri tsoro da sanyin hali amman ta rasa gane irin kiyayar da take yi wa Mahaifin ta,abun har mamaki yake bata inda ta ke caka masa maganganu wani lokacin,jakar ta kuma bude wa tare da kara irga wasu dubu goman ta kuma bawa Maman,inda da kyar ta samu ta karba,haka tana hawayen farin ciki tayi ta sanya musu albarka tare da adduoin gamawa lafiya har saida Sabeehar ta ji kunya ma,a take kuwa ta mike ta fito tare da kiran Faisal don ya je yayo musu chefanan abincin rana,zuciyar ta kalla don ta kada gabas da yamma ta rasa inda za ta samo bashin kudi ma balle kyauta sai gashi har gida Allah ya kawo mata,lalle ta yarda haihuwa akwai rana.

Rungume Sabeeha Zuhra tayi kam,tana hawaye domin ko shawara da ita kan za ta baiwa Maman ta kudi bata yi ba,kawai ta dai ce su taho gidan su ta gaida Mama

"Goofy angel Allah ya miki albarka ya kara budi,yanda kika cire mu a damuwa yau Allah ya kau miki da duk wasu damuwowin ki,I love you 3000 times"

Kan ta Sabeeha ta kwade sanann tace "don't you think that's too much,silly girl babu komai stop thanking me and I love you more,so wipe off your tears ki tashi muyi salla ki raka ni,and Wlhy Zuhra za mu samu mugun matsala da ke in kina maida wa Abba magana,ke ki ma gode kina ganin Abban duk lallacewar shi da kike gani,ni da ban ma san ya ma kalan Mahaifi na yake ba,zan so ko ya yake yana tare da ni Ai da na ji dadi ko,don Allah Zuhra ki na sanin yanda za ki na wa su Mama da Abba magana,domin kananun abubuwan da muke wa iyaye muke raina su Wlhy Allah baya yafe mana,sai ya daukar musu fansa domin iyaye ba abun wasa bane"

"In sha Allah Goofy angel daga yau na daina,kuma in ya dawo anjima zan je na bashi hakuri,Allah ya yafe mana ya kuma ba mu ikon yi musu biyayya"

"Ameen thuma Ameen shi biyayya wa iyaye wajibi ne amman fa sai an daure an kuma kai zuciya nesa,ya sanya Mala'ika da kan shi ya zo gurin Manzon mu yace Allah ya tsine wa duk wanda ya taso ya samu iyayen shi duk biyu ko guda a raye be kuma yi abunda zai sanya ya samu kofar Aljannar shi ba ta dalilin su,Annabi kuma ya amsa da Ameen,saboda kin san akwai Aljannar da akan shige ta saboda kyautata wa iyaye,aka ce in har kika taso kika samu iyayen ki a raye to kina da key din Aljanna haka zalika kina da na wuta sai wanda kika zaba kika ga daman shiga,so pls take note okay bana son me kama da haka ya kara faruwa don Allah"

A sanyaye Zuhra tace "Goofy angel na gode sosai Wlhy Gaskiya zama da mutanan kirki na sanya ka zamo na kirki kaima,Allah ya kara mana hakuri da tsoron Allah and ba zan taba daina gode wa Allah ba da ya azurta ni da Aminiya irin ki,you are such a rare gem my love Allah ya bar mu tare"murmushi Sabeeha tayi tare da mike wa "Ameen thuma Ameen yanzu dai mu tafi daki muyi salla muka tsaya magana sai lokaci ya kure"

Ko da suka ida babu yanda Mama bata yi ba kan Sabeeha ta tsaya ta ci abinci amman tace aa za ta tafi gida ta bar Umma ita kadai,da haka suka yi sallama Mama nayi ta saka mata albarka sanann suka fito da Zuhra don raka ta

"Goofy angel Yauwa na tuna"hararan ta Sabeeha tayi sanann tace "to uwar tune tune yanzu kuma
me kike tuna"duk dariya suka saka sannnan Zuhra tace "this time around am being serious wlhy,Sabeeha don't you think FIK ya fada Son ki ne"wani irin rass ta ji a kirjin ta har saida ta sa hannu ta dafe saitin zuciyar ta,sanann ta tsaya cak tare da kallon Zuhran kafin ta iya furta kalman

"Inalilhi wa ina ilaihi raju'un ke Zuhra!!da hankalin ki kuwa,ya sanya kullum nake ce miki you should think before speaking,wani irin So don Allah ana zaune kalau"

"Allah Sabeeha da gaske nake in ba son ki ba to ni Wlhy ban gane abubuwan da yake yin nan ba,just imagine kudaden da ya bar miki yau he was even pleading with you kan ki rike kudaden after marin da kika yi mishi,wlhy tunda nake ban taba jin ance ga macen da FIK ya ce wa pls ba a rayuwar shi,just ki tuno inda ya ke magana da ke dazu very calmly and ki tuno inda ya shigar miki tare da saurin dakatar da Nabeel daga zagin ki da yake kokarin yi,ki tuno"

Da sauri Sabeeha tace "just keep quite for Allah sake Zuhra bana son jin komai,ashe ke har yanzu da sauran ki,don kawai yayi behaving so nicely da ni na yan mintoci sai ya nuna alamun so na yake yi?haka aka ce miki shi soyayyar ta ke"

Da sauri ita ma tace "me kika sani game da soyayya Goofy angel?Abunda har yau ba yin ta kika taba yi ba,and Wlhy ni dai zan iya ce wa alamun da FIK ya nuna yau is like son ki yake"

"Zuhra!!ke baki da wani zance da ta wuce na Soyayya!!to ni dai Wlhy ki raba kan ki kuma ki raba ni,ko hauka nake taya ma zan yarda da abunda kike fada,ke ma da za ki taimaki kan ki da kin farka daga wannnan munanniyar mafarkin da kike yi domin abune da ba zai taba faru wa"da sauri tace "amman Sabeeha"

Itama katse ta tayi da fadin "no more amma don Allah this chapter is over,babu abinda za muyi da juna daga ni har shi"baki Zuhra ta cuno sannan tace "Wlhy da hakan zai faru da na fi kowa farin ciki,OMG cute babies alert"

Tsaki Sabeeha ta ja "sai kiyi ta yi aiki ne be ishe ki ba,ko maza sun kare duniyar ga ni ko me zan yi da FIK yaro sai shegen isa fadin kai da girman kan masifa,Allah ma ya raba ni wlhy,koma gida bana son wannan maganar don na ga alamun yau iskanci kike ji"dariya Zuhra ta fashe da shi wanda ya kara hasala Sabeeha har ya sanya ta kara sauri ta dan wuce Zuhran da sauri ta nufo ta tare da riko hannun ta "yi hakuri Sahiba ta wasa nake fa"harara Sabeeha ta watsa mata sanann tace "na ji gwamma ya tsaya a wasan ba,and Wlhy kar ki kuma bana son wanann wasar banza"da haka suka cigaba da takowa har suka samu abun hawa,salama suka yi da Zuhran kan sai zuwa gobe in Allah ya kaimu sannan Sabeeha ta shige kasuwa,sauran kudin hannun ta ta dan yi musu tsince tsince na kayan abinci wanda za su bukata daidai karfin ta sannan ta nufo gida,tun a kofar gida ta ji ranta ya baci ganin Abdul-Fatah da shashasun abokan shi suna zaune suna shan rake daga ganin ta kuwa ya mike da sauri tare da nufo ta "Ah chika ta an dawo ke nan,kawo in karba miki kayan rayuwa ta"

Cikin sanyin murya tace "Yaya Abdul ka bar shi kawai zan karasar da kai na"da sauri yace "no no no Chika Ai ke yar hutu ce,in ma tunanin ki Hajiya na nan ne za ta yi miki haushi don ta ga na dauka miki kaya to kwantar da hankalin ki bata ma nan,kawo kawai mana baby ta"ya kare yana kokarin taba hannun ta,da sauri ta mika mishi ledoji tare da saurin yin gaba,bayan ta ya biyo yana wakar "67 150"yana wani dariyar yan iska tare da kare wa duwawkan ta da ke juyawa idanu yana me lashe baki kamar wani tsohon maye,a haka suka shigo gidan tana jin shi yana wakar ko kula shi bata yi ba,don irin wanann tace za ta tanka rai ne kawai zai baci.

Sun zo dab da shashin su suka jiyo muryan Latifa "Kan uban nan na rantse da girman Allah Sadauki sai na fada wa Hajiya dan dago wanann shegiyar mayya ta maida ka"

Da sauri yace "Ke karamar yanyan in ban ci durin uwar ki akan zagar chika ta da kike yi ba ki canza mun suna,dan gatan uwar ki har kya hada wanann mummunan fuskan naki iya ta tsohuwar karya da wanann Butuful babes din,idan baki daina shiga harka ta ba na rantse da Allahn Annabi Musa sai na canza miki halitta"

A zafafe tace "Bura Uban nan kai Fatah ni kake zagi da ciwa mutunci akan wanann karamar alhakiin nan"da sauri ya katse ta da fadin "na ci miki har wata mutunci gare ki Shegiya da gashi kamar gashin Hammatar Waske aboki na,dan uwar ki har wani mutunci gare ki ke da karan sigari ta ta fiye mun ke da Uwar ki da Uban ki mutunci da daraja a guri na"

A zafafe tace "Fatah!!!Wlhy ya ishe ka ba fa zai yu don ka ga ina kula ka duk wata banzar maganar da ta fito bakin ka ka fada mun ba fa,Wlhy sanin kan ka ne bani da mutunci,in ci uwar ka Ladi abu ne me sauki a guri na"

"Ke dallah rike mun aiki,jakar mata soyayyar dai nace bana yi da ke Babes nake so ana dole ne,ehyeee
Mayya ki Kyalle ni na huta,ki nemo daidai da ke domin ni ba class din kucaka irin ki bane"ya kare yana yana jan tsaki tare da shige wa sashin su Sabeehar,wata yar karamar ihu Latifa ta sake ta rasa gane dalilin da ya sanya Abdul Fatah baya kaunar ta,duk iya kokarin ta a kan shi amamn kullum a banza,gashi babu abinda ka mata ciwo kamar yanda ko kunya baya ji a ko ina caka mata maganganu da zagi ya ke yi,wata zuciyar ne tace da ita laifin ki ne ko ma miye yayi miki da baki nuna kina kaunar shi tare da jakantar da kan ki a gare shi ba Ai da be isa yayi miki haka ba,hawaye ta share domin so ba a dadi yana mata zagin kare dangi a gaban Sabeeha ta san tana can tan ta kal ta ci nasara a kan ta,dole ne ma ta gyara masa zama rayuwa ba za ta tafi a haka ba.

Saida Abdul Fatah ya karaci surutun shi,sanann ya ja kafa ya bar sashin nasu ,a nan ne Sabeeha take fada wa Umma duk yanda suka yi don ganin ta da kayan abinci,nan ta sanar da ita wani ne ya mata kyautan kudin kan wai yana son alawar madaran ta,amman sam bata sanar da ita kan FIK bane,Addua sosai Umma tayi tare da sanya masa albarka,sanann Sabeeha ta shiga tayi wanka tare da sako kayan bacci,sanann ta shiga kitchen don daura musu abincin da za su ci,sai a lokacin ne ma maganganun Zuhra suka dawo mata a kai,kai kawai ta girgiza sanann ta ce a bayyane "Allah ma ya raba bawa da munanniyar kaddara,akan me Allah ya sauwaka"Umma ce tace "Ke lafiyar ki kuwa na ji kina maganganu ke kadai?"

"Umma babu komai wani labarin da Zuhra ta bani nake tuno wa"daga haka ta shiga aikin nata inda Umman kuma tana dakin ta.


**************

Direct hostel ta biya gurin Zuhra inda tana isa kuwa ta tarar ta gama dafa indomie sai turiri yake a plate,a take ta washe hakwara

"Zuhraty Aminiyas tsaban missing din ki da nake ya sanya ma kasa shiga class saida na zo na ga kyakkyawar face din ki"wata wawiyar dariya Zuhra ta saki sanann tace "to munafuka uwar dadin baki,Sabeeha in ma akan Indomie na kike haka to kwantar da hankalin ki ba ci za ki yi ba"

Cokali Sabeeha ta dauka sannan ta zauna tana fadin "Ke Dalla zan ji ko ya kai na ran nan dadi ne ni ba wani ci ma zan yi ba"haka dai Zuhra na ta bar ta ta ci abincin ta amman Sabeeha saida suka ga karshen plate din nan a tare,rai a bace Zuhra ta mike tare da wanko face da bakin ta sannan ta karasa shiri suka nufi ajin su,tana ta yi wa Sabeeha mitar ta cinye mata indomie,inda Sabeeha ta share ta kamar bata san da ita take ba.

A seat din da suka saba zama kullum suka zauna inda zaman na su yayi daidai da tabo ta da Zuhra tayi "Sabeeha look"ta kare tana nuna mata Red Roses 🌹 da ke aje a gaban ta,tare da wata yar card karama me design me kyau,sai kuma box of chocolates daga gani kasan zai yi dadi,fuska cike da mamaki Sabeeha tace "ikon Allah what all this kuma?"

"Nima abunda na fada ke nan,check out the card maybe ki samu idea akan wanda ya turo miki,don Wlhy chocolates din nan sun shiga rai na"

"Ke dai Zuhra Wlhy kwadayi zai zamo ajalin ki,kika san ko na Aljanu ne?", "Ke Wlhy ko na Aljanu ne sai na sha in ya so su kama ni,in ba za ki bude card din ba ma bari na karanta miki da kai na,don Wlhy my mouth is watering"ta kare tana daukan card din tare da bude wa ita dai Sabeeha da ido kawai ta ke bin ta.

Nan ko ta bude card din tare da karanto rubutun da ke ciki kamar haka
"You're so super sexy! There's no one — and I mean no one — who comes even close to you,baby pink Abaya looks good on you😍

Da sauri Sabeeha kalli Zuhra sanann ta kalli card din kuma ta kalli kan ta,tabbas Baby pink Abaya take sanye da shi yau,Waye wanann haka?

"Zuhra from Waye wannan card din??" "Wlhy Sabeeha nima ban sani ba iya abinda na gani ke nan"hannu ta mika mata alamun bani card din mu gani,babu musu kuwa ta mika mata card din,in da same abunda Zuhra ta karanta haka ya ke a rubuce,tsaki ta ja rai a bace tace "Ke ki ji mun wani maganar banza wannan wani irin card ne,wai so sexy no one will come close to me,ko wani wahalallan ne sai Allah"ta kare tana yanyanka card din.......

Jama'ar Annabi mun wuni lafiya??

Ayi mun afuwa na jina shiru kwana biyu ko in ce kwana hudu ban dan ji dadi bane,musu kira da mun messages Jiki yayi sauki Alhamdulilah na kuma gode Allah ya saka ya kuma bar zumunci😌

WASA DA SO NOVEL FANS

Ina godiya kwarai da irin so kula da kaunar da kuke yi mun Ubangiji ya saka muku,Allah ya tsaya muku a duk inda kuke❤️

Hakika nin Gaskiya ina mika godiya ta ga dumbin masoya na wanda na sani da wanda ban sani ba,bisa kaunar da kuke wa littafin WASA DA SO,irin yanda kuka karbe shi Allah ya so ku ya kaunace ku ya kuma
tsaya muku

Alhamdulilah na warere za mu cigaba daga inda muka tsaya😌kar dai a manta da yin Comment da sharing pls

Ina yi wa kowa fatan Alkhairi.

Ga verder met lezen

Dit interesseert je vast

545K 22.1K 92
Join the ride full of possessiveness, love,hate,pain,happiness,joy,rudeness.
115K 4K 41
Y/N was a teenage introvert who enjoyed having her own space and being alone. She loved listening to music in her room, which was a great escape for...
7K 61 12
⚠️رواية منحرفة خاصة للبالغين⚠️ وَقَعْتُ بِحُبِ رَجُلٍ ثَلٰاَثِينِيٖ قَاٰمَ بِتَرْبِيَتِيٖ إِنَكَ مُتَزَوِجْ يَاسَيِدْ جُيُوٰنْ قَتَلَ كُلْ مَنْ حَا...
7K 338 10
All that terrified 23-year-old Ayra were pink notes. Whenever she found one, she ran like hell. This time, her frantic escape led her to the bustling...