Da kamar ma baze barta ba yace se ta haihu.

Se da ummansa tasa Baki sannan fa ya yadda ba Dan ransa ya so ba ,dole ya hakura,tayi shiri yau zata zo ,shi Kuma ze kawota

Washe fari da wuri. Suka taso suka zo kano ,iyayensu  sun yi murna da ganinta cikin koshin lafiya ita ma haka ,bayan sun huta ne ,washe gari yaya Sadiq ya juya bakin aikinsa

A bangaren Amal ita ma abubuwa da yawa sun faru ,yanzu yaya farouk ya bar takura Mata da fada ko hantara ,iya karta da shi gaisuwa da Kuma kula da gida se girki da take masa ya ko saki jiki ya kwashi abincin sa ba kunya ba komai🤣

Har gidansu ya kai ta kwanaki Nan me ummee ke cewa ya sawo Mata waya yace to da zasu dawo ne ya biya ya saya Mata ITEL P33PLUS ,ai ko ranar yasha godiya wurin Amal har se da ya gaji yace ya isa hakanan ,yanzu ma Shirin shiga school take yi Dan har ya kammala Mata komai Ammah cewa yayi ss3 zata shiga yadda ba jimawa zasuyi exam se ta shiga jami'a
Ranar kusan raba dare tayi ta na murna har gari ya waye shima yaga canji sosai a wurinta se fari'a take har suka zauna yin breakfast se tace

"Yaya nagode sosai Allah ya saka da Alkhairi "

Dagowa yayi ya kalleta yace Amin
Kafin yace
"Naga alamar tunda Akayi zancen school dinnan kike ta farin ciki Allah yasa zakiyi karatun ba Wasa Zaki yi

Ai Amal sake sakin jiki tayi Tana washe Baki tace" Allah yaya karatu Zan yi sosai da ma fa Ina matukar son karatun sosai"

Kallonta yayi shima ya Dan saki fuska yace"Really"

Tace "eh"

Yace "Allah ya bada sa'a"
Tace "Amin"

To zan  iya cewa shima farouk tuni ya watsar da haushin aurensa da yake ji ,Dan ya kula yarinyar nada hankali Bata damu da shi ba ma ,sannan a Dan tsakanin Nan ya rasa meke damunsa akanta ,duk lokacin da ya zauna baya da aiki se tunanin ta, har khaleel ya so dago sa, ammah se yace masa Allah ya kiyaye shi Kam me ze sa ya zauna yana tunanin Amal

Se dai khaleel yayi dariya yace "zama kazo ka fara ne"

Bayan fitarsa ne ba jimawa taji ana knocking Tana budewa taga Aunty Ramla ai kuwa ta saki kuwa ta rungumeta ,ita ma rungumeta tayi suka shigo gidan ,bayan sun saki juna ,Aunty Ramla ke ta kallon Amal ganin yadda cikin wata biyu ta murje ta Kara wani fari sosai,ko ita da ke da yaron ciki jikinta be canza kamar na Amal din ba

Ganin irin kallon da Ramla ke Mata yasa tace
" aunty lafiya?"

Murmushi tayi tace kanwata Naga duk kin canza ko dai mun samu baby ne matar soja

Rufe fuska tayi Tana dariya tace a'a Aunty ba komai Allah ,tace "to naji , to ya kike ya gidan

"Tace lafiya Lau"

Tashi tayi taje kitchen ta dauko ruwa da lemu da Kuma snacks ta gabatar ma Ramla

Ita dai Ramla se biyar Amal din take da Ido taga ta fara Hankali,tana Kuma jin dadin yadda ta iskota lafiya Lau

Ruwa kawai Tasha ,saboda tunda ta samu cikin Nan ba komai take ci ba ,Amal din ce ta zo tace "Aunty tashi mu shiga dakina?"

A hankali ta tashi ta bita ,suka shiga gado Amal ta nufa ta zauna , Ramla na Shirin zama kan stool tayi sauri tace

Aunty ki zauna kan gado Mana

Harararta tayi tace "gadon mijin naki Zan hau ,Allah ya kiyaye"

"Ai ba Nan ya ke kwana ba gadonsa na dakinsa ,a can yake kwana "

Kallon tuhuma Ramla ta fara ma Amal din  kafin tace
"Wai har yanzu baku shirya ke da mijinki bane?"

Murmushi Amal tayi kafin tace "ai yanzu mun shirya aunty ba kamar da ba Kinga ya siyamin waya Kuma yanzu ya mayar da Ni school ,sannan ya ce Ni ai kanwar sa ce , yanzu ba ya sani aiki me wuya baya min fada Kuma duk abunda n nace Ina so Yana siyamin"

Kallon marar wayau Ramla ke ta biyar Amal din da shi kafin tace

"Habah Amal ke Wai kamar Baki taba zuwa Islamiyya ba ,ai duk wadannan abuabuwan da kika lissafo ban ji kince Yana sauke hakin sa na aure ba"

"Aunty nifa kanwarsa ce Baki ga yadda muke shiri ba"

Buge bakin Ramla tayi ,Amal ko ta bata fuska ,Nan Ramla ta shiga yi Mata fada sosai ,sannan ta dawo  ahankali ta mata bayanin komai dalla dalla Nan fa ta dinga rufe fuska,inda a karshe ta bata shawarar Abubuwan da zata dingayi har ta jawo hankalinsa ,ta ce Mata Kuma"in kika yi Wasa kina Nan zakiji yayi aurensa ya barki

Ai ko Amal tace"aure Tana zare ido" dama kishi ne da ita kamar me ,Nan fa tace Aunty Insha'Allah Zan gyara
Ramla tace da dai yafi Miki ,Nan ta bude jaka ta dauko wani littafi me suna
DON MA'AURATA
ta bata Nan ta shiga yi Mata godiya

Kusan yini Aunty Ramla tayi a gidan Dan har farouk ya isko ta a gidan ,suka gaisa cikin sakin fuska kuwa har yake tambayarta yaya sadiq tace Yana Nan lafiya

Ganin ya dawo aunty Ramla tace zata wuce yace "ta bari yazo ya Kai ta "

Ai ko Amal Tai kwal kwal da Ido  kamar zata yi kuka ganin Ramla ta fito zasu wuce,cewa yayi je ki dauko hijab dinki mu kaita

Ai kusan da gudu ta juya ta dauko hijab dinta suka je tare Kai Aunty Ramla gida,suna Akan hanya se da ya tsaya a wani mall yayi sayyayya sosai,sannan  ya dawo cikin motar suka ci gaba da tafiya har suka iso kofar gidan Nan Ramla ta masa godiya zata fita kudi ya dauko ze Bata ,taki karba har se da yayi muryar Amal yace "habah Aunty Ramla"
Duk dariya suka saki sannan fa ta karba ta sake to masa godiya sosai

Tana fita Ramla da sauri ta juya Tana kokarin bude kofar da take zaune ,ji tayi  an riko dayan Hanunta Tana juyowa se taga shine yake binta da wani mayen kallo ,sannan idanunsa sun wani Kara girma,gira ya daga Mata yace "Ina Zaki "?

Marairaicewa  tayi tace "yaya gaisawa za muyi da su Ummah na fito mu tafi"

Se ya sake cewa "nifa a wurin wa Zaki barni"

Gabanta taji Yana faduwa ganin irin Abubuwan da yake Mata ,sannan ga wata kunya da take ji ,katse Mata tunani yayi yace to kimin iso nima Zan shigo mu gaisa ,ya Bata ledojin da yayo sayayya yace "gashi kiba ummah"

Godiya ta masa ta fita a motar,cikin gidan ta shiga

Tana fita ya dafe kansa ,ya rasa me yake damunsa Akan yarinyar Nan yanzu..................✍️

*Aysha galadima ce*

Vote
Comment
Share

ANYI GUDUN GARAWhere stories live. Discover now