Aysha tana da kokari sosai dan gaba daya malaman boko da islamiya,sun santa da kokari dn duk abinda aka koya tuni brain dinta ke nadewa ,komai ka koya mata zama yake daram akanta.sosai sauran students suke bakincikin kokarin da Allah ya bata,dn daga class dinsu na boko hr na islamiya bata taba haura first position.wannan yasa m.saleh da umma atika ke iya kokarinsu wajen ganin sun mata kyauta ta bajinta idan ta kawo report card din ta.

  "Ummana ina kika sanya min turaren wannan na duba bn ganshi ba"aysha ta fada kamar zatayi kuka sbd ganin ta kusan yin latti yau gashi itace da duty yau dole su zasu tare masu latti su da teacher dn dake da duty yau,idan kuma prefect tazo a makare to sai malamin ya mata hukunci fiye da sauran daliban da suka makara.yanzu aysha tana matakin jss2 ne kuma prefect  ce dan dama iya jss3 senior scul dn tana can tsallaken kwalta.

"yanzu kina ganin bakwai har da minti goma amma bazaki zo ki tafi ba ,kn tsaya neman turare,ace kullum mutum sai yayi wanki da guga indai yasa uniform bazai Maimaita ba gashi dai kayan ba wani datti suke ba,na fada miki babu kyau mace ta shafa turare in zata fita"Umma atika ta fada tana daga waje.

"haba umma ynzu sai nayi latti, dn allah ki fada. min wlh banaso inke warin gumi,Kuma kinga turare bashi da karfin kamshi tunda Body spray ne"Ta fada yayin da take tsaye bakin kofar daki tana neman yin kuka.

"Ay sai ki duba Cikin lokar wannan karama"umma atika ta fada tana juyawa domin cigaba da abinda take.juyawa tayi a guje taje ta fesa Turaren ta dakko scul bag dinta ta fito da sauri,dakin abbanta ta shiga ta gaishe dashi ya bata kudin makaranta ta fito ta yiwa ummanta sallama ta fito tana sauri dan lokacin har bakwai da ashirin da biyu.

  Misalin karfe biyu aka tashesu daga scul,su uku suke tafiya ita da kawayenta guda biyu,sun zo daidai inda zasuyi hanyar gdnsu sukayi sallama da juna ta kama hanyar layin da zai sadata da gidah.

 
Tafiya take a nutse sanye take da uniform green din dogon wando da farar rigah iya gwiwa sai karamin farin hijabi da ko cikinta,kayan sun bala,in karbarta,yellow din dankwalinta na prefect ya bala,in fito da zallar kyanta,doguwar fuskarta tayi kamar jikin hijabin aka halicceta.ko daga nesa kake kana iya hango wata Tawadar allah a gefen kumatunta ,labbanta sun yiwa fuskarta ado dan idan ba wanda yasan aysha ba zaiyi zaton pink din janbaki take shafawa.alhalin matukar scul zataje bata shafa komai daya danganci kayan kwalliya daga kwalli sai ko perfume.gashi daga scul ta dawo amma in ka ganta sai kayi zaton yanzu zata tafi scul din sbd yadda kayan suke a goge dan tsabar sawun gugar dake, tsakaninsu.AYSHA SALEH RONI akwai tsafta sosai amma na fita tsafta😅😜

Dai dai kwanar gdnsu tana shirin tsallake wata yar karamar kwata ,irin makwaranyar wanke wanke ce aka mata hanyar wucewa zuwa babbar kwata,shine ta biyo ta kan hanya wani wawan hon taji an saki,dago kan da zatayi taga wata farar mota mai bakin glass dn ko na ciki baka iya gani.dakatawa tayi da tsallaka kwatar amma kuma kafin ta matsa,mai motar ya bi ta cikin kwatar gaba daya sai ruwan kwatar yayi jikin uniform dinta,dn hr fuskarta sai da ruwan kwatamin ya taba,gefen hijabin tasanya inda ruwan bai taba ba ta goge fuskarta,kallon kayanta take da gaba daya suka gama baci,juyawa tayi ta kalli motar kamar zatayi kuka dan tuni ma kwalla ta taru a idanunta,gani tayi motar ta tsaya.

"Me hakan kb ya zaka tsaya akan wannan karamar yarinyar???"zuly ta fada tana tsareshi da ido.

"Haba zuly ya zakice mesa zan tsaya byn kina ganin yadda na batawa yarinya jiki da kwatami"kabeer ya fada yana kokarin bude kofar zai fita.

"To wai me kake kokarin yi ne hakuri zaka bata,kome kake nufi kamar kai dai kb hr ka tsaya baiwa wannan kazamar yarinyar hkr,kodan na ga tunda muka shawo kwanar nan idanunka akanta,daman garin kallon nata ka shiga kwatamin Allah ma yasa baka jefamu cikin katuwar kwatar can ba, dn kaga farar mace"Ta fada tana murguda masa baki tare da juyar da kai gefe"

Kankance idanu yayi yana kallonta,dan shi kwata kwata bayason raini,dn bai yarda kowace yarinya                         rainashi ba,"An kalleta dn kiyi abinda zakiyi"ya fada yana Bude kofar ya fita daga cikin motar,saurayine baki dogo kyakkyawa dashi dan bakin nashi ma na kyau ne,sanye yake da wando dogo wanda aka yayyaga gwiwar sa,sai farar riga mai dogon hannu an yi rubutu a jikin rigar kamar haka LUV ME 🧡 sai kuma akayi hoton heart ,kafafunsa sanye cikin bakin sau ciki.

Kallon wurin daya ganta tsaye ta cikin mirrow dn motar yayi,lokacin tana goge ruwan fuskarta da hijabinta.amma me kamar anyi ruwa an dauke babu ko alamarta a wurin bare ya sanya ran ganinta,Hangawa ya shiga yi wai ko zai ganta amma bai ganta ba.

"Oh God ina yarinyar nan ta shigane"cewar kb yana dafe goshi.juyawa yayi jiki ba kwari ya koma motar,"to ko dai aljana ce?"wani sashen na zuciyarsa ya tambaya.

"Wayyo Allah kuyi  hkr ku kuke ganinmu bamu ke ganinku ba"ya fada a tsorace dn kb akwai tsoron aljannu

Zuly kokarin danne dariyarta take, dan ta fahimci inda tunanin kb yaje sosai tayi farinciki dn tasan yanzu sai yace yanason yarinyar bazaiga kankantarta ba,dn shegen son matane dashi.ita kuma taga lokacin da yarinyar tayi tafiyarta.

"Ayya sorry insha Allah ay kafi karfinsu ,bazasu maka komai ba tunda ba da gan gan ka mata ba"ta fada dn ta kwntar masa da hnkali.kallonta kawai yayi ya maida kanshi kan styarin ,dn bayaso ko kadan ta gane ya tsorata dan karta rainashi.zuciyarshi ce ta bashi gwara ya bar wurin kar wani abu ya faru dashi.key ya yiwa motar ya figeta a guje yana barin layin ma gaba daya.

Aysha kwa ganin sun bata mata kayanta yasa tayi tafiyarta,dan tasan tsayawar da sukayi ma zasu iya dukanta tunda duniya ba gskia yanzu,sai a dannewa bawa hakkinsa matsawar bashi da karfi ma,ana idan shi ba kowan kowa bane.wato bai ajiye ba bai kuma baiwa wani ajiya ba.

  Tafiya take kanta a sunkuye dn gaba daya kunya take a ganta a haka dk da ba sabon aysha bane kalle kalle ahanya,dn ma dai ta kusa zuwa gida,ita daman bata da fada gata kuma da zallar hkr ,dk da taji ciwon bata mata kayanta da akayi Amma bazatace komai ba ,bare ma bataga na cikin motar ba.shiga gdnsu tayi bakinta dauke da sallama,umma ce ta amsa mata,tana shigowa tayi ido biyu da kawunta kanin ummanta kawu habibu ya kawo musu ziyara.
"Oyoyo kawu"ta fada da murna.su kuma tsayawa sukayi baki suna ganin yadda kayqnta ya baci,itama kallon jikinta tayi inda taga suna kallo

Dan tabe baki tayi tace "wata motace ta fallatso min da zata wuce"aysha ta amsa kafin a jefo mata tambayar.

"Kawu bari inyi wanka inzo mu gaisa ka bani labarin tsoffin nan"cewar aysha tana juyawa ta shige daki.

GIDAN MIJINAKde žijí příběhy. Začni objevovat