TA FI DA HAKA!!!.

1 0 0
                                    

_*🍒TA FI DA HAKA🍒*_
           *2/1/ 2021*

_MALLAKAR:HAUWA S ZARIA_
             *(Mman Uswan)*

*Arewa writers association✍️*

*FREE PAGE__2*

Yana sa kai da niyyar shiga ɗaki Karima ta hankaɗesa gami da wawuransa ta shake kana taci gaba da cewa"yau koni ko kai a gidan nan, wlhy saika sakeni domin bazan zauna da mutumi dake bakin ciki dani ba.
   Yanzu menene abin bakin ciki eyye Karima!?sabida...Bata bari ya ƙarisa ba ta taresa da eh!komai me zakace kace nidai saika sakeni...Tsuki yaja sanan ya buge mata hannu daga riƙon da tayi masa..da sauri ta kuma rarumosa ta shaƙe,babu yanda beyi data sakesa ba taki..take ransa ya ɓaci besan lokacin daya ɗauketa da wasu lafiyayyun maruka wanda Saida takai kasa ba tare dasani ba.
  Fatsuma dake tsaye bin Innarta tai da ido tana kallonta.
A ɓangaren Umaima da Rahina kuwa dik abinda keceyi a kunni su,zamansu sukayi suna sauraron duk abinda faruwa.
   Ya sanya kai kenan kamar daga sama yaji saukan abu a kansa wanda yasa shi gigita gami da faɗin innallilahi wa'inna'ilaihin raju'un..kalmar da yayi ta memetawa kenan.Take jini ya wanke masa jiki.Fatsuma dake tsaye ihu tasa gami da niman ɗauki..kadan kenan daga Cikin aikina.abinda naji ya fito daga bakin Karima kenan.
Tirƙashi Allah ya kyauta nace.
  Jin muryan  malam Ado cikin wani irin yanayi ne yasa Umaima leƙowa..Hannu Tilo tasa ta rike babanta. Ko kafin Umaima ta fito tuni jini ya rufe masa ido, dafe Fatsuma yayi gami da dafe kansa inda ke fidda jini.
Leƙowar da Umaima zatayi tasa ihu..jin ihun Umaima yasa Rahina fitowa daga nata ɗakin.
   Duk da faruwan hakan besan Karima nadama ba. Ko kafin su sami wanda zai daumakesu su kaisa asibiti jikinsa yayi weak zamewa yayi ya faɗi ƙasa daƙyar numfashinsa ke fita.
A guje Rahina ta fita waje ta samu wasu matasa suka taimaka masu, daukarsa sukayi zuwa wani babban asibitin ɗin dake layinsu.
  Gani yanda ake fita dashi yasa zuciyar Karima karaya.
Suna isa asibitin saida aka tambayesu dalilin afkuwar hakan.
Rahina ta ta fara magana da Umaima tayi saurin dakatar da ita da cewa"yaje shiga ban ɗakine ya zame ya faɗi.Allah ya tsare gaba doctor yace kana ya hau aikinsa.Gani yanda numfashinsa ke watan gaririya yasa doctor sawa a kaisa gado, alluran dai-daita numfashi yayi masa,kana yaci gaba da aiki. Gani girman raunin yasa doctor bada umarni ɗauko masa kayan ɗinki,alluran kashe zafi yayi masa kana ya hau ɗinki.
Koda kafin a kammala tuni bacci ya daukesa hakan yasa basu tafi a lokacin ba.
Yana kammalawa ya umarcesu tasu fita su barsa ya huta, tare suka fita,shi ya nifi office nasa su kuma gefe suka koma suma zauna.Fatsuma dake tare dasu ne yasa basu samu damar magana ba,amma kowa da abinda yake faɗi a zuciyarsa dangane da halin da mijinsu ya shiga tun daga lokacin daya auri Karima har zuwa wannan lokacin.
Karima dake gida ta kasa zaune ta kasa tsaye, sai faman kai kawo takeyi har lokacin sallah yayi batayi ba,da shiya damuta yayi ba hakan yasa batabi takan ba.Bakin gado ta zauna gami da zabga uban tagumi,babu abinda zuciyarta ke raya mata irin sake da warwara.duk a tunanita gawar Malam Ado ne za'a dawo dashi.
Alhamdullhi malam Ado be falka ba sai misali taran dare,sanna ya falka bakinsa dauke da salati,a lokacin duk matayen nasa na kansa tsaye, sannu-sannu naji suke ce masa..shi kuma yana amsawa da yauwa.Fatsuma dake gefensu sannu baba tace,gami da tambayarsa jiki.
Da sauki uwata yace"Cikin karfin hali ya yunkura zai miƙe da sauri suka kamosa gami da tambayar mai zaiyi?.
Alwala zanyi nayi sallah.
A'a ka bari ka ƙara jin sauki mana malam!.
   A'a kudai barni nayi kada lokaci ya kure.
  Mikewar da zaiyi yaji kansa yayi masa nawi,hannu yasa ya dafe gefen kansa,gami da cewa"washhhh!!!..turo ƙofar doctor ne dukkansu juyawa sukayi ga ƙofar da aka turo.
Sannuku yace,kana yayi kan malam Ado dake zaune sannu baba ya jikin?.
  Jiki da sauki.Allah ya ƙara sauki.Amin. magugunu ya rubuta masa sanan yace"ya basu sallama akan bayan kwana uku su dawo.
Godiya sukayi masa, Umaima ta ta taimakawa malam Ado,ita kuma Rahina na rike da rigarsa suka bar asibitin.
Gani har goma tayi babu malam Ado babu dalilinsa yasa Karima ƙara shiga matsananci damuwa,wasu-wasi takeyi ta bisu asibiti ne ko kuma ta tsaya ta gani.
  wata zuciyar kuma tace"idan kije asibiti me zakice dashi bayan kece silar shigarsa wanan hali, a fili tace"ohh!ni Karima naga ta kaina, Allah yasa kada malam  Ado ya mutu,kwalla ne suka gangaro bisa kuncisa me cike da nadama da dana sani.
  Tana Cikin wanna halin ne tajiyo muryan su Rahina da Umaima da sauri ta mike ta nufosu har ta kusa kaiwa garesu sai kuma taja ta tsaya tirus.Umaima ce ta daka mata tsawa da dallah kaucewa mutane a hanya, yarinyar banza yarinyar wufi kawai.
  Sumi-sumi taja gefe suka shige, ɗakinta ta kaisa kasancewar itace uwar gida.
     Bakin gado suka zaunar dashi, Rahina ce ya umarta data kawo masa ruwa a buta yayi alwala.Cikin hanzari taje ta ɗibo gami da ɗan madai-daiciyar bawon da zai tare ruwan yayinda Umaima ke finshiɗa masa sallaya.
  Yana idarwa yahau sallaya domi sallah, Jin juwa na ɗibansa yasa shi zama, a zaune yayi sallahr.ko kafin ya idar tuni suje su haɗo masa farau-farau suka tanada masa, yana idarwa yasha gami da magugunarsa sanna ya kwanta.
    Su jima zauna suna hira sanna sukayi sallama Rahina ta tafi nata ɗakin,babu yanda Umaima batayi da Fatsuma da taje ɗakin innarta ta kwanta ba amma taki, hata ta gaji ta kyaleta suka kwana tare.
   Daren yau Karima batayi baccin kirkiba, abu goma da ashirin ne ya sata gaba, na farko rauni da tajiwa malam Ado na biyu kuma kwanar da Tilo tayi a ɗakin Umaima,haka ta kwana tana murƙusu-murƙusu sai kusan asuba bacci ya dauketa.
     Misali ƙarfe bakwai saiga jama'ar unguwa su doka sallama a bakin garka, Rahina ce ta amsa da shiya tunda ta idar da sallah bata tashi daga kan sallayar ba zama tayi tana lazumi.
   Leƙawa tayi gami da tambayar su waye?.
   Gyaran muryan daga daga cikinsu ne yasa ta tsayuwa, can daga nisa suka gaisa ba tare da ta hangosu ba, sanna suke sanar da ita, suzo duba malam Ado ne ko lafiya,kasancewar baya fashin sallar tun jiya da muka idar da sallar la'asar dashi bamu kuma ganisa ba shine mukazo dubasa ko lafiya?.
   Sallah sarki naji Rahina tace kana ta sanar dasu abunda ya samesa...haɗa baki sukayi da subhanallilahi, su jima suna jajjata mata kana tace dasu tana zuwa. Ciki ta koma taje ta sanar dashi, umarni ya bata da taje ta shigo dasu.
Komawa tayi ta sanar dasu,tare suka shigo, kasancewar sunada yawa yasa basu samu shiga daga ciki ba a bakin kofa suka tsantsaya suka gaisa gami da jajjata masa.
Bayan fitarsa ne lokacin Rahina na ɗakin, Umaima ta umarci Fatsuma data fita ta basu waje.
Ba tare da musu ba ta fita, ɗakin Rahina taje ta zauna tana jiran su gama magan ta dawo wajan babanta.
    Bayan fitan Fatsuma ce Umaima ta fara da cewa"yanzu sabida Allah da Annabi haka zaka zubawa Karima ido,duk irin abinda takeyi maka be ishe ba har sai takai ga niman ranka?to wlhy bari kaji idan ta gaji dakai mu bamu gaji dakai ba.. Rahina dake zaune tace"Ato kema kyace.kana Umaima taci gaba da cewa,tunda har kaga ta fara da haka gaba nefa abu ji...Gaskiya ne Rahina tace..Gyaran murya malam Ado yayi kana ya fara da cewa"naji duk bayananki amma wani abu da kika mance dashi, aure raine dashi,da zaran lokacinsa yakai tofa babu makawa sai an rabu, don haka nake ƙara maku hakuri, ba naki taku bane,lokacin rabuwarmu ce beyi ba.
Kusa a ranku da zaran lokaci yayi rai mu rabu...ajiyar zuciya dukkansu sukayi kana Umaima tace"yanzu haka zamu zuba ido muna kallo wanan irin rashin ɗa'a da ɗiban albarka da takeyi.. nannayar ajiyar zuciya yayi kana yace"hakurin nadai da kukeyi shi nakeso kuci gaba duk abinda yayi farko yanada ƙarshe,uhmm kawai Umaima tace,daga sanan bata kuma magana ba.Itama Rahina shiru tayi.Gani har tara bega Karima ba yasa shi miƙewa ya fita zuwa dakinta,cike da mamaki suka bisa da ido,duk da hakan ba sabon abu bane a wajansa.
Da sallama ya shiga ɗakin, bakin gado ya sameta zaune, tana daga kai suka haɗa ido da sauri ta dauke kanta gefe.
   Murmushi yayi sanna ya samu waje kusa da inda take zaune ya zauna gami da kiran sunanta Karima!!!!!...

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Oct 19, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

TA FI DA HAKA!!!Where stories live. Discover now