81&82

672 47 10
                                    

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
         *GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

     *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________________

  _STORY AND WRITING_ _BY_

    _Jameelah jameey 🖋_

    *(Yar mutan kankia👸🏻)* 

  


*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*

_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

'''NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍'''

81&82

Koda ya shiga room ɗinshi toilet ya wuce direct, shower ya kunnama kanshi tundaga sama sai da yaji ya dan dawo dai dai sannan ya ɗauro towel ya fito, maganin da Aliyu ya kawo mashi ya ɓalla ya sha, dafe kanshi yayi da hannu biyu yana mamakin yanda da yaga Hakima sai yaji shi'awa ta taso mashi kamar ya mutu, ashe daman haka yake da saurin shi'awa bayan shi dai yasan ba haka yake ba, kwanciya yayi rubda ciki yana yana tunanin yanda zamanshi da Hakima zai kasance cikin wannan yanayin idan ko haka ne gaskiya da matsala babba tunda ya fahimci shi mabukacine sosai, haka ya kama juye juyenshi bisa gado har lokacin sallah yayi ya tashi ya tafi massallaci.

Tunda Hakim ya tashi ya shiga room ɗinshi, Hakima take dariyar ƙeta dan ta lura Hakim bai da wuyar shiga hannu, tana gama breakfast ta shiga su Lantana suka shigo suka cigaba da firar su, da ta gaji da surutun ta tashi ta shiga room dinta ta cigaba da waya da Maryam sai da lokacin sallah yayi Sannan sukayi sallama, Hakima taji dadin wayar da sukayi da Maryam dan ta kara bata shawara sosai kuma ta dauka, wanka ta shiga sannan tayi kwaliya tasa shidda darkblue ɗinkin doguwar riga fiketgown da tasha aikin paintward abun yayi kyau sosai sallah tayi sannan ta wuce kitchen dan sama ma kanta abunda zataci, fitowa tayi tana gyara ɗaurin dan kwalinta bata lura da mutun ba sai kawai taji sunci kwaro da juna, dan kwalin faduwa yayi gashinta baki ɗaya ya baje bisa fuskarta, hannu tasa ta matsar da gashin tana sosa goshinta dan zafi yake mata sosai ji tay yana cewa, "wai ke wata kallar wawiyace? Ko ke makauniyace da zaki wani taho baki kallon gabanki sai kace gidanki."?

"Ya isa haka Hakim, baka isa ka gaya man magana ba, bayan bugeni da kayi kuma ka dawo kana gayaman maganganu mararsa dadin ji, idan ni makauniyace to kai mai zance maka? Naji ban gani kai da kake gani waya hanaka kaucewa da ka hangoni."?

"Ke har kin isa kiyi man wannan questoin ɗin sai kace sa'anki."?

"Gashi kuwa ai gaskiya na faɗa, ta faɗi tana murguɗe mashi baki, kallon dan ƙaramin bakinta yake dan tayi mashi kyau sosai dake murguɗe bakin sai yaji dama ta dawo tasake yi mashi, cewa yayi, "Ni Hakima kike murguɗe ma baki, kamar abokin ki."?

"Eh ɗin an murguɗe."...  tace tana  ƙara murguɗe wa biyota Hakima yayi da gudu itama ta ruga, haka suka kama zagaye parlourn suna gudu shi dole sai ya kamata, yana sane yaƙi kamata dan abun yayi mashi dadi sosai shiyasa bai kamata ba, da Hakima ta gaji ta faɗa ɗakinta ta kwanta bisa gado tana maida numfashin wahala, tana cewa, "mugu kawai kaidai Hakim wallahi mugune ko dan baka sona shiyasa kake san cin zalin ɗina.".... Haka ta kamaa surutunta sannan ta tashi ta fito dan ta ɗauki dan kwalinta, zaune yake cikin parlourn yana kallon NTA NEWS, ta gefenshi ta wuce ta shiga kitchen indomie ta dafa sannan ta fito ta zauna ta fara ci tana kallo tashi tayi ta ɗauko remote ta sake tasha ta mai TELEVISTA TV tana kallon music, shima Hakim tashi yayi ya maida NTA NEW haka ta tashi ta chanza inda take haka sukai tayi ba wanda yayi ma wani magana, tashi taga yayi ya nufo ta ta shi da gudu ta shiga, ɗaki dariya ya kamayi yana cewa, "ga jan faɗa dai shigen tsoro."

GIMBIYA HAKIMAWhere stories live. Discover now