BAKU FINI BA by Zainobe.Bismillahir Rahmanir Rahim.

49 5 2
                                    

Ajine da akalla yake dauke da dalibai sama da mutum ashirin,idan aka hada lissafin yan ajin gaba daya zasu tasamma mutum ashirin da biyar.Wannan doka ce ko kuma ka'ida na makarantar Noble College a duk wani aji dalibai basa haura ashirin da biyar,wasu na duba littattafan su yayin da wasu ke hira,wasu kuma na kokarin maimaita abinda ya shige musu duhu ta hanyar karawa juna sani wato group discussion.Maryam Ali Bawa daya daga cikin daliban ajin JSS 1A na takure a gefe ɗaya ita kadai duk da dai ko wani kujera mutum bibbiyu ne amma ita a nata kujerar,ita kadai ce ba don bata da seat mate ba ah ah,ita seat mate din ce tayi gudun hijira zuwa wani seat din sakamakon kin son wata mu'amala ta shiga tsakanin ta da Maryam Ali.Maryam tayi tagumi,da taga babu mai kula ta kamar kullum,sai ta bude jakanta ta fiddo littafin Save The African Womb tana karantawa,daya daga cikin littattafan da aka basu yayin registration,tana tsaka da karatu malamin English ya shigo,nan da nan kowa ya nitsu malam ya shiga bada darasi,kamar kullum bayan ya gama yayi musu tambaya Maryam ce ta amsa saboda darasin turanci na daya daga cikin darussan da tafiso kuma take fahimta sosai,malamin yace a tafa mata,daliban suka tafa sama-sama badon ransu ya so ba.Akasarin daliban Noble College ya'yan manya ne kuma yawanci half caste ne,ko ya'yan turawa ko kuma larabawa da sauran kabilun duniya mazauna Najeriya.Lokacin break nayi suka fito dan suje school dining hall suci abinci don dokace a makarantar,ba'a yarda ko wani dalibi yaci abinci a ko'ina sai a dining hall da aka gina da zaran an tashi break kowa ta dauki lunch box dinta taje can taci,hakan ce ta faru da Maryama yayinda ta dauki dan karamin lunch bag dinta ta nufi hanyar dining hall kasancewar bata da kawa kuma yan class din su basuson jerawa da ita ta wuce salin alin taje tazauna abun ta,tashiga cin abinci a nitse batabi ta kan masu tsegumi a kanta ba don idan da sabo ta saba.

Bayan sun gama breakfast aka buga kararrawa dalibai suka koma aji,aka ci gaba da darasi har aka tashi,Maryama ta saba school bag din ta a baya ta rike lunch bag din ta tana kokarin fita daga class din wanj yaro ya sa mata kafa da gangan ta fado tim!a kasa ya dubeta yana dariya yace"Black magic tasha kasa",Cikin bacin rai Maryam ta tashi ta rabe ta gefe ta wuce ba tare da tace mishi komai ba har ta isa wurin motar su,ta shige mal.Sadi direba yaja suka tafi.A hanya in banda tunani babu abinda Maryam keyi,a ranta cewa take"me yasa akasarin mutane suka tsaneta ne?"Ita tunda ta taso tayi wayo ta lura mutane basa son ta hatta yan gidan su idan ka cire Iyayenta yayyinta basu damu da ita ba duk da ta kasance auta a gidan.Ta duba,ta hanga ta hango bata ga wani aibu a tattare da ita ba,bata da wani nakasar da za'ace ita nakasashshiya ce,da lafiyan ta,sannan tarbiyya daidai gwargwado ta sameshi duk da dai yanzu take tasowa shekarunta basu wuce 12 ba a duniya amma kwakwlawarta ta fara samun damuwan kyara da wasu ke mata,bata an kara ba sai jin muryan Malam Sadi tayi yana cewa"Yar Baba mun iso gida".Ta sauke ajiyar zuciya tare da bude kofan motan ta fito ta nufi cikin gida.Kasancewar gidan babba ne a farko bata iske kowa ba sai kai tsaye ta zarce dakin mahaifiyarsu Hajiya Amina wacce suke kira da Amma,ta iske Amma na waya ta zauna a bakin gado tana jira ta gama,tana gamawa ta dubi yar autar ta ta da fara'a a fuskarta tace"daddy's girl an dawo,ya makaranta,da fatan kin fara sabawa da environment din?"Maryam ta dubeta tace"Alhamdulillahi Amma,ina wuni?" "Lafiya lau,maza aje a cire uniform ayi wanka,ayi sallah ko?" Ta mike tare da cewa"Amma..."sai kuma tayi shiru.Amma ta dubeta tace"Ya dai,menene?"Ta girgiza kai alamar ba komai kana ta fita daga dakin ta nufi kitchen ta ajiye lunch bag dinta ta wuce daki,ta iske yar'uwarta Hafsah da ta gama Secondary bana tace"Sis ya gida?"Hafsah da hankalinta yayi nisa a kan waya ta amsa a dakile "Lafiya".

Da la'asar Maryam da Hafsah sukayi shirin Islamiyya mal.Sadi ya sauke su kasancewar ita Hafsah duk da tayi sauka tana zuwa hadda,duk arzikin iyayen su basa wasa ta wannan bangaren da tarbiyyan ya yansu,Amma jajirtacciyar mace ce kan iyalanta arzikin su baisa ta sangarta ya'yan ta ba tana kula da tarbiyyar su sosai.Alhaji Ali Bawa dan asalin Jihar Jigawa ne,yayi karatu har zuwa matakin masters,a halin yanzu yana aiki ne da kamfanin fasa kauri wato custom kuma har ya kai matsayin Assistant Comptroller general,A Abuja yake da iyalanshi Hajiya Amina wacce ya auro daga Kano da ƴaƴan shi hudu Maza biyu mata biyu.Marwan shine babban dan shi,a halin yanzu yana Lagos inda yake aiki da matar sa sai mai bi mishi Safwan shikuma yana Uganda yana karantar Engineering sai Hafsah da a bana ta gama Secondary sannan auta Maryama.Hajiya Amina Fulanin Sumaila ce,kyakkyawar mace wanke hannu ka taba,shi kanshi Alhaji Ali ba baya bane wurin kyau saboda haka duk ya'yan su suka debo kyawun iyayen su da hasken fatan su idan ka cire Maryam da ta fita daban,saboda Maryam Baka ce sosai sannan bata cikin sahun kyawawa,sai dai adan shekarunta idan ka dubeta zaka gane nan gaba za'ayi mace mai diri,Maryam bata da Kyan azo a gani ko kadan sannan bakin ta daban ne sai dai kuma akwai yalwar gashin kai da suka gado wurin Amma,kowa ya dubeta sai yace"mummunan gidan" lokacin da aka haife ta mahaifiyar Alhaji Ali cewa take"Amina farar tukunya mai fidda farin tuwo amma dai kam bana kin fidda bakin tuwo,wannan ya kaman a yanka a boye wuka".Wasu kuma sai suce"Yar dunan gidan Amma"ire-iren waɗannan maganganun ake gayawa Amma akan Maryam tun tana basarwa har ta fara jin zafin masu fadan saboda hatta yayyinta basa wani damuwa da ita Hafsah har cewa take Maryam money miss road ce,sam bata kama da ƴaƴan masu kudi,sai da Amma tayi mata kaca-kaca kan wannan furucin,su kuma dama yayyinta maza kadaran kadahan ne babu dai affection tsakanin su kawai hujjar su shine Maryam ta faye baki da muni, a bangaren Daddy kuwa,duk ya'yan shi babu wacce yake so irin Maryam saboda tanada wani irin charisma da idan ka dubeta beyond the beauty,zaka gane hakan,ga nitsuwa kaman ba yarinya karama ba.

BAKU FINI BA.Donde viven las historias. Descúbrelo ahora