25

667 80 10
                                    

Koda Ummu suka dawo Aisha ta riga ta tashi, harma tayi shirin islamiya ta magariba dan haka kawai cewa ummu tai Basira tazo tace Abbansu yace ta cewa Faruk ya ɗan jira su.

To kawai ummu tace ta hau warkajamin ta.

******

Zaune take tana bawa Muhammad Mama, Hajiya ta fito ya dan tago kansa ya yaɗa mata hannu yana murmushi, Hajita tace ohni Rakiya, wato ummu kindai ƙi yaye yaron nan, kinajin abinda umman Walid tace miki ki yaye shi ba sai bikin yazo ba kinƙi yaro yai wayo.

Murmushi ummu ta yi, fadin haka da Hajiya ta yi sai ya tuna mata da iyayan ta lokacin tana goyon ƴan biyu harma da khairi, haka Abbansu zaita mita yara sun zama barden goyo taki yaye su, ta ce ita sai yaranta sun shekara biyu.

Azahiri kuwa murmushi Ummu ta yi, kafin tace khai Hajiya shima fa Faruk ɗin yasan ina shayar wa, kuma munyi da shi sai Muhammad ya shekara biyu zan yaye shi ta faɗa a shagwaɓance tana shafa kan muhd ɗin.

Salati Hajiya ta saka eyye to baki isa ba, sati mai zuwa dole ki yaye shi, ba inda zaki da yaro rabe rabe azo ganin amarya aga tana zaune tana shayarwa to me za'a ce ya auro.

Dariya Ummu ta yi kafin tace basai a ɗaga auren ba zuwa ya isa yaye.

Ah lallai yaro na gudu da kafar sa ki ce bai isa yaye ba, Hajiya ta faɗa ba alamun wasa.

Watansa fa tara kwata kwata, Ummu ta faɗa tana kallon yaron.

Girgiza kai Hajiya ta yi kafin ta ce sai kuma kiyi, batun yaye dole ne, ni zan fita.

To Adalafiya tace tana ƙoƙarin gyara rigarta bayan ta dire Muhammad dan ganin ya ƙoshi.

Hajiya na fita ita kuma ta ɗauki abincinta taci, kafin tayi soro dan karɓar Khairiyya, maza na gama shiri ki tafi kar Ya Sheikh yai fishi dan ma munyi sa'a yana muku uziri yanzu.

Bari kawai yaya har fa mamaki nake ya zane wasu mu ya barmu bacin yasan anan muke zama ba wani abin muke ba inji Khairiyya.

Murmushi tayi Ummu, kafin tace tausayi ne yasan nan ce kawai hanyar samunmu, ya kuma san indai kun zauna ɗin lalura ce tasa na barku.

Hakane Khairiyya ta faɗa kafin ta yi ciki agaggauce, dan shiryawa su Su Aisha sun jima da tafiya, kusan kullum haka suke wani zai zauna kafin ummu ta gama komai sauran su tafi in ta gama sai ta amshi mai zaman.

Muhammad na naniƙe da Ummu Khairiyya ta fito ta miƙa masa hannu alamar tawo mu tafi, ya maƙe kai jikin Ummu alamar basai jeba Khairiyya taɗan masa dukan wasa ta ce karkazo ɗin ta fita tana dariya ummu tace lala kika dakeshi sai na rama masa.

Sai yanma lis Hajiya ta dawo kamar shekaran jiya yauma kasuwa taje haka akai ta shigo da kayan da ta siyo a kasuwa, wanda duk kayan bikin Ummu ne da amarya ke buƙata na gida.

Ummu tayi tayi ta amshi wani abin agunsu na cinikin su taƙi filin ta guda ta siyar dan yiwa Ummu kayan ɗaku.

Yauma saida Ummu tai kuka gami da godewa Allah ya amshi tasu mahaifiyar ya basu wata.

********

Kusan kwana uku tsakani Kawu ya aikawa yace ummu ta Faɗawa Faruk in sun shirya shida iyayen nasa sa su zo ranar Lahadi.

Daɗi cika ummu yayi, dan tanason Faruk sosai ji take tamkar ta janyo gobe tazo ta faɗa masa danma yanzu kunyar kiransa awaya take da tuni ta kira ta faɗa masa.

Ko da daddare kasa faɗa masa tayi, amma shi kansa yadda take hirar yasan tabbas tana cikin farin ciki.

Washe gari kuwa tun kan ta faɗa masa yace wai Matar ya ne, naga yau annashuwar ta daban ce kusan ma zance tun jiya.

Ummu HaniWhere stories live. Discover now