12

21 1 0
                                    

💥KISWAH💥

(Surrogacy was the cause)

              Na

CHUCHUJAY ✍️

Book1⃣

Page 1⃣2⃣

__________Washe gari cikin wata irin  walwala Kiswa ta tashi,dan haka tayi shirin office ,bata da Niyyar yin wani breakfast dan haka tacewa Baba Baraka idan an tambaye ta inda take tace tana azumi ,ille kuwa Appa ya tambayi Baba Baraka ganin kowa yazo banda ita,Kafun ya rufe baki daga tambayar da yayi Farry ta cabe inda take cewa"Appa we are complete here tunda dai dama ai ba ƴarka bace  Ko Mother Why bother?"

Wani irin kallo Appa ya bata Kafun yace"sai dai in ba ƴar maman ki ba amma ni Kiswa tawace domin kuwa yarda nake jinta a raina ma bana jinki sannan idan na sake jin wata maganar banza a bakin ki zaki zauna a gida ki bani kujerar office ɗina dan bana tunanin zaki iya girmama ma'aikatana yarda ya kamata duba da yarda respect ɗinki yake neman ƙarewa ".

Dif kake jin Farry kamar anyi Ruwa an ɗauke,duk da yarda bakin ta ke ƙyaiƙayi akan tayi magana ta ƙwabesa dan tasan halin Appa.

Fitowa Kiswa tayi cikin shirinta tsaf tare da wani vibe Energy da ta samarwa kanta dan tayi Alƙwarin sauke nauyin Saleek dake kanta a yau wanda take ganin Shine best solution,at least bazai kashe ta ba haka zalika bazai daketa ba,ganin yarda suka zauna suna cin abinci zuciyarta taji tana mai bata taje ta zauna musamman yarda taga seat ɗinta empty ,Allah ya sani tana san su tana ƙaunar su saboda sune family ɗin da ta sani sannan ta shaƙu dasu tun yarinta bata fatan ace yau sabani mai girma yana shiga tsakanin su amma Mother is hellbent taga ta b'ata mata abunda take so da sunanta dana mahaifiyarta ,dan haka itama ta ɗaura ɗamarar kare duk wani bullet da zata jefeta da shi,Takawa tayi dan zuwa gaisawa dasu Kafun ta wuce,tana isa gurin Appa ya Faɗaɗa fara'arsa yace "har na fara tunanin fushi Kike damu da yasa ba zakici abinci da mu ba "cike da ƙaunarsa tace "Appa ni ina zan fushi da family na mai kyau,na tashine da azumi ,ina ƙwana"ta faɗa gudun zama taci abincin dasu duk da ba azumin take ba.

Cike da jin dadi ya amsa mata gaisuwarta yayin da ta gaida mother da yayyinta amma su kadai suka amsa banda mother,ba tare da ta damu ba ta tashi tayi musu sallama ta fita..

**********

Ta daɗe cikin motar ta tana tunanin yarda zata fuskanci Saleek kasancewar sa mutum mai murɗaɗen hali,ta iya iyuwa jira yake tazo tayi confessing ya ɗauki wani matakin akanta amma hakan bai dameta ba domin kuwa ta shirya daukar consequences na abunda ta aikata at least ta fito masa da gaskiya kuma zata basa hakuri hukuncin da zai ɗauka ya rage nasa ,wata irin kunyarsa take ji musamman da ya kasance irin sunayen da ta kirasa dasu waɗanda ba hallayarsa bace sharrin Farry ne ,ajiyar zuciya tayi ta dauko Jakarta ta fito a motan ta kulle ta nufi cikin company ɗin,straight office ɗin Saleek ta nufa Kafun kwarin gwiwarta ya ƙare dan a yanzu ta shirya fuskantar sa da  karfinta ,koda ta isa bakin ƙofar sa tsaye tayi tana cije baki Kafun tayi karfin hali wajen ƙwanƙwasa masa ,knocking ɗaya tayi ya bata izini da ta shigo kamar barauniya haka ta shiga bakinta ɗauke da sallama,kamar an mitsinesa haka ya ɗago ya kalleta dan baya expecting ɗinta ,jingina bayansa yayi da kujerarsa yana kallanta Kafun ya Amsa mata sallamar ta ya ƙara da cewa"lafiya dai Ko? dan duk wani document, da nake bukata yana kan desk dina sannan duk wani meeting schedule ɗina Khaleefa yayi arranging mini so a yarda nake tunani abu daya ne zai kawoki inda nake wanda Shine ƙarya da rashin kunya domin kuwa idan akwai abunda kika ƙware akai Shine wannan abu guda biyun bayan aikin ki dan haka bismillah nasan duk wata hanya da zanbi dake in dai Nine have a seat ".

Zama tayi tana mai saukar da kanta ƙasaa cike da jin kunyarsa sosai,kula da yayi da kunyarsa da take jine yasaka shi kwashe wa da wata irin dariya har yana mai fito da ƙwalla yace"kaji mun yarinyar nan fa,nine kike jin kunya Ko kuma wani sabon salan munafurcinne kika shiryo da safiyar Allahn nan kika zo ki sauke mun ita dan bana tunanin Ko office ɗinki Kin shiga,Allah yasa ba wani bacin ran kika kullo mun ba domin kuwa Dariyar nan da kikaga inayi akwai wani abu a bayanta idan aka tunzura ni dan haka karki fara.

KISWAH 1✔Onde histórias criam vida. Descubra agora