7

16 1 0
                                    

💥KISWAH💥

(Surrogacy was the cause)

   Na

CHUCHUJAY ✍️

Book1⃣

Page7⃣

Da mamaki Kiswah ke kallan Saleek wanda ya bayyana gaban ta yana tafa hannunsa yayin da fuskarsa ke dauke da wani irin murmushin da take ji kamar ta cire masa Shi da tafin hannunta domin ba sai ya faɗa mata ba labe yayi mata,

Cike haɗe rai tace"na haɗu da maza kala kala amma Ban taba haɗuwa da ill mannared irin ka ba,bana tunanin ka samu tarbiyya sanin menene labe akan maganar wasu take nufi,idan kuma ka samu to a wannan gibar bakayi amfani da ita ba.

Wani irin haɗe rai Saleek yayi domin maganar ta tayi masa zafin da bai tunanin zatayi masa ba,cikin mutuƙar bacin rai yace"Ko Me zaki ce kar ki fara jimamin yama tarbiyya ta take Cos bana tunani Kin fitini ta wani guri Cos Your personality is a mess,kinsan bake nake tausayi ba shi wanchan guy din da ya wuce shine yake mugun bani tausayi saboda he's in a deep shit da yayi getting involved da Gold digging bitch kamar ki,Just imagine baki Ko jin nauyi da tsoran Allah,mata irinki mayaudara maha'inta babu waɗanda Ban gani ba,running from one man's pants to another.....

Marin da ta dauke sa dashi cikin hawaye shine abunda ya katse masa hanzari ,hannun sa ya ɗaga cikin fushi ya daki gefen motarta yana mai faman huci kan ya kama hannunta da karfi yace"This should be the last time da zaki kuma daukan wannan hannun naki mai kama da bulaliyar kara ki taba fuskanta,sannan ki gode ma Allah bana dukan mata da yau sai na fasa miki baki,and for Your information i heard it jiya kece kika je date dina wanda dama na sani i would never be wrong ,ki shirya saboda i will sue you for slender idan ba haka ba ba sunana Saleek ba "

Sakin hannun ta da ya damƙe da karfi yayi ya juya a fusace yana mai fadin"useless girl".

Kuka ta rushe dashi tace"you're the must useless stupid jerk I've ever meet sannan idan ka sake shiga hurumina Zan ci maka mutunci fiye da tunanin ka,wawa kawai"

Kamar bai ji ta ba haka ya cigaba da tafiya zuciyarsa kuma na masa wata irin zafi da ƙuna na tabbatarwa da yayi cewa Kiswa itace taje gurin sa jiya abunda kuma ke sake soya masa zuciya shine rashin sanin dalilin yin hakan,tunanin sa ya fara bashi kilan dan kuɗi tayi,maimakon ya koma ciki sai ya shiga motan sa ya bar harbar gurin zuciyarsa nayi masa wani irin tuya da ba zai iya fasaltawa ba.

   ******

SALEEK BASIL MADUGU babban ɗa a gurin Chairman Basil Madugu da matarsa Hajiya Asiya,asalinsu mutanen cikin Kauyen Gwagwalada ne dake cikin garin Abuja,mahaifinsa Chairman Basil ada talaka ne wanda idan ka kallesa a yanzu da da zaka daɗe kana karyatawa akan bashi bane waninsa ne,rayuwa yayi shida matarsa da yaransu guda ɗaya Habib cikin yan uba wanda suka sakashi gaba cike da tsangwama da takura musamman da 'ya kasance shine bashi da komai ,rashin jituwa da kuma rashin daɗin zama shine ya fito da Chairman Basil daga cikin Gwagwalada inda 'ya tarar da Alherin sa cikin garin na Abuja,Rayuwa da daɗi babu daɗi haka ya dage wajen ganin ya gina rayuwar yaran sa Habib da matarsa Asiya mai hakuri da juriya,lokaci ɗaya ciwan cancer ya kama Habib ta kwakwalwa wadda ke neman maƙuda kuɗin da za'a shawo kanta amma duk yarda ya buga ya buga a kulle ga dukkan wasu samuwarsa ta ta'allake kan ciwan na Habib,ganin abun yaci tura ga habib na buƙatar a fitar dashi kasar yasa ya koma gida domin a siyar da gadonsa a raba a bashi amma abunda ya tarar yafi na da domin kuwa karyata kasan cewarsa jinin mahaifinsa sukayi sannan suka masa korar kare,baƙin ciki goma da ishirin komawarsa gida ya tarar da gawar Habib,yaci kuka iya kuka domin shi daya Allah ya basa ga kuma bakin ciki Na karyata identity ɗin sa da yan uwansa sukayi bugu da ƙari har da manyan garin waɗada suka san tabbas Shi ɗin jin mahaifnsa ne amma suka juya masa baya saboda abun duniya,yayi fushi mutuƙa wanda ya sakashi rantsuwar babu shi babu danginsa har abada,a haka ya rungumi matar sa suka cigaba da rayuwa inda 'ya samu wani uban gidan da yake aiki karkashinsa cikin aminci da amana,a hankali arziƙi ya fara zuwar masa kasancewar 'ya samu uban gida na gari mara mugunta ,yana da nasibi na kasuwanci dan a kome 'ya taba sai albarka ta sauka cikinsa,lokacin da ya samu shago na kansa Asiya ta samu cikin Saleek wanda Chairman Basil ya kwallafa rai akansa ,kulawa ga Asiya kuwa sai tafi ta da a haka har ta sauke cikin Saleek wanda suka dauki san duniya suka ɗora masa,haihuwar Saleek kuwa kamar an ƙara masa arziƙi haka arziƙinsa ya cigaba da habaka,kafun kace mene abun yasha banban Dan shi mutum ne maiyi da gaske,Ko ta ina kasuwanci zuwa masa yake ana damawa dashi,

KISWAH 1✔Kde žijí příběhy. Začni objevovat