Mu na nan zumuncin mu na ta qara qarfi da Maman Abdurraheem, zaman lafiya na ta wanzuwa tsakani na da Yah Maheer, sai dai kun san a koda yaushe ba a rasa sabani irin na harshe da haqori, to muma mu na samun wannan lokaci zuwa lokaci,watarana mu na zaune ana hirar gida da ni da Yah Maheer sai na ce,

"Kaiiii amma ban taɓa zuwa gidan da ya yi bala'in yi min dad'i ba sama da wanda mu ka yi d'innan ba hayaniya,ba takura ba tashin hankali,zallan zumunci aka sha aka dawo,komai cikin sauqi gwanin sha'awa"

Wata kalma Yah Maheer ya jefe ni da ita da ta sanya ni hantsilawa daga kujerar da nake zaune na kifa qasan carpet ba shiri tare da sauke masa idanu na da ke cike da tsantsan mamakin kalaman shi.

"Me ka ce? Me ka kira ni da shi?"

Cikin nuna rashin danasanin kalaman shi ya maimaita abinda ya ce,

"Cewa na yi dole ki ce wancan zuwan ya maki dad'i mana tunda kin haɗa munafurci kin taho"

Ji na yi kamar ya buga min guduma akai na, tsabar yanda na ji kalmar munafurcin ta dake ni, mutumin da banza ko wani sunan zagi be taɓa haɗa ni da shi ba ke faɗin na haɗa munafurci, to wanne munafurcin na haɗa, nan da nan na ji ido na ya taru da hawaye, Suwaidatu da ke zaune a gefen mu sai ta hau raba ido a tsakanin mu, zama na yi da kyau ina fuskantar shi na ce,

"Wanne irin munafurci na haɗa ni kuwa har da ban sani ba tsahon lokacin nan da muka ɗauka da dawowar mu, ashe na haɗa munafurci shine ba ka taɓa faɗa min ba? Ba dan an dakko maganar gida ba kenan haka za ka dinga min kallon munafuka ba zaka sanar da ni komai ba ko?"

Nan take idon shi ya nuna nadamar abinda ya faɗa amma bakin shi ya kasa qaryata kalaman shi, zama na gyara na ce se ya sanar da ni munafurcin da na haɗa, nan ya fara zayyano min wani zancen qarya da aka tuqa shi aka ce ni Mahreen ni na faɗa kuma ni na hada komai, ashe bayan tafiya ta Bauchi daga liman Katagum har gaban manya aka zauna aka tattauna, direct a gaban mutane Yah Maheer bai kare ni ba saboda kar a ga ya bi baya na sai ya furta musu cewa 'Ashe Mahreen ita ce munafukar da ta haɗa komai ta tafi' nan take Kabeer  ya ce 'Kai ma ka san ba zata taɓa aikata hakan ba a dai sake bincike'.

Wani irin duhu na ji ya mamayen ido na tsabar hawayen da ke zuba min ba na gani sosai kwata kwata, nan take na zauna na zayyane masa duk abinda ya faru iyakar gaskiya ta,alamun gamsuwa da kwanciyar hankali ne suka bayyana a saman fuskar Yah Maheer wanda ya bani mamaki matuqa, kenan da ban masa bayani ba ya yarda ni munafuka ce har ya iya furta hakan a gaban mutane? A duniya be taɓa min abinda ya qona min rai irin wannan ba, wani irin haushin shi da ban taɓa ji bane ya mamaye zuciya ta.

Nan take mu na zaune ya sa waya ya kira Kabeer  ya bashi labarin kaff da na bashi, ina Jiyo sanda kabeer ya ce masa,

'Ai na faɗa maka ba zata taɓa yin abinda aka ce ta yi ba, habaa kowa fa da kalar tarbiyyar shi, kuma mun san halin kowa, kowa da abinda in aka ce maka ya aikata to fa ba makawa ya aikata ɗin in kuma aka ce maka be aikata ba to fa be aikata ba'

"Hakane, Allah ya sa mu dace ya haɗa kan iyalan mu, Allah ya shiryar mana da su"

"Ameeen ya Allah"

Sallama suka yi da junan su, sannan Yah Maheer ya miqe ya na so ya kama ni dan ya bani hakuri, wani irin kallo na watsa masa da ban san ma zan iya yi masa irin kallon ba har abada, jikin shi ne ya yi mugun sanyi, ya durqusa gaba na ya na so ya kamo hannu na, kuka na fashe da shi sosai, zuciya ta na quna matuqa.

Ina son da yake min?
Ina kulawar da yake bani?
Ina qaunar da ke tsakanin mu?
Ina aminci da yardar da ke tsakanin mu?
Ta ya za a yi abu bana nan iya tsahon wannan lokacin ya kasa sanar da ni?

Ta ya za a yi abu bana nan ya kasa tsaya min har ya kira ni da munafuka a gaban mutane?

Me yasa ba zai bada shaida akai na ba tunda ya san ba hali na bane ba zan taba iya bata zumuncin da ke tsakanin mu ba se dai na gyara.

MAHREEN Where stories live. Discover now