part 11

31 6 2
                                    

*FRIENDSHIP*
            *(ABOTA)*

*_SHOT STORY_*
_*[GAJEREN LABARI]*_

*E.W.F*

By
Mrs bb
Mom muhseen.

Watt pad name
Humaira3461.

     Page.....11

"Allah sarki Annur hak'ik'a ba karamin so yake miki ba Noor, kuma yayi namijin k'ok'ari da ya iya sarrafa zuciyarsa akan ki, ba duka maza ne zasu iya haka ba ace har gidan ku yana zuwa har cikin falon ku amman bai tab'a yunk'urin tab'aki da sunan sha'awa ba, har cikin raina naji ina son shi dake hankalin sa ya burgeni natsuwar sa da kamewar sa abunso ce ga kowa, hakika naji maki babu dad'i rabuwarku da tazo a haka, amman bazan baki goyon bayan rabuwa dashi ba ina maki sha'awar auren sa Noor, inaji araina zaki ji dadin zama dashi"

Wasu hawayene suka silalo mani ban san ko namiye ba, nafi alak'anta su sa hawayen farin cikin yabon Besty na da yaya yusra tayi, sai naji wani kwarin guiwa yana shigata, wani karfi da kuzari yana ninkuwa a zuciyata murmushi yake maye gurbin kuncin da na shiga a farko, na share hawayen nace "yaya yusra naji dadin kalamanki, kuma zanso ace hakan ta kasance nida shi, amman kin san akwai babban k'alubale gaban mu? Kin san koda babu wannan case d'in tsakanina da Annur Abby bazai barni na aure sa ba?"

Tana kallo na tace, "saboda me? A ganina Annur yakai duk matakin da Abby zai bashi ke"

Na tashi ina lalubo kayan da zan saka nace mata, "uhm yaya yusra kenan, kamar dai kin soma mance waye abby ko? Bari na tuna maki to, Abby dai baya hud'd'a da talaka shi ko jikin gidansa baya son talaka ya rab'a balle ace shine yau zai dauki d'iyar sa yaba shi matsayin aure, baya ga haka annur yana da wata *NAKASA* da har yau ban san wace irin nakasa bace, da maman sa take fad'a akodayaushe shima kuma yake yawan cemun.
"Besty akwai abunda yake kullub'e dani, wanda nakejin tsoron watarana ki gujeni domin sa"

"Idan na tambayesa miye wannan abun, saidai yai murmushi yace mun in lokaci yayi zan sani, inajin tsoron wannan abun yaya yusra inajin matukar tsoron koma miye, wanda zai k'ara nisantani dashi, ban tab'a soyayya ba haka ban tab'a jin ina son wani ba kwatantacin irin abunda nakeji akansa, ban tabbatar ba sai jiya zuwa yau yaya yusra"

Na karashe da rauni acikin muryata, isowa tayi wurina ta riko hannuwa na cikin lallashi tace, "karki tashi hankalin ki noor, insha Allah babu abunda zai rabaki da Annur, koma miye zai faru zaizo ya faru ya wuce yabarku tare, zan tsaya maki wajen baki kwarin guiwa da kuma shawara har sai kin mallake sa"

Mun jima sosai da ita adakina muna tattaunawa kafin sham ta shigo kawo mani dinner sannan tatafi, saida nayi sallolin da banyi ba nai karatun qur'ani sannan na fara shan fruits d'in dake cikin tiren, kallona kawai sham keyi nasan tausayi nake bata har dai ta kasa yin shiru tace, "kiyi hakuri Noor haka rayuwa take"

Murmushi nayi mata nace, "dole zanyi hakuri da rayuwa sham, amman bazan iya hakuri da Besty ba a yadda nakejin zuciyata bana jin zan iya yin wata rayuwar Aure da wani inbashi ba, rabanin da akai dashbaiba abunda ya k'ara mani face tsantsar kaunar sa, duk kafiyar Abby sham insha Allah nida Annur tip da taya ne ba zamu tab'a rabuwa ba"

Jinjina kai tayi tace, "ina bayanki akan hakan, domin Annur yakai hakan duk wadda ta samesa rik'esa zatai tsam ba zata so ya kub'uce mata ba, amman don Allah kibi komi ahankali zan tayaki da addua insha Allah"

Godiya nai mata mai yawa sannan tace, "zan tayaki kwana ko nabarki ke kad'ai"

Murmushi nayi nace, "kije abunki baba Azumi na buk'atarki, nima zanyi waya da Annur nasan duk inda hankalin sa yake yakai k'ololuwar tashi, kuma nasan ya kirani yafi sau miliyan wayar kashe, kije kawai sham saida safe kinzo tashina sallar azuba"

Da haka muka rabu da ita na gama shan fruit din ban ma tab'a cus-cus din ba nadai sha furar da ta hado mun da ita, nakoma na kwanta ina kwanciya na zaro wayata dake caji gefen gado kenan naji za'a shigo, nai saurin rufe idona don bana son ganin kowa yanzu.

Ammi ce ta shigo zama tayi gefen kaina tana ta kallona, ta shafi kaina daga karshe ta tofa mun addua ta sumbaci kaina sannan tatafi.

Kunna wayar nayi na zura mata idanuna ina kallon ta tana loading, gabana bugawa kawai yake da sauri da sauri kamar zuciyar zata keta kirjin ta fito waje, har ta gama setting din komi sannan missed call d'insa suka ringa shigo min ba k'akkautawa, da yake wayata ko kashe take inka kirani dana kunna zanga missed call, bazan ma iya kirga adadin kiran dayai mani ba, na gyara kwanciyata na danna numbers din banki na na saka creadit don wanda garan bazai isheni ba, no din sa na lalubo na danna kira rufe idona nayi inajin sautin shigar kiran yana tafiya tare da bugun zuciyata, hankalina naji duk ya tashi jin bai dauka ba na sake kira ina jin tashin hankali, saida nai kira biyar ana shiddan ne aka d'auka..................muryata da kuka nace, "BESTY karka ce mun fushi kayi, besty ba laifina bane................kwantar da hankalin ki Noor kowa yasan bakida laifi, karki ga bai dauka ba kwance yake ba lafiya, amman da sauki ruwa ma ake samashi ya samu bacci"

Duk mama ce ke maganar, hawaye suka ziraromun ina shashshekar kuka nace, "mama don Allah kigaya mun gaskiya, badai wani mummunan abu ne ya samesa ba ko"

Tace, "Kibar kukan haka Noor babu abunda ya same sa masassarace da ciwon kai, sai damuwa kinga ma ya tashi baccin bari na baki shi"

Muryar sa ta dishe sosai tayi irin ta marasa lafiya yace, "BESTY"

Wasu zafafan hawaye suka silalo man na limshe idona inajin wasu sabbin feelings suna taso mun, kuka na sake fashewa dashi nasaka hannu na toshe bakina.

Cikin raunin murya yace, "kibar kukan nan besty karki saka ciwona ya karu, kibarni naji da mikin rabuwar mu, abunda Abby yayi mani ko kad'an bai b'ata mun raiba Besty, saima k'aramun ganin girman sa da darajarsa da nayi, kuma kema na k'ara sanin girmanki da muhimmancin ki, abunda zaifi tayar mun da hankali akanki shine Abby ya rabani dake rabuwa ta har abada, Besty injin aranar bazan kwana duniya ba domin inajin kece mahad'in rayuwata..............tari ya sarke sa saida yayi mai dan yawa sannan, ya tsagaita ni kuma banda kuka da nakeyi can k'asa babu abunda nake, wani sabon son shi ne yake huda zuciyata har bansan yadda bakina zai misalta ba, jin nayi shiru ya sashi cigaba da cewa.

"Besty ki yimun wata alfarma guda d'aya don Allah"

Ina shashshekar kukan muryata ta shak'e nace, "inajin ka"

Ya lumshe idonsa saboda jin yadda muryar tashige sa, cikin kasala yaci gaba da cewa "BESTY karki bari Abby ya rabani dake, nasan ko badad'e koba jima dole hakan zata kasance don Allah Besty kiyi mun wannan alfarmar"

Ina ta shashshekar kukana nace, "Annur taya zan hana Abby ya rabani dakai? Bacin ba wata manufa acikin *ABOTAR* mu, sannan abunda baka sani ba shine Abby shirye yake ya aurar dani cikin k'ank'anin lokaci"

Wani tari ya fara yi daya gigitani na ringa kuka ina kiran sunan sa, karshe ban sake jinsa ba wayar ma nai kiran duniya kashe take, nayi kuka wannan dare har bansan iyaka na karshe durk'ushe nayi bacci naci kuka nagode Allah saidai kiran asuba ya tayar dani da kuma sanyin tayils d'in wajen.




Mom muhseen✍🏻

FRIENDSHIP (A BOTA)Όπου ζουν οι ιστορίες. Ανακάλυψε τώρα