Ba wai dan baya sonta ba, a'a sai dan saboda tsananin ƙaunar da yake mata hakan yasa shi sadaukar da soyayyar da yake mata ga wanda zuciyarsa take ganin ba shine ya dace da ita ba matuƙar yana raye...duk da irin bala'in son da yake mata amma ita tata zuciyar ta gaza fahimtar hakan daga gare shi, a sanda tata zuciyar ke can ta faɗa tarkon son abokinsa amininsa ABBAS wanda ya riga shi furta mata kalmar so. Bai farka daga neman halaka kansa da yake ƙoƙarin yi ba saida maganar aure ta shiga tsakanin Amininsa da Abar ƙaunarsa, ya danne zuciyarsa ya haneta nuna ƙulafucin da take akan Hanan, yana ji yana gani Amininsa zai Aure muradin ransa. Kuma a kowacce rana, kowanne yini, kowacce daƙiƙa, kowanne fitar nunfashi, a duk bugu na zuciyarsa Sonta ƙara ruruwa yake a gare shi, tausar zuciyarsa yake yana lallashinta sai dai kash duk yanda yaso ya daure ya kasa, ba zai iya ba, rashin kasantuwarsu a inuwa guda zuciyarsa zata illata...shin me zai faru?, shin zai mallake ta ko A'a....?