MENE NE AIBUNA

37 2 0
                                    

*MENE NE AIBU NA??*
               
©Jeeddah Tijjani Adam
  (Jeeddahtulkhair)

Follow me on Wattpad
@jeeddahtou

27/6/2020

1

Drivern yake amma gaba ɗaya hankalinsa ba a jikinsa yake ba, ya rasa ta inda zai fara, tunani ɓacin rai gami da damuwa su suka mamaye zuciyarsa, duhu kawai yake gani, ya rasa duk wani farin cikinsa, bai qi a ce yau mutuwa ta ɗauke shi ba, sabo da tsananin damuwar da yake ciki.
Lumshe idanu ya yi gami da fitar da numfashi mai tsananin zafi, ɗaci kaɗai yake ji na fita daga cikin makoshin sa, bai san wanda zai tunkara da maganar ba, ballantana har ya iya yi masa maganin matsalar sa, Rahma ce kaɗai ita ma kuma a yau ta guje shi ta juya masa baya, bai ankara ba yaji motar na ƙoƙarin kwacewa daga hannun shi, wannan dalilin yasa ya dai-daita tunaninsa ya fara ambaton Allah don shi kaɗai ne abin da xai kawo masa rangwami a halin da yake ciki a yanxu.
  Agogon da ke daure a hannunsa ya duba ƙarfe 12:00 dai-dai na rana,  juyar da motar ya yi da niyyar ya wuce gida, amma sai wata zuciyar ta bashi shawara da kada ya tafi idan ma ya je gidan ƙarin wata damuwar ce, don haka ya kama hanyar zuwa ƙauyen Gud'e da ke karamar hukumar Gwarzo, zuciyar shi gaba ɗaya a raunane take sabo da bai san ta ina zai fara ba.
A hankali ya ci-gaba da murza sitiyarin motar har ya isa cikin garin, a bakin hanya ya tsaya ya siya kayan marmari ya wuce da su, tun daga farkon garin mutane ke masa barka da xuwa  kasancewar Aliyu mutum ne mai kyauta da girmama jama'a, kuma a duk lokacin da ya je sai ya yi musu alkhairi mai yawa, wannan dalilin ya sanya duk wanda ya ganshi sai ya yi masa barka da zuwa.

A bakin wani gida ya yi parking, gida ne irin na fulani gefe guda kuma ga shanun da suke kiwo, sai kuma rumfar kwano da ke gefe guda, cike da nutsuwa ya buɗe murfin motar sa ya fito, a hankali yake takawa ya nufi inda wasu dattijai guda biyu ke zaune bisa tabarmar kaba kowannen su hannun shi riƙe da mahuci suna fifita kasancewar lokacin ana zafi sosai, tunda suka hango shi suke washe masa baki tare da yi masa sannu da zuwa, kanshi a sunkuye ya ƙarasa inda suke, cike da girmamawa ya risuna ya gaida su, fuskar su ɗauke da murmushi suka amsa tare da kiran sunan shi.
"Aliyu barka da zuwa kaine a garin namu, ka zo tafiya da Rahma kenan, dama kai ba a ganinka sai ka kawo ta ko kuma kazo tafiya da ita" suka fadi maganar cike da zaulaya.
Rausayar da kai ya yi.
"Haba Baffa ba haka bane, ko da Rahma ko babu ita ya zama dole nazo na gan ku" gaba ɗaya suka kwashe da  dariya.
Sai da suka ɗan taɓa hira kaɗan sannan ya miƙa musu ledar da yake ɗauke da ita, godiya suka yi masa tare da saka masa albarka. kallon shi Baffa ya yi tare da yi masa magana cike da sakin fuska "ka shiga ciki mana ka gaisa da mutan gidan ita ma Rahman tana ciki, tunda dama don ita kazo" ya ƙarasa maganar tare da taɓa kafadar Aliyu.

Da farko sai da ya ji kamar yace masa bazai shiga ba sabo da bai san irin karɓar da Rahman zata yi masa ba, amma sai ya daure ya tashi, cikin ƙasan zuciyar shi cike take da tsoro, sabo da a yanzu babu wani sauran so ko kauna da Rahaman ke masa, illa ma dai kallon shi take a matsayin mutumin da ta fi tsana a rayuwarta, wanda bata so ko hanya ta haɗa su, wanda take addu'ar Allah ya nisanta ta da shi. Cikin ƙarfin hali ya amsa masa da "To" ya tashi ya shiga ciki.

Babu abin da zuciyar shi ke yi banda dukan uku-uku, tashin hankali ne sosai ya bayyana a fuskar shi, a hankali ya ja ƙafa ya shiga cikin gidan cikin sassanyar muryar shi ya yi sallama, wata dattijuwa ya tarar a tsakar gida tana tankade, da fara'a ta tarbe shi. "Barka da zuwa Malam Ali jan zaki, dama na san dole zaka biyo Rahma, kai da kace zata yi sati biyu ga shi ko kwana biyar ba a yi ba ka biyo ta, lallai wannan angon nawa ba kada ta ido"

Ɗan murmushi ya saki wanda ya tsaya iya saman lebban shi, wato  yau dai innah ɗan biki ku ke yi min ke da Baffa, shi ma abin da ya faɗa min kenan yanzu kema kuma ga shi ki maimaita" Gefenta ya samu ya xauna tare da ɗaukan rariyar da take tankade da shi "bari na taya ki aikin innah" murmushi tayi "A'a bar shi Malam Ali, so kake Rahma ta ci tara ta na saka mijinta aiki ko? ka san kishi take da ni" Da sauri yace
"A'a baxa ta faɗa ba innah ai ta san kece ta karfen" gaba ɗaya suka kwashe da dariya.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jun 27, 2022 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

MENE NE AIBUNA?Where stories live. Discover now