AMAREN BANA

AMAREN BANA

31.8K Reads 2.4K Votes 17 Part Story
Azizah Idris M. By ummyasmeen Completed

#9 in romance on 05/09/2016
"Wai ina son ki fada min, me yake damun ki ne, da za ki haddasa irin wannan fitina, sannan ki zauna lafiya, kamar ba abinda ya faru?"
Dubansa ta yi a sanyaye, sannan ta-ce. "Ina da dalilina."
"Wane irin dalili ne, zai sa ki na ji, ki na gani auren iyayenki ya mutu? Idan banda irin gurguwar tunani irin naki? Ashe ki na da halin yin gyara a wannan al'amari, ba za ki yi ba?" 
Mikewa ya yi daga kan kujerar zai tafi, da sauri ta kamo bakin rigarsa, ya tsaya, ganin zai saurareta, ya sa ta sakar masa riga.
"An fada maka ni ma ina jin dadin ganinsu da na ke yi a haka ne? Sam, ba son raina bane, amma na daure na kauda kaina, saboda mu kawar da gagarumar matsalar da ta fi wannan.
 Na san halin Momi, tana da fada, tana da rashin son gaskiya, amma kuma haka tana da saurin nadama, na san za ta nemi afuwa, kuma Abba zai saurareta. Sai dai wannan tafiyar, dole ka taimaka ka ba ni goyon baya, don mu shawo kan al'amarin nan tare."
Kallonta ya yi, ita ma duk ta jikkata, ta jejjeme ta zama wata iri, tabbas yadda take ji haka yake ji, koma fiye, don bayan baya sonta, ya tsani uwarta, sannan yana mutuwar son Meena.
"Ki yi hakuri, amma ba zan iya aurenki ba."
Ranta ya baci kwarai, har ya juya zai fita ta-ce. "Saboda me ya sa ba za ka iya aure na ba? Saboda me ya sa ban kai matsayin na zamo matarka ba?"
"Ki fada min, ta yaya zan iya zama dake, alhali ki na matsayin 'yar matar da na tashi da tsanarta a zuciyata?" 
"Wane irin dalili zai sa maka tsanar mahaifiyata, har da zai sa ni ba za ka iya aurena ba?" Shiru ta yi don ta ji dalilin wannan tsanar.

panti1996 panti1996 Apr 21
Hehe ni na dauka ma momi din itama hada rai da fada ake mata Ashe waazi ne
panti1996 panti1996 Apr 21
Shi yawa in life ina guujewa shakuwa da namiji sosai, akwai illa gaskia
panti1996 panti1996 Apr 21
Kaiiiii lallai irin su ne ake gudun zuciyansu. Akwai wani da na sani yana in ina shima and he talks very fast in yaji haushi fa da Har biga kai yake da bango amma yanzu da yayi girma sosai ya daina
panti1996 panti1996 Apr 21
Waiiii wannan a tuzuru ma shi emeritus ne chappp! Ashe ba na yau bane
UmarFatima UmarFatima Aug 23, 2016
Hummmmmm. Hope ba auren zumumci za a hada da Rumuisa ba? Akwai badakala kenan if my hunch is right. Well done Ummyasmeen great as usual
Har na hango wani dan ajinmu ke ce min haka 😂😂😂😂😂. Idan na fata dariya ma sai ya kule