MASIFAFFAN NAMIJI..!

By JamilaUmar315

55.9K 4.3K 635

A mu"amalansa da kowa Sai son Barka....Kowa kuma zai iya Fadin kyakyawan Hallayarsa..Ammh ga Matarsa Hafsah b... More

01
002
009
012
010
011
013
014
015
016
017
018
027
03
019
020
021
022
023
033
024
036
025
026
04
034
028
029
005
030
031
032
037
038
06
035
040
039
FINALE
007

008

2.1K 133 17
By JamilaUmar315

*MASIFAFFAN NAMIJI..!*

*Wattpad:JamilaUmar351*

*Dedicated To:My Habibaty❤️Aisha Abdullahi Idris..*!

*Jinjina Tare da godiya mai yawa garesku Masu Sharhi,Hakika naga Soyayyarku ga wannan labarin na kuma ji Dadi,Masoyan Audu how far?🤣Team Hafsatu..? Abdullahi na godiya da Caccakarsa da akayi tayi yace na Fada muku kowacce ta zauni Gidan Mijinta in Budurwace itama ta zauna agida banda Fitar Rashin Dalili🤣My Wattpadian Fans..? Abdullahi na kai gaisuwa fa🖐️yace ku daina sa mai ido Shi da matarsa yafi kowa iko a kanta...Allah ya bar zumunci Ameen So So So mara iyaka..*

*008*


  "Ahaka suka isa Gida,ita ta Sauka Ta Bude Gidan Tana Rike da karamar Kular da Ammi ta saka musu Ferfesun kayan Cikin,Shi kuma ya Shiga da Mashin din Cikin Gida.

Tare suka Bude Dakin Suka Shiga,Hafsah ta Bude Kitchen ta Dauko Filet tazo ta Zubama Abdullahi yaci kadan sunayi suna Hira Jefi Jefi Duk game da Ciwon Daddy ne,Bayan ya gama ya Shiga Toilet yayi wanka yau dai yayi wanka da Ruwan Zafin Data saka a Kittle Dashi yayi wanka Bayan ya Fito itama Hafsah ta Shiga Tare sukayi Sallar Isha"i Shi yaja musu Jam"i.

Bayan Sun kamallah sukayi Shirin kwanciya Kowannensu ya Saka kayan Barci Abdullahi ya saka Riga da wando na Pjm ita kuma Hafsah ta Saka Wata Rigar Barci Mai kalan pick,wacce iyakarta Gwiwa Kuma SharaShara ce Ana ganin komai na Jikinta wanda pant kadai ta iya sakawa.

Abdullahi na kwance yana Kallon Hafsah Dake gaban madubi Tana Fesa Turare,ya Daga kansa yana Fadin"Ni kam Hausina yau kuma Audin naki kike jama Aji..?

Hafsah ta saki Mirmishi kafin tace"Wace Hausi ta jama Mai Babban Suna aji..? Ganinan Tafe gareka Mijina.."Tafada Cikin wani Shauki da Soyayyah Mirmishi ya sakarmata Hanyar Fita Falo ta Nufa ya Dago yana Fadin"Ina kuma Zaki..?

Hafsah tace"Kicthen zan Rufe sai na Kashemana wuta na Rufe Kofa..."Da Sauri ya tashi zaune Lokaci Daya ya Sauko Daga kan Gadon yana Fadin"Karki Fita ahaka..Bari ni naje na kulle ina key din..? Hafsah tace"Yana kan Fridge afalo.."Fita yayi ta Bishi da kallo acikin Ranta tana addu"an Godiya ga Allah Daya Saussauta Fushin Abdullahi akanta.

Kitchen din ya Fara kullewa kana ya Shigo Falon ya Kashe kwan Waje kana ya Kashe na Falon ya Rufe Kofar da key,kana ya koma Cikin Bedroom din ya iske Hafsah har ta kwanta Taja Blanket,ta Rufe Jikinta Dashi Mirmishi ya saki kafin ya Kashe Lantarkin Dakin ya hayo Gadon Cikin Bargon Ya Riko Hafsah Lokaci Daya ya sakata acikin Jikinsa,Atare suka saki ajiyar Zuciya Domin Dukkansu sunyi kewar Jikin Juna.

Yana ta Bayanta ne ya saka Kanshi Cikin Wuyanta yana Hura mata iska Cikin wani Salo Zillewa tayi Tana kamkame Hannuwansa,Cikin Wata irin Murya,tace"Abban Amirah...!
Taja sunan cikin wani yanayi Kamar mai Rada Cikin wani Salo kuma Cikin Shakewar murya kansa na Cikin Wuyanta Yana Fadin"Hmm...Uhm...!Hafsah ta Juyo da Kanta Suna kallon Juna Lumshe ido yayi kafin ya kara Budewa Cikin Wani irin yanayi mai kama da Sha"awa yace"Uhm ina Jinki..." Menene..?

Yafada yana Kara Tusa kansa Cikin Kirjinta Hannuwanta ta Zagaya abayansa Tana Shafashi kafin ta Fara mgana"Don Allah kayi Hakuri Bisa Duka Laifin Dana aikata maka...Wlh bada Son Raina bane Abban Amira ka yafemin...."!Ta karishe Fada kamar zata saka kuka Kamkameta yayi Cikin Sakin Numfashi kafin yace"Ya isa...!yake Fada lokaci Daya yana Yawo da Hannuwansa a Dogin Wuyanta.

Cikin Muryan Rauni Hafsah tace"Kana Fushi dani Abban Amira...Ka sakani ku..."Shiii..."!Abdullahi yace mata Lokaci Daya yana Dora Bakinsa saman Bakinta ya Sumbata kafin ya Dago kansa yana kallon Cikin kwayan Idanuwanta Da dan Hasken Farin Watan Daya ke Shigowa Ta Cikin Labulen Window Dake Bude.

Hannu ya Saka yana Shafa Fuskarta kafin yace"Kinsan meyasa nayi miki wannan Hukuncin..? Bai bata Zarafin mgana ba ya Cigaba da Fadin"Saboda na nuna miki kuskusranki,Kuma Abu mai Girma mafi Muhimmanci Shine Bana son Watarana ki Raina ni ko kuma Watarana Na zama nine a kasanki bana son awayi gari Watarana nagaya agidana kuma aki amfani Dashi Bana so ki Rainani Hafsatu Shiyasa wani Lokacin zaki ga na koma Miki Masiffan Namiji ba Laifina bane kema Ba naki bane kawai bana son Watarana ki zama ina Fada kina Fada ko kuma in Bada Umrni ya zama abun Banza..."Yafada Cikin Wani Raunin Murya

Hafsah tamai kuri da ido Kafin ta Murmusa Hannunsa Dake yawo saman Fuskarta ta Damke tana Fadin"Taya Hafsatu zata Raina Gwarzon maza kamar Abdullahi..?Taya kake tsamamin Zan iya Raina ka..? Kana Tunanin akwai Watarana da zata zo naji kai ba Shugaba na bane..? Ko kana Tunanin irin Tarbiyan Dasu Ammi suka Bani kenan..?Ta karishe Fada Cikin Sanyin Murya.

Rumgumeta yayi yana Fadin"Ko Daya bana Tamtama ga Tarbiyanki kuma Bana ja da cewa ke macece ta gari..Kawai dai bazan iya sakin Jiki bane..Sai dai kawai ki kara Hakuri wani Lokacin ina da Fushi da Kuma Zuciya.."Hafsah ta Kara kamkameshi Tana Fadin"Bakomai Mijina...Ina Sonka kuma zan Cigaba da zama Dakai a yadda kake...Ina mai Tabbatar maka Ni Hafsah bazan Taba Raina ka ba koda yaushe kai Shugabane akan Hafsah.."Tana Rufe baki Taji ya Rufe bakinta Danashi Ya fara Kissing dinta,itama sai ta Tallabe kanshi Tana taimakamai suna Kissing din Juna Cikin Fitan Hayyaci Lokaci Daya kuma Hannayensu na kara kaina Cikin na juna,Chan kuma Abdullahi ya Zuro Hannu yaja musu Bargo har kansu sai dai kawai naga sun Dungule waje Daya Suna Cigaba da Bama Junansu da Jikinsu hakkinsu......

****

Haka suka kwana Cikin Farinciki da Annushuwa,Sun kwana Suna Raya wannan Daran mai Cike da Soyayyah da Muradi mai Girma,wanda suka sakashi Cikin Darare masu matukar albarka da Alheri da Tarihi acikin Dareren da Suka gudana acikin Tarihin Auransu.

Wuni Sukayi Ranar Asabar agidan Suna Shan Soyayyarsu Abdullahi ko nan da chan bai Fita ba sai dai in zashi masallaci,Yana gida kusa da Hafsah yau ba Fada ba Korafi sai ma wani Tattali da Soyayyah Dayake Nuna mata kamar ya Hadiyeta Batayi mamaki ba Sanin Abdullahi haka yake wani Lokacin kamar mahauniya wajen Chanza launi in yau anyi Dadi Dashi Bai zama lalle Gobe ayi Dadi Dashi ba.

Wajen karfe 2pm na Rana Bayan Hafsah tagama Abinci Fatan Wake Tama Daddy da hanta sai kayan Fruit Abdullahi ya Dauketa suka Tafi Gidansu Hafsah Suka kara Duba Daddy da Jiki Chan suka Wuni sai gabda mangariba ya Daukota Suka Dawo Gida,Shi daman yana kaita bai Jima ba ya barta nan ya Shiga Cikin Gari ganin Anty Hadiza tazo da kuma wasu Daga Cikin yan"uwan Daddy da suka zo Dubashi.,Alhamdulillah Sun samu Jikin Daddy da Sauki Sosai yama Warware Ganin ya"yan nashi Suma Cikin kwanciyar Hankali musamman yar Lelensa Hafsatuwa.

Ganin gidan su kadai ne Shiyasa Hafsah bayan Sun Dawo  ta Tsuke Cikin Wata Riga wacce iyakarta Asirin Nonuwanta kadai ta Rufe,cibiyarta Duka da Cikinta suna Waje sai wani karamin Wandon Jeans wanda iyakarsa Rabin Cinyarta ya Rufe Komai daga Sama zuwa kasa yana Bayyana ne,Kanta kuma tayi Tsifa ta Tara gashinta waje Daya ta Daureshi da Band ta sakeshi kawai Tana yawo haka gashi tayi aiki da Turare ko'ina ta Gifta sai kamshi ke tashi Abdullahi ya Rude da Dressing din Hafsah wanda Dama Shi aduniya yana Son yaga mace da irin wannan Shigar yawancin kayan ma Shi ya Siyo mata,Da Farkon kunyar sakawa take sai da Anty Hadiza tayi wani Zuwa Gidanta ta gansu Cikin Wardrope dinta bata sakawa ta Fara mata Fada Rashin amfani Dasu Da ita da Subai"atu babu Abunda zata ce musu sai Godiya Domin Suna bata Shawarwari da kuma Karin Haske game da Abunda ya Danganci Zaman Aure.

In yaran na nan Sai Da Daddare take sakamai irin kayan Lokacin sun kwanta suna Dakinsu Weekend ne in yana Gida take Chakaremai wani Lokacin ko Ransa na bace ne ya Dinga Satar kallonta kenan Har Daga karshe dai ya saki Tsiyan nashi ya More kallonnashi Dakyau Abu Guda Daya Dake kara Burgeta kan Abdullahi duk Abunda ya gani na kwalliyar mata sai ya Siyo mata yace wannan zai yi ma Hafsatuna kyau matuka,in kuma ya Siyo ta sakamai ya Dinga ya bata mata kenan yana Kuranta kyan Datayi acikin Idanuwansa Shiyasa Sau Tari bata Dora Fushi ko Masifar Abdullahi awata gagaruman mtsala tafi Dora hakan da Shi yanayin Halittarsa kenan kuma ita bazata iya Taba Chanzashi ba sai ta bar ma kanta Mijinta yana Sonta itama tana Sonshi Zatayi kokari wajen kyautatamai Daidai gwargwardon iyawarta.

Da daddare ma hanata yin wani Abincin yayi ya Fita yaje ya Siyo musu kaza da kuma kayan Fruit suka ci suka Sha Hafsah na kan Jikinsa Tare suka Ciyar da Juna,Ya Dauko Yankan kankana ya sakamata abaki kenan Shi kuma sai ya Bude Bakinsa alamun ta sakamai Shima make kafada tayi alamun ta Shagwaba ganin haka yasa ya kama kanta kawai ya Tura Harshensa Cikin bakinta ya Fara wasa da kankanan aciki itama sai ta Biyemai suna ta Gutsiran kankanan a Hankali Gefe Daya kuma Suna Wasa da Harshensu Lokaci Daya sai da suka gama Cijye kankanar nan Tas kana kuma Suka Zarce da kissing din Juna Cikin wani yanayin Muradi mai Girma sunyi Nisa basa jin kira kawai sai Kiran Wayar Abdullahi ya katse musu Hanzari Hafsah ce ta Fara Janye Kanta Lokaci Daya da Jikinta Tana kallon Abdullahi wanda ya koma ya Jingina da kujera yana maida Numfashi Idanuwansa suna Lumshe kamar mai Barci.

Cikin Sanyin Murya tace"Ana kiran Wayarka fa Abban Amira..."Dakyar ya iya Bude ido yana Fadin"Mikomin wayar.."Tashi Tayi da Sauri ta mikamai wayar dake Chan gefensu,Ya karba sunan wanda yaga yana Kiran nashi ne yasa ya Gyara zama yana kara Bude idanuwansa Cikin Girmamawa ya Daga Kiran da Sallama tare da gaishe da wanda ya Kirashi Ganin Haka yasa Hafsah ta Duka Tana Tattara Kasusuwan kazan da suka ci suka Zuzzubar a kasan Cafet kamar wasu yara ta Tattara Fruit ta Hada da Filet din ta kai Kitchen Gabadaya ta bar Abdullahi ya samu Damar amsa wayarsa.

Baba Wada Daga Chan Bangaren yace"Lafiya lau Abdullahi ya gida ya yara da kuma ita iyalin naka...? Abdullahi yace"Duk suna Lafiya Baba.."Baba Wada yace"Masha Allah...Dama Abunda yasa na Kira Rokonka zanyi Abdullahi Don Allah ka Taimaka Gobe Tun Safe ka Shirya Nazifi zai zo ya Daukeka kuje Chan kano Tare Wajen iyayen mai Dakinsa ku basu Hakuri,Wauta ne dai Nazifi ya Riga yayi,sai Hakuri Tunda Tun Shekaranjiya Mahaifin Sakinar ya kara Kirana yana gayamin Sakina ta dawo Gida tace bazata koma ba kuma ga Duk alamu yama Goyi bayan yar"sa yace yazai zai maka Shi Nazifi kotun Bisa Dukan yar"sa da yayi.."Abdullahi yace"Ashh Abu bai yi Dadi ba..Ai ya kamata ya Kira Shi Nazifin yaji nashi Bangaren in adalci yake so yayi.."

Baba Wada yace"Abdullahi kenan ai wannan sai Dattijo wanda yasan Dattako ba irin Gidan da Nazifi yaje ya Dauko Aure ba Dama na gayamai Duk wanda ya Siyi Rariya yasan zata Fidda Ruwa akoda yaushe ina gayamai ya kamata ya rika Koyi Dakai Bai Dubaka yagani ba Duk da iyayen mai Dakinka suna da Halinsu ammh kaga ai Dattijom arziki ne Alhaji Hamza Dalilin Zuwa neman Auranka har yau muna gaissawa ta waya kuma Duk inda ya ganni sai ya tsaya mum Gaisa da ita kanta mai Dakin nashi Komai da ita ake Gudanarwa an zama Daya ammh Shi ka Duba inda yakai kanshi Ai daman wanda ya Hau Motar kwadayi karshensa Tashar Wulakanci ne.."Abdullahi yace"Sai Hakuri Baba....Insha Allahu in Allah kaimu goben sai muje..Allah ya kyauta na gaba.."Baba wada yace"Ameen..Nagode Abdullahi ka gaidamin da Amaryata Hajara da kuma Abokina Usman tare da ita mai Dakin naka.."

Abdullahi yace"Zasu ji Baba.ammh amaryanka da Abokin ka Suna nan tare Dakai Suna Gidan mama sai gobe da yammah zasu Dawo.."Mallam wada yace"Hakane fa...Na manta Karshen mako me suna zuwa makaranta Shikenan zan Shirya Dakai naje har gidan naji Dalilin karima na Kin barina naga Amaryata.."Abdullahi na Dariya sukayi sallama da Baba wada mahaifin Nazifi wanda dama Haka yake Mutum ne na gari ga Dattako Da sanin yakamata ga kuma Barkwanci.

Yagama wayar kenan sai ga Hafsah ta Shigo Kallonta Abdullahi yayi kafin yace" Ahaka kika Fita waje..? Kallon kanta tayi kafin tace"Eh.."Wani kallo yayi mata Kafin yace"Ammh dai baki da Hankali ko..? Yanzu fa Dare ammh Shine zaki Fita ahaka ina laifinki ki saka Hijabi Hafsah ko Domin idanuwan Wadanda bama Gani,."Sai Lokacin Hafsah ta gane laifinta ta kuma san bata kyauta ba ko ba Domin komai ba sai Domin Tsarin Jikinta kuma ta manta ne Datashi Fita wani karamin gyale kawai ta yafa ma kanta.

Kai ta Sadda kasa kafin tace"Kayi Hakuri na manta ne ammh Haka bazata kara Faruwa ba."Mikewa yayi yana Fadin'"Tsiyana Dake da Abun bada Hakuri da bana bada Hakuri sai kin Bani Hakuri meyasa kike Hakane..? Nifa ba saboda komai yasa nayi mgana ba, sai Saboda yau ba fata ake ba Dalilin Haka wata lalura ta sameki kinga wa gari ya waya kenan..?

Hafsah tace"Hakane...ammh ai Shima Bada Hakurin ba laifi bane ko Abban Amira..? Kai Tsaye ya kalleta zai yi mgana kenan Wayarsa ta fara neman Dauki kawai sai ya Daga mata Hannu ya Juya ya Nufi Hanyar Bedroom din Lokaci Daya yana Daga Wayar da Fadin"Hello Mutumina.."Tunda Taji haka ta gane Nazifi ne Domin Shine kadai abokin Abdullahi na kusa wanda suke Kiran da juna da Irin Sunayen nan.

Tsayawa tayi afalon ta Kankanta komai kana ta kashe kwan Falon ta Kulle Kofar key dama already ta Kullo Kitchen dinta kana ta Bishi Cikin Bedroom din ta isleshi Zaune yana Duba wani Abu Cikin Sytem dinshi Tailet kawai ta Wuce ta Tube kayanta ta Fara wanka Bata Dauki Lokaci ba ta gama kana ta Dauro alwala Har ta Fito bai gama ba kawai sai ta Zura wata Rigar barcinta Ja Doguwa mai Zanen baki Tana da igiyiya ne ta gaba wanda ake Daurewa ko Botir  Bata Dashi Sallaya ta Shinfida ta saka Hijabinta tayi sallar Isha"i ta Dora da Shafa'i da Wuturi Sai da ta Idar kana Abdullahi ya Kashe System dinsa ya Shiga wanka da Kallo Ta Bishi ganin yanayin Fara"arsa ta Sauya Daga Shigowarsa Daki Baya Rasa Nasaba kila da wayar da sukayi da Nazifi ko kuma Daga wajen aiki ne Bacin Ran nashi.

Koda ya Fito wanka Har ta kwanta Tana kallonshi ya isa Gaban madubi yana Fesa Spary Wardrope ya Bude ya Dauko Wata Bakar Jallabiya ya sanya Shima Sallayar ya Shinfida ya Tada Sallar Shafa'i yayi da Wuturi ya Dade yana Addu"a kafin ya Shafa Lokacin Tuni Har Barci ya Fara Daukan Hafsah kashe Wutar Dakin yayi kana Shima ya Raba gefenta ya kwana yana Shafa Kumatunta Lokaci Daya yana Fadin"Hafsatuna...Hafsatuna kin yi Barci ne..?

Sama sama Taji Shi ta Bude Idonta Jinta Cikin Jikinsa yasa ta Juya Suna kallon Juna kafin tace"Barcin ne ya Daukeni Bansani ba..am Sorry.."Hancinta ya lakuce kafin yace"Bakomai..Dama zan gayamiki ne gobe Tun 7am Nazifi zai zo ya Daukeni zamu je kano in Allah ya kaimu.."Cikin mamaki tace"Kano kuma Abban Amira..? Kai ya Dagamata yana Fadin"Eh..Gidan Surukansa zamu Sun samu matsala da Sakinar ne ta koma Gida.."Yafada yana Kokarin Warware Band din data Daure Kanta Dashi Daga haka kuma bai kara cewa komai ba Saboda daman Shi bamai wannan Surutun bane ko Hafsah ta sani Abdullahi bashi da Surutun barkatai Shidai Abunda ya Shafeshi yafi maida kai akanshi.

Tana jinsa yana waasa da gashin kanta yana kuma Tura Hannuwanshi Cikin gashin nata Dayake tana da Suma kuma bata Dade da zuwa gyaran kai ba,lumshe ido tayi kafin tace"Ayyah Abu bai yi Dadi ba..Allah ya kyauta ya kuma kaimu Goben Allah kuma yakai ku lafiya ya Dawo mana Daku lafiys.."Kiss ya bata a goshinta kafin ya Rumgumeta yana Fadin"Ameen ya Allah Matata..."Tana jinsa ya warware igiyar Rigar barcin yana Tusa Hannuwansa Duka Cikin Rigarta Itama Tallabanshi tayi Lokaci Daya ta Hade bakinsu waje Daya Daga haka dai bai mata komai ba ya Dai dan Rage zafi kadan sai kuma ya kara sakata Cikin Jikinsa yana Fadin"Oya yi barcinki yau Babu Abunda zan miki"Mirmishi kawai ta saki Ta Rufe idanuwanta Domin Tabbas Dama Barci nacin idanuwanta.

*****
Washegari Tun karfe 7am da wani abu na safe sai ga Nazifi acikin Gidansu ya ci Shadda Mai Ruwan Toka sai maiko take da yarari Abdullahi ma Tuni ya Shirya Domin Tunda Hafsah ta tashi sallah bata koma ba sanin yace mata zasu yi Tafiya,Nan gidan Nazifi yayi Breakfast dinshi yana bama Abdullahi labarin ba"a Zaria ya kwana ba yanzu haka Daga kaduna yake,Abdullahi natamai Dariya yana Zolayansa da mai Gida Uku,Hafsah dai na Ciki tana Jinsu Dayake itama bamai Son Hayaniya bace Daga gaisuwa ta Shige Ciki ta barsu nan har tayi wanka tazo ta Shirya Cikin wani less basu gama Breakfast din  nasu ba Tana Saka Dankunne akunnenta kenan Taji Abdullahi na Kiranta ta amsa Cikin Hanzari ta karisa saka Dan kunnen ta kuma Zari mayafinta ta saka ta Fito Falon

Tsattsaye ta Gansu Abdullahi ya kalleta yana Fadin"Mikomin wayata kiga mu tafi kada muyi yammah Bisa Hanya.."da Sauri ta Juya Zuwa Cikin Bedroom ta Daukomai wayarsa tazo ta mikamai Tana Fadin"ka ko saka Turare Abban Amira..? Kai ya Dafe yana Fadin"Inafa na saka na manta wannan Dan Wutar Cikin yazo Tun safe ya Dameni.."Yafada yana kallon Nazifi wanda ke latsa waya Dagowa yayi yana Hararan Abdullahi kafin yace"Kaji Sharri..Ba gidan ka kwana ba wani ya Hana tun jiya ka Fito da Turaran da zaka Fesa.? Kinga Hafsah Don Allah kyalesa haka mu Tafi,wazai sakama Turare shi da ba neman Aure zashi ba in kuma kina so Daga zuwa Bikon Wata ya Dawo da mganar wata kuma Shikenan..'Yafada yana Dariya.

Hafsah tace"Naji ba komai...Komai dai menene bana son Arainamin Mijina muje Ciki na Fesa maka Turare harda ma Hula domin wannan Hular bata Dace da wannan Shaddar ba.."Tafada tana kama Hannunsa Shi kuma Abdullahi ya Bita yana Fadin"Yauwa Hausina..Matata har agidan Aljannah.."Yafada yana waigen Nazifi yana mai Dariya Harda gwalo.

Hular ta sauyamai ta Daukomai wacce tayi Shige da kalan Shaddarsa mai kalan Sararin samaniya,ta kuma Jikanshi da Turaransa na azzaro Visit,Kallonsa tayi ganin yadda yayi wani kyau kamar Zarah Cikin wata Cikin Shagwaba tace"Lala...Kaga yadda Mijina ya Hadu kuwa..? Nidai ina Tsoron kada mganar Nazifi ta zama gaskiya.."Dariya ta kama Abdullahi kawai sai yajata Jikinsa ya Rumgume yana Fadin"Karki biyema Mganar Nazifi kinsansa magulmaci ne yau ko Aure zan kara matata ai kice wacce zan Fara sanarmawa kafin kowa balle ma ba mganar karin Aure a Tsarina bansani ba ko zuwa gaba.."Ya karishe Fada yana Hura mata iskar Bakinshi kan Dogin wuyanta Zillewa tayi tana Dariya ya taka zai Rikota Kawai Sukaji Hon din Motar Nazifi na neman Toshe musu Dodon kunne Kai Abdullahi ya Dafe kafin yace"Kai Wanchan gayen dan Wutar Ciki ne..Kasan kana son matar taka ka bari ta tafi gida kawai ni ina son yau na zauna naga kwalliyar Hausina Dakyau dakyau ammh yazo ya Takuramin.."Yafada yana wani Bata rai Daidai Lokacin da Nazifin ya kara sakin Hon.

Dariya ta kama Hafsah bata karisa ba Abdullahi ya Rikota ya kara sakata Cikin Jikinsa Na dan wani Lokaci kafin yayi mata Kiss Saman kanta yana Fadin"Miss u...Take care of ur self for me kinji HAFSATUNA.!

Yafada Cikin wata Murya Mirmishi ta sakarmai kafin itama tayi Dage Domin ya Fita Tsawo ta sakamar sumba bisa karan Hancinsa Tana Fadin"Insha Allah U Too..Abdullahi Mijin Hafsatu.."Mirmishi ya sakarmata kafin ya Riko Hannunta har Tsakar Gidan ta Rakashi kana suka saki juna ya Fita Tana Dagamai Hannu,jikinta Duk yayi sanyi Tafiyar ne tazo ba wani Shiri.

Yana Fitowa Nazifi ya saki Tsaki kawai Abdullahi ya Bude gaban Mota ya Shiga yana Fadin"Mallam karfa ka Takuramin wlh..Kaja Tsiya sai na koma Abuna.."Ko kallonsa Nazifi bai yi ba ya Fizgi Motan da Gudu sai da Abdullahi yayi gaba ya Dawo Cikin mamaki ya kalli Nazifi yana Fadin"Shin wai ni nace ka mari Sakinar ne har tatafi Gidansu..? Yau ga Shawarakin Banza Yana neman Hushe haushin wata akaina..'Ba Abdullahi kadai Daya Fada ba Hatta Nazifin sai da ya kyalkyace da Dariya suka Hada Hannu suka Tafa suna Cigaba da Dariyansu irin na Shakikan abokan da Shakuwa da yarda da Juna ke Tsakaninsu.



*Janafty..*

Continue Reading

You'll Also Like

80.5K 12.3K 64
Title Quick Transmigration Cannon Fodder's Record of Counterattacks 快穿之炮灰女配逆袭记 Author(s) 很是矫情 Hen Shi Jiao Qing English translator Butterfly's curse...
1.3M 70.8K 58
သူ႕နာမည္က ' ေတာ္၀င္မင္းခက္ထန္ ' တဲ့... ကြၽန္ေတာ့္ရဲ႕ ခက္ထန္ ၊ ကြၽန္ေတာ့္ကို မုန္းတဲ့ခက္ထန္ ၊ ကြၽန္ေတာ့္ကို ေျမႀကီးေပၚက သဲမႈန္႔ေလးလို စုပ္ေခ် ဖ်က္စီးပ...
308K 24K 84
គេមាន​សំណាង​ ដែលបានអាល់ហ្វាកំណាចប្រៀបដូចសាតាន ថ្នមស្នេហ៍ថែថួនដូចជាកែវភ្នែកទាំងគូ ។ ជុងហ្គុក​ ព្រីនស៊ីសគ្រីសស្តាល់​ / គីម​ ថេហ្យុង មីន យ៉ុនហ្គីXផាក ជី...
678K 31K 46
နှလုံးသားထဲဝင်ကြည့်ချိန်ရောက်ပီ နှလုံးသားထဲပန်းရောင်လေးတွေတွေ့လား အဲ့ဒါအချစ်တွေ သိမ်မွေ့နူးညံ့တဲ့အချစ်တွေအေးမြတဲ့အချစ်တွေမြင်ကြည့်ပါ... ကြည့်ပါ.....စ...